Taskun da mata ke shiga kan rashin haihuwa

Taskun da mata ke shiga kan rashin haihuwa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A Amurka, duk ma’aurata ɗaya cikin takwas ke fama da matsalar rashin haihuwa.

Amma al’adar yin shiru da tsangwama da ke baibaye da batun na sa mutane da dama cikin tasku.

Masu bincike a Cibiyar Lafiya ta Jami’ar Washington sun nuna cewa yanayin haihuwa a faɗin duniya ya ragu da kusan rabin kashi 2.4 a 2017 – kuma bincikensu wanda aka wallafa a mujallar Lancet, ya yi hasashen hakan zai faɗi da kashi 1.7 nan da shekarar 2100.

Ga dai labaran wasu matan da suka taba samun kansu cikin damuwar rashin haihuwa.