Bidiyo: Yadda talauci ya hana wata yarinya zuwa makaranta a Kebbi

Bidiyo: Yadda talauci ya hana wata yarinya zuwa makaranta a Kebbi

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wata yarinya da ke tallan awara a jihar Kebbi Najeriya ta bayyana halin da tsa tsinci kanta a ciki sakamakon rashin zuwa makaranta.

Zubaida Kabir ta shaida wa BBC cewa ba a son santa ne ba ta zuwa makaranta ba.

"Gaskiya ko ni ba a son raina nake yin kwai da kwai ba. Mamana ba tare take da babana ba. Kuma babana bai dauki naiyuna ba. Mamana ce cina da shana da maganina," in ji ta.

Ta kara da cewa an cire ta daga makaranta ne saboda iyayenta ba su da damar biyan kudin makaranta.

Sai dai ta ce yanzu ana amfani da ribar da take samu a talla wajen daukar nauyin kanenta zuwa makarantar.

Alkaluma sun nuna cewa kashi 53.8 na yara mata miliyan 65 da ba sa zuwa makaranta a duniya suna zaune ne a yankin Afirka, kudu da hamadar Sahara.

A Najeriyar ma wannan matsala ta fi Kamari ne a Arewacin kasar inda miliyoyin yara mata kan gaza samun ilimi sanadiyyar talauci ko kuma dalilai na ala’ada.

Wasu bidiyon da za ku so ku kalla: