An gama duk wani yabo da za a yi wa manzon Allah – Bashir Ɗan Musa

An gama duk wani yabo da za a yi wa manzon Allah – Bashir Ɗan Musa

Latsa hoton da ke sama domin kallon hira da Bashir Ɗan Musa:

Fitaccen mawaƙin begen Annabi Muhammad SAW, Malam Bashir Ɗan Musa ya ce yana matukar takaicin yadda aka lalata yabon manzon Allah (SAW) a shekarun nan.

Bashir Ɗan Musa ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce rashin ilimi da kuma son rai ne ya kai masu yabo "suka faɗa duhun jahilci" a wannan lokaci.

"A baya mukan rubuta waƙa mu bai wa junanmu kamar ni da Rabi'u Usman Baba da Rufa'i Ayagi da Bashir Tashi da sauransu, idan akwai kuskure mu gyara wa juna.

"Za a duba idan ka bai wa Annabi haƙƙin Allah sai a gyara, in kuma ka bai wa wani waliyyi hakkin da ba nasa ba shi ma a gyra maka," in ji Malam Bashir.

Ya ce idan kana buƙatar yabon Annabi ba sai ka kushe wanda suke tare da shi ba ko kuma 'yan uwansa annabawa "saboda kowa matsayinsa daban".

"Idan mutum yana so ya yi bege kamar yadda ya kamata a kan turbar gaskiya to sai ya bi sawun magabata.

"An gama duk wani yabo da za a yi wa ma'aiki, mafi kyau sai mutum ya bi turbar da magata suka bi sai a dace. Amma da ka yi yadda kake so to sai ka zame.

"Da akwai waɗanda suke yin yabo karshe ba sa samun ladan komai, saboda ba sa yin sa kamar yadda ya kamata."