Afghanistan: Tsokaci kan rayuwa karkashin Taliban daga 1996-2001

Afghanistan: Tsokaci kan rayuwa karkashin Taliban daga 1996-2001

A wannan bidiyon abokiyar aikinmu, Fauziyya Kabir Tukur, ta yi waiwaye kan yadda rayuwa ta kasance karkashin mulkin 'yan Taliban tsakanin 1996-2001.

Mun yi waiwayen ne yayin da 'yan kungiyar ta Taliban suka sake kwace mulki a kasar Afghanistan, shekaru 20 bayan dakarun Amurka sun kawar da su.

Kasashen duniya dai na fargabar cewa Taliban za ta sake kwata 'yar gidan jiya, sai dai jagororin kungiyar su ce wannan karon za a samu sauyi.