Dan arewacin Najeriya da ke binciken gano maganin cutar sikila da ke shafar al'aurar maza

Dan arewacin Najeriya da ke binciken gano maganin cutar sikila da ke shafar al'aurar maza

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

Watakila nan ba da jimawa ba masu cutar amosanin jini ko kuma sikila musamman maza da cutar ke shafar al'aurarsu ka iya samun maganin cutar wani abu da aka tabbatar ba shi da magani.

Kungiyar American Society of haematology, kungiya mafi girma a duniya mai bincike kan jini, ta bai wani likita dan arewacin Najeriya tallafi domin bincike kan cutar ta sikila da fatan samo maganinta.

Dr Ibrahim Musa, kwarraren likita ne kan cuttutukan da suka shafi jini ya dukufa domin cimma wannan buri da ya sa a gaba.