'Abin da ya sa aka canza Salma ta Kwana Casa'in'

'Abin da ya sa aka canza Salma ta Kwana Casa'in'

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Salisu T. Balarabe, daraktan shirin nan mai farin jini na Kwana Casa'in, ya bayyana dalilinsu na sauya tauraruwar da ke taka rawa a matsayin Salma.

A wata hira da BBC Hausa, daraktan ya ce ita da kanta ce ta bayyana cewa ba za ta ci gaba da fitowa a shirin ba.

A cewarsa: "A tsarinmu na Kwana Casa'in duk lokacin da za a gabatar da wani zango, akan tuntubi jarumai kafin lokaci cewa an sa lokacin da za a dauki wannan zangon; wadansu sukan fadi cewa ba za su samu yi ba saboda yanayi na karatu ko kuma wani dalili da su suka bar wa kansu sani.

Lokacin da muka tuntubi ita Salma a kan cewa za mu dauki shirin Kwana Casa'in Zango na shida ta fada mana cewa gaskiya ba za ta samu dama ba, mun so mu san dalili sai ta fada mana cewa yana da nasaba da iyayenta wanda ba lallai ne ta iya bayyanawa b.''