Waiwaye: Wata tsohuwar hira ta BBC da Sarkin Ban Kano

Waiwaye: Wata tsohuwar hira ta BBC da Sarkin Ban Kano

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan ya rasu yau Juma'a da Asuba.

Marigayin ya rasu yana da shekara 95 a duniya.

Daya daga cikin 'ya'yansa Baba Ado ne ya tabbatar wa da BBC labarin rasuwar tasa.

Wannan wata tsohuwar hira ce da BBC Hausa ta taba yi da shi a lokacin bai wa Sarki Muhammadu Sanusi na II sandar sarauta.