Girman matsalar cin zalin dalibai a makarantun kwana

Girman matsalar cin zalin dalibai a makarantun kwana

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Matsalar cin zalin dalibai a makarantun kwana ta dade tana damun dalibai da iyayensu a Najeriya.

Sau da dama daliban manyan azuzuwa wadanda ake kira seniors ne suke cin zalin na kasa da su, wasu lokutan hakan kan kai ga kisa.

Lamarin ya jan hankalin jama'a a a baya bayan nan yayin da aka yi zargin wasu dalibai sun kashe kashe wani dalibi a wata makanta da ke Lagos bayan ya ki yarda ya shiga kungiyarsu ta asiri.

Khadija Nasidi ta yi mana nazari kan hakan: