Bidiyon hirar BBC da Bashir Dandago

Bidiyon hirar BBC da Bashir Dandago

Fitaccen sha'irin nan na jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Bashir Dandago, ya ce wakar 'Fadimatu' ta yi sanadin samuwar daukakar da ba zai manta da ita ba.

Ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC Hausa.

A cewarsa, daya daga cikin mutanen da suka ba shi kyautuka kan wakar ita ce fitacciyar tauraruwar Nollywood, Genevieve Nnaji.