China na bincike kan wata 'bukka' da jirgin sama jannatinta ya hango a duniyar wata
China na bincike kan wata 'bukka' da jirgin sama jannatinta ya hango a duniyar wata
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
China ta ƙaddamar da wani bincike kan wani abu da ba a gane ko mene ne ba a can wata kusurwa ta duniyar wata.
Jirgin saman jannatin Yutu-2 ne ya gano abin wanda yake dunƙulalle mai kama da bukka, a watan Nuwamban 2021.
Ƙwararru sun ce wataƙila kuma wani ƙatoton dutse ne.