Gwarazan ƴan takarar wasanni na BBC Aspoty 2021: Bayani kan Edouard Mendy
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Edouard Mendy ya taka rawar gani a Stamford Bridge tun bayan da Chelsea ta saye shi daga hannun ƙungiyar Rennes ta ƙasar Faransa a Satumbar 2020 kuma ya bayar da gudunmawa wajen nasarar da kulob ɗin ya samu a gasar Champions League a watan Mayu.
Ya kafa tarihi ta hanyar hana a ci shi a wasa tara wanda hakan ya kai shi ga ɗaga kofi a kakar. Mendy ya kuma kafa tarihi ta hanyar zama gola ɗan nahiyar Afrika na farko da ya yi tsaron gida a wasan ƙarshe na gasar Champions League kuma shi ne na farko a Turai a babbar gasa ta Turai tun bayan da Bruce Grobbelaar ɗan ƙasar Zimbabwe ya yi tsaron gidan Liverpool a gasar European Cup.
Wasa 19 jumulla da Mendy ya yi ba tare da ƙwallo ta shiga ragarsa ba a kakar da ta wuce a gasar Champions League da Premier ya sa ya samu kyautar golan UEFA na 2020-21.
An kuma zaɓe shi domin samun kyautar golan da ya fi iya tsaron gida na duniya wanda FIFA ke bayarwa.