Gwarazan ƴan takarar wasanni na BBC Aspoty 2021: Bayani kan Tatjana Schoenmaker

Gwarazan ƴan takarar wasanni na BBC Aspoty 2021: Bayani kan Tatjana Schoenmaker

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Tatjana Schoenmake ta kafa tarihi a Tokyo inda ba wai ta tafi da zinare da azurfa kaɗai gida ba, amma ta kafa wani sabon tarihi na tseren mita 200 da 100 na ninƙaya a gasar.

A irin hakan, ita ce mace ta farko da ta samu zinare daga Afrika Ta Kudu a ninƙayar mata tun bayan shekarar 2000 inda ta kawo ƙarshen jiran da ƙasarta ke yi na shekara da shekaru ga mata su samu zinare.

Schoenmaker ta kusan daina wasanni ma tun a 2016, bayan ta kasa samun cancanta ta je gasar Rio. Sai dai ta ci gaba da wasan inda ta samu nasarori a ƙasar da ma wasu ƙasashen da ma wasannin ƙasashen rainon Ingila inda ta samu zinare biyu da azurfa ɗaya.