Gwarazan ƴan takarar wasanni na BBC Aspoty 2021: Bayani kan Eliud Kipchoge
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon
Babu tantama shi ne wanda ya fi shahara a gudun famfalaƙi a bana, Eliud Kipchoge ya samu wannan nasarar ce bayan ya yi gudun mil 26.2 inda ya samu kyautar zinare a gasar Olympics.
Shi ne mutum na uku da ya taɓa kare kyautar tasa ta gudun famfalaƙi a gasar, ɗan ƙasar na Kenya daga baya ya samu yabo a matsayin wanda ya fi shahara a wasannin tsalle-tsalle na shekarar.
Nasarar da ya samu a Tokyo na nufin ya samu nasara a manyan gasar gudun famfalaƙi 13 cikin 15 da ya yi tun a lokacin da ya fara mai irin wannan nisan a 2013, inda cikin tarihin da Kipchoge ya kafa a duniya har da gudun da ya yi a birnin Berlin a cikin sa'a 2:01:39 a shekarar 2018.
Ɗan wasan mai shekara 36, shi ne ɗan wasan gudun famfalaƙi da ya fi shekaru da ya yi irin wannan nasara tun bayan Carlos Loppes na ƙasar Portugal wanda a lokacin yake da shekara 37 a 1984 inda ya samu nasara da bayar da tazara tun daga 1972.