Abu bakwai da ke haddasa gobara a lokacin hunturu a Najeriya
Abu bakwai da ke haddasa gobara a lokacin hunturu a Najeriya
Ku latsa wannan alamar hoton da ke sama domin kallo da sauraro:
Shugaban hukumar kashe gobara ta Najeriya, Alhaji Ibrahim Liman ya ce a lokacin hunturu ne aka fi samun tashe-tashen gobara fiye da kowane yanayi.
Alhaji Ibrahim Limana ya lissafa wasu dalilai guda bakwai da ke janyo tashin wutar wadanda kuma suna da alaka da sakaci na mutane, a gidaje ko ofisoshi ko kuma kasuwanni.
Shugaban hukumar ta kashe gobara ya ja hankalin al'umma cewa da sun ga gobara su gaggauta kiran su a kan lambar gaggawa ta 112.