...Daga Bakin Mai Ita tare da Hamisu Lamido Iyantama

...Daga Bakin Mai Ita tare da Hamisu Lamido Iyantama

Ku latsa hoton sama domin kallon bidiyon:

Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.

A wannan kashi na 84 din, shirin ya tattauna da fitaccen dan was an Hausa, furodusa kuma darakta a masana’antar Kannywood wato Alhaji Hamisu Lamido Iyantama.

A cikin hirar, Iyantama ya yi mana bayani game da rayuwarsa.

Shi ne mai shirya fim na farko da ya fara biyan ƴan wasa kudin fitowa a fim kamar yadda ya ce mana.

Sannan fim ɗinsa na Badaƙala na daga cikin na farko-farko da aka fara rawa da waƙa a ciki.

Baya ga kasancewarsa ɗan fim, Hamisu Iyantama ɗan kasuwa ne mai zuwa ƙasashen duniya don shigar da kaya Najeriya.

Kazalika ɗan siyasa ne da ake damawa da shi, inda har ya taɓa tsayawa takarar gwamnan jihar kano.

Iyantama ya yi fina-finai da dama da ya ce ba zai iya tuna adadinsu ba.

Ya ziyarci ƙasashe da dama don harkokin kasuwanci ko don yin kwasa-kwasan da suka danganci harkar shirya fina-finai.

A yanzu haka Iyantama ya buɗe wata katafariyar makaranta inda za a dinga yin karatun difloma da kwasa-kwasai na neman ƙwarewa kan tsara da shirya fina-finai da kuma ba da umarni.

Ya ce za a fara karatu a makarantar ne a cikin wannan shekara ta 2022.

A zagayen da BBC ta yi a cikin makarantar ta ga har da situdiyo na naɗar sauti da aka tsara yadda za a yi wa ɗaliban bayanin komai a bayyane.

Tsarawa da gabatarwa: Halima Umar Saleh

Ɗaukar bidiyo/Tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir