Yadda ake katse mutane cikin ladabi

Tattaunawa a wayar tarho

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Sirrin katse mutane shi ne ka girmamasu lokacin da kake katse su

Idan aka bude layin waya domin tattaunawa da mutane da yawa, kowa kan so ya tofa albarkanci bakinsa. Amma, ta yaya za ka iya katse mutane ba tare da bata wa kowa ba?

Tattaunawar waya da mutane da yawa a lokaci guda abu ne mai wuyar sha'ani, kama daga wanda za ka ji karar ruwan famfonsa a kunne, zuwa ga wadanda su ka iso daga baya amma su ke tambayoyin da tuni an bada amsoshinsu. Ga kuma wadanda wayoyinsu kan katse su yi ta kokarin sake shiga tattaunawar.

Sai dai kuma, abinda yafi komai wuya a irin wannan tattaunawar ta waya shi ne, yadda za ka samu ka ce wani abu. Babu wata alama da zaka iya nunawa da gabbanka ta cewa ka na son yin magana kamar yadda akan yi idan ana hira gaba da gaba. Ga shi kuma mutane da yawa na son a ji ta-bakinsu.

Tambayar anan ita ce; yaya za ka iya yin magana ba tare da ka bata wa kowa ba?

Yin magana

Sylvain Barrette, dan kasar Canada ne bangaren da ke amfani da harshen Faransanci, wanda ya ke aikin banki a birnin Frankfurt na kasar Jamus. Yace katse mutane ya zama dole; "Babu yadda ka iya, sai ka yi."

Duk da haka, akwai dabarun da yake bi kafin ya katse mutane. Ga misali, Barrette yafi katse Faransawa fiye da Jamusawa "saboda Faransanci na kunshe da hayaniya da yawa," a cewarsa.

"Faransawa sun saba hirar da ba mai jin wani don haka mun saba katse juna. Jamusawa kuwa sun saba magana dalla-dalla," in ji Barrette. "Amma dai sirrin shi ne ka girmama mutane lokacin da kake katse su."

Na farko dai, ka tabbatar ka na da kwakkwaran dalilin da ya sa ka yi kutsen, in ji Richie Frieman, marubucin littafin kyakkyawar mu'amala a zamanance mai suna "REPLY ALL... And Other Ways to Tank Your Career".

Dalilin na iya zama na kokarin iza mutane su yanke hukunci, tattara bayanin matsayar da aka cimma ko kuma ware wadansu bayanan da za'a tattauna akai nan gaba. Mataki na biyu shi ne ka saurari yadda sauran mutane ke katse wasu domin fahimtar hanyoyin da su ka karbu wurin mutanen da ka ke tattaunawar da su.

Kar ka bada kunya

Da zarar ka katse mai magana, to kowa zai mai da hankali gare ka, in ji Frieman, don haka kar ka yi abin kunya.

"Ka tabbatar maganar da zaka fada mai muhimmanci ce. Ba wai kawai 'na amince da wane ba'". Idan kutsen naka na da ma'ana, zai fi saurin samun karbuwa, a cewar Frieman.

"Na kan ji haushi idan wani ya ce, 'Ina ga ya isa haka'… Wannan wulakanta mai maganar ne," in ji Frieman. Duk lokacin da ka nuna gudunmawar wani ba ta da amfani, za a kalle ka a matsayin mara mutunci.

Domin kauce wa haka, akan katse mutane ne a hankali, tare da gode wa mai maganar bisa batutuwan da yake fada.

Daga nan sai Frieman ya karkata akalar hirar ta yadda wancan mai surutun ba zai ci gaba da zuba ba. Ya kan ce, "Wannan maganar taka na da muhimmanci, kuma zamu iya tattaunata nan gaba, kasancewar yanzu lokaci na neman kwace mana."

Asalin hoton, Frieman

Bayanan hoto,

Ka tabbatar ka na da kwakkwaran dalilin da ya sa ka yi kutsen

Ban da in-da-in-da

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Katharina Barta, ma'aikaciyar kamfanin BASF a Jamus, ta jagoranci wani bangare na shirin samar da tashoshin 'yan yawon bude ido a manyan birane shida dake fadin duniya. A lokacin aiki ta na kashe mafi yawan lokutanta ne wurin tattaunawa kai tsaye da mutane da dama a wayar tarho.

Tace katse maganar sauran mutane na daya daga cikin aikin jagorar tattaunawar, kuma abin ya zo da sauki kasancewar ita da abokan aikinta sun dauki lokaci mai tsawo wurin tantance rawar da kowa zai taka. Lokacin da ake laluben hanyoyin da za'a bi wurin gudanar da aikin, Barta kan kyale mutane su yi ta zuba zance, amma bayan da aiki ya kankama ta kan katse su akai akai.

A mafi yawan lokuta ta kan katse mai magana ne idan ta gamsu cewa ta gama jin hujjojin masu goyon baya da masu sukan ra'ayin da ake tattaunawa kuma lokaci ya yi da za'a dau mataki. "Wani lokacin ki na bukatar tsoma baki domin ki tabbatar ana tattaunawa kan magana mai muhimmanci," in ji Barta.

Togaciya

Wani lokacin da yake da saukin cusa baki, shi ne idan mutane su ka fara magana a tare ba mai jin ta wani ko kuma lokacin da aka yi tsit, in ji Frieman. "Ba wanda zai ga laifinka don ka yi kokarin cewa wani abu a lokacin da kowa ya yi shiru."

Ko kuma ka yi dabarar da Barta ke yi: "Na kan yi togaciya tun kafin a fara tattaunawar. Na kan bayyana musu cewa idan na ga maganar da ka kawo ta fita daga hurumin abinda muke tattaunawa zan iya ce maka 'ba yanzu ba sai dai karo na gaba'. Wannan togaciyar, kan taimakawa mutane su amince da duk wani kutse da za ka yi musu a lokacin da ku ke tattaunawar.

Ta kara da cewa: "Togaciya, kan sa mutane su fi sakin jiki idan an katse su."