Wani sabon littafi na ikirarin samo sirrin karbuwar litattafai

Litattafan da suka fi karbuwa a kasuwa

Asalin hoton, Olivia Howitt

Bayanan hoto,

Marubuta sun bayar da shawarwari game da dabaru da matakan da marubuci ya kamata ya dauka domin littafinsa ya samu karbuwa a kasuwa

Darussan koyar da rubutu da dama kan jaddada muhimmancin jumlar farkon littafi wurin samun karbuwarsa a wurin masu karatu. Marubutan wani sabon littafi mai taken 'The Bestseller Code' sun amince da wannan ra'ayi.

Jodie Archer da Matthew L. Jockers sun ce jumlolin da fitattun marubuta irin su Sylvia Day, da Toni Morrison, da Jeffrey Eugenides da Virginia Woolf kan yi amafani da su wurin bude labaransu, kan dunkule rikicin da ke cikin littafi mai shafuka 300 a cikin jumla guda mai kalmomi 20 ko ma kasa da haka.

Ko da yake Archer da Jockers na da dangantaka da harkar littattafai - domin kuwa ita tsohuwar edita ce a kamfanin wallafa littattafai na Penguin, yayinda shi kuma farfesan nazarin Ingilishi ne a Jami'ar Nebraska - wannan shawarar ta su ta dogara ne kacokan a kan alkaluman lissafi.

Archer ta kuma yi aiki a kamfanin Apple, shi kuma Jockers yana dga cikin wadanda suka kafa cibiyar gwaje-gwajen adabi ta Jami'ar Stamford. Ta hanyar amfani da na'urorin kwamfuta, sun bi diddigin littattafan kagaggun labarai fiye da 20,000 wadanda aka wallafa a shekaru 30 da suka gabata, inda suka yi nazarin jigo, da zubi, da warwarar labarin, da taurarin littattafai da kuma abubuwan da suka danganci salo da wurin da aka gina labarin a kai.

Sun ce idan aka tattara wadannan bayanan, lissafinsu zai iya hasashen ko littafi zai yi kasuwa ko ba zai yi ba. Lissafin nasu ya nuna cewa littafin 'The Art of Fielding' na Chad Harbach na da damar yin fice a kasuwa da kaso 93.3 cikin dari. Littafin Mitch Albom mai taken 'The First Phone Call From Heaven' ya samu maki 92.2 cikin dari, haka ma 'The Lincoln Lawyer' na Michael Connolly.

"Samuwar wadannan alkaluman lissafi sun faranta ran wadansu mutane, sun fusata wadansu, sannan kuma da dama sun shiga tantama", in ji Archer da Jockers.

Asalin hoton, Olivia Howitt

Bayanan hoto,

Kullum ka kasance dauke da littafin rubuta sababbin abubuwa

In da ace

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tuni dai masana suka dade suna bayar da shawarwari game da dabaru da matakan da marubuci ya kamata ya dauka domin littafinsa ya samu karbuwa a kasuwa. A cewar Stephen King, ba zubin labari ne ya kamata ya dauki hankalin marubuci ba sai dai yanayin da za a gina labarin a kai, wanda za a dunkule shi da fadin "in da ace", wato me zai faru in da kaza da kaza za su faru? Haka kuma ba sai ka zurfafa bincike ba, ka yi hattara da yadda taurarin littafin ke tattaunawa da juna, kuma ka tuna cewa mutane suna son karanta labarin ciki. "Ban san dalili ba amma dai su na so," in ji Stephen King. A cikin littafin "Writing With the Master" mashiryin tallace-tallace a garin Chicago Tony Vanderwarker ya bayyana sirrika uku na daukakar littafi da ya ce fitaccen marubuci John Grisham ne ya koya masa: ka samu dunkulallen labari, wanda tsakiyarsa ke da kwari sannan kuma yana da jan hankali. Sophie Kinsella, marubuciyar jerin littattafan Shopaholic cewa ta yi sirrin rubuta littafin da zai karbu a kasuwa shi ne: kullum ka kasance dauke da littafin rubuta sababbin abubuwa, ka tsara yadda za ka rika rubuta labarai, sannan kuma ka shakata da barasa idan ka ji rubutun ya cushe ma.

Mutane kadan ne a duniya suka fi Jonny Geller, shugaban sashen wakiltar marubuta na kamfanin Curtis Brown, sanin sirrin yadda littafi ke samun karbuwa a kasuwa. Geller, wanda shi ne wakilin fitattun marubuta irinsu John le Carré, da Tracy Chevalier, da David Nicholls, a wurin kulla yarjejeniya da kamfanonin wallafa litattafai, ya gabatar da wata laccar TEDx, inda ya bayyana muhimman abubuwa biyar da litattafan da suka fi karbuwa a kasuwa suka kunsa bisa nazarin da ya yi na tsawon shekaru 20. Abubuwan sun hada da gamsasshiyar muryar bayar da labari, da kuma kwakkwaran labarin da zai iya dauke mai karatu daga duniyar da ya saba da ita zuwa wata duniyar ta daban. Haka kuma labarin na bukatar jigo mai taba zuciya fiye da ainihin abin da ya ja hankali a cikinsa. Misali littafin 'Room' na Emma Donoghue ya zarta jigon wata uwa da danta da aka kulle a daki tsawon shekaru, ya tabo batun irin tsantsar son da iyaye ke yi wa 'ya'yansu. Ya ce kuma, wani lokacin littafi kan dace ne da zamanin da ya fito ya "samar da mafaka a lokacin da duniya ke cikin yamutsi, ya bayyana tsoro lokacin da ake cikin fargaba, ko kuma ya tallata soyayya a lokacin da ake cikin jin dadi."

Asalin hoton, Olivia Howitt

Bayanan hoto,

Sirrin karbuwar littafi shi ne ka tabbatar mai karatu ya juya shafi na gaba cike da shaukin gano mai ya faru.

Alkaluman lissafin Archer da Jocker sun dace da mafi yawan shawarwarin da aka saba bai wa marubuta, kawai dai samuwar na'urorin tattara bayanai tare da nazari a kansu ta ba su damar nuna muhimmancin wasu abubuwan da aka sani kamar samun fadi-tashi a cikin warwarar jigon littafi. Sai dai kuma wannan tsarin na son a bi diddigi, ya sa suna iya gano abin da mutum ba zai gane ba saboda dadin labari ya kwashe shi. Misali, sun gano cewa jima'i na sayar da littafi amma iri guda kurum, wanda daman an yi shi ne don batsa.

Amma anya da akwai wata dabarar da za a iya amfani da ita ko da yaushe domin littafi ya samu karbuwa? Da na tambayi marubuci Jeffrey Archer sai ya ce: "Akwai mana. Kurum ka tabbatar mai karatu ya juya shafi na gaba cike da shaukin gano mai ya faru. Shi ke nan."

Kashe basira

Hakan bai hana masu burin rubuta littafi kokarin nemo sirrin ba - wani lokacin kuma su kan dace da gagarumar sa'a. Lokacin da wata 'yar fim Jacqueline Susann ta so rubuta littafinta na farko kuma na karshe a 1962, ta bayyana kudirin samar da labari mai kasuwa kamar irin litattafan Harold Robbins, wanda shi ke tashe a zamanin. Don haka sai ta sai littattafansa uku da suka fi kasuwa ta duba kamanceceniyar da ke tsakaninsu sannan ta rubuta nata, bisa wannan tsarin da ta gano. Nata littafin, 'Valley of the Dolls' ya zamo littafin da aka fi saurin cinikinsa a tarihi kuma har yanzu ana ci gaba da sake wallafa shi.

A daya bangaren kuma, kwasa-kwasan gaba da digiri da ake gudanarwa a manyan jami'o'i na nuna cewa rubutu baiwa ce da ba za a iya koyar da ita ba, sai dai a nuna maka yadda za ka kyautata baiwarka. Daya daga cikin litattafan da suka fi samun kasuwa a bana, 'Sweetbitter' na Stephanie Danler ya bayar da labarin yadda rayuwa ke gudana ne a cikin wani kayataccen shagon sayar da abinci a birnin New York.

Danler ta rubuta abin da ta sani ne kasancewar ta taba yin aikin shagon sayar da abinci a New York, amma kuma salon rubutunta ya samo asali ne daga digiri na biyu da ta yi a kan rubuta kagaggun labarai. Daya daga cikin malamanta, wacce ita ma fitacciyar marubuciya ce, Helen Schulman, ta ce babu wasu alkaluman lissafi da za su bayyana sirrin daukakar Danler: "Rayuwar Stephanie da baiwarta su ne suka yi tasiri a kan littafin 'Sweetbitter' ba wasu alkaluman lissafi ba."

Asalin hoton, Olivia Howitt

Bayanan hoto,

Littafi daya ne kurum 'The Circle' na Dave Eggers ya cika duk sharuddan Archer da Jockers inda ya samu maki 100%

Idan har da akwai dabarar da marubuta za su yi amfani da ita domin littafinsu ya samu karbuwa, anya hakan ba zai kashe musu basira ba, ya zama kowa ya koma yin abu guda? "Babu abinda ke yi wa mai kirkirar labari kamar ace za a takaita tunaninsa," in ji Geller. Sai dai wata marubuciya da ta ce za ta so ta samu wadannan alkaluman lissafin karbuwar littafin ita ce Naomi Alderman, marubuciyar fitattun littattafai irin su Disobedience. Ta ce: "Kowa ya san akwai irin littattafan da kan samu karbuwa a kasuwa fiye da wasu saboda mutane sun fi son abin da suka saba da shi. Sai dai ni nafi sha'awar littattafan da suka yi kasuwa bayan sun sabawa wadancan ka'idojin ko kuma littattafan da ba sa kasuwa duk da kasancewar sun yi rubutu da kyau."

A hakikanin gaskiya, akwai littattafan da suka sabawa alkaluman lissafin Archer da Jockers. A cikinsu akwai 'The Help' na Kathryn Stockett wanda na'urar ta ce ya na da kashi 50 cikin dari na shika-shikan karbuwa a kasuwa, sai ga shi kuma ya yi fice fiye da zatonsu. Haka kuma littafi daya ne kurum 'The Circle' na Dave Eggers ya cika duk sharuddan Archer da Jockers inda ya samu maki dari bisa dari. Littafin dai an bude shi da jumla mai daukar hankali, ga shi da salo mai kyau da tauraruwa mai kokari, sannan kuma ya danganci fasahar zamani. Sai dai kuma da aka fitar da shi kasuwa, littafin 'The Circle' ko kudin wallafa shi ba a mayar ba, balle a yi zancen riba!