Me ya sa fatar tabo ta bambanta da mai lafiya?

Amma tambayar anan ita ce: menene tabo?
Bayanan hoto,

Faduwar da na yi ta jawo har tsakwankwani sun nutse karkashin fatata.

Tabo alama ce da ke shaida wa duniya mun samu miki a baya, amma me ya sa fatar wurin ke bambanta da sauran jiki?

Lokacin ina da shekaru 10 ko 11, na ji ciwo a gwiwata lokacin da nake 'yar tsere da abokaina a wani wurin wasa mai cike da kananan tsakuwoyi.

Faduwar da na yi ta jawo har tsakwankwani sun nutse karkashin fatar gwiwata.

Da aka kai ni asibiti, bayan da ma'aikatan jiyya su ka wanke jinin, su ka kuma cire tsakwankwanin, sai suka sa magani su ka wanke mikin.

Na ji zafi, amma hakan ya sa babu wata kwayar cuta da samu shiga. Sai dai na samu tabo.

Akwai wani lokaci kuma da na cake hannuna da wuka a kokarin bude wasu akwatuna a dakinmu na jami'a.

Duk da kokarin neman maganin da na yi, a wannan karon ma sai da na samu tabo a hannun haguna tsakanin babban dan yatsa da mai yatsan farko.

Kusan duk wanda na sani ya na da tabo daya ko biyu a jikinsa. Amma tambayar anan ita ce: menene tabo?

Da fari dai, tabo, wani abu ne da kan biyo samuwar rauni kowanne iri ne.

Saboda shi ne abinda jiki ke haifarwa a lokacin da yake gyara inda rauni ya lalata.

Bayanan hoto,

Kusan duk wani dan adam yana da tabo a jikinsa

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sai dai kuma sauran dabbobi da kan sake samar da sassan jikinsu da su ka gutsure, kamar jela ko kafa, ba sa yin tabo a wurin da sabuwar gabar ta fito.

Bayan samun rauni, kuna, ko miki, abu na farko da jiki zai yi shi ne zubar da jini.

Na biyu shi ne daskarar da jinin. Bangaren da ke saman daskararren jinin, shi ne ke kekashewa ya zama bawo domin kare raunin daga abubuwan da za su iya cutar da shi.

To a karkashin wannan bawon ne, wasu kwayoyin halitta da ake kira fibroblasts ke taruwa, wadanda aikinsu shi ne maye gurbin bawon da tabo.

Kodayake ana yin fatar tabo da irin sinadiran protein mai suna collagen, wanda ake yin lafiyayyar fata da shi, tabo ya kan bambanta da sauran fatar jiki a ido da kuma wurin tabawa.

Masana lissafi a jami'ar Warwick ta Ingila John C Dallon da Jonathan A Sherratt sun bayyana dalilin haka a wani bincike da su ka wallafa sakamakonsa a 1998.

Su ka ce: "a jikin mutane, da sauran dabbobi masu matsattsiyar fata, ana shirya sinadirin collagen ne a karkace a lafiyayyar fata, a kuma jera shi a mike a fatar tabo".

Wannan ba karamar hikima ba ce idan mu ka lura. Budadden ciwo na ba da damar cutar da jiki ta hanyoyi da dama.

Don haka, maimakon a gina fatar da za ta rufe ciwo a hankali kamar yadda ake samar da ragowar fata, sai halittu masu agajin gaggawa a jiki, su kai dauki a kan kari.

Kamar kai ne rufin gidanka ya ke zuba da damina. Ba bukatar jiran kafintan da yafi kwarewa a garinku idan za ka iya samun wanda bai kai shi a nan take.

Musamman ma idan wanda bai kai shin ba, zai gudanar da aikin a rabin lokacin da kwararren zai dauka kuma a rabin farashi.

Gaggawar kare jikin ita ce tafi muhimmanci fiye da samar da kyakkyawar fata.

Bayanan hoto,

Fatar da ba ta da tabo ta banbanta da mai tabo

Kodayake wasu kan yi alfahari da tabonsu, wasu kuwa kyamarsa su ke yi.

Babu wata hanya ta magance afkuwar tabo kwata-kwata, amma akwai hanyoyin rage shi.

Wannan ne dalilin da ya sa likitoci kan dinke bakin ciwo domin rage fadin tabo.

Idan kuma tabon ya yi muni da yawa, likitan fata kan yade shi, ya sake dinkin wurin ta yadda wani sabon tabon da bai kai na farkon muni ba zai maye gurbinsa. Saboda ba za'a iya hana tabon baki daya ba.

Sauran hanyoyin da ake bi wurin rage tabo sun hada da daye fatar sama ta hanyar amfani da sinadirai. Fatar kan warke daga wannan sabon raunin, kuma sabuwar da za ta maye gurbinta ta kan fi waccan kyan gani.

Sai dai duk da yake wadannan hanyoyin za su iya rage tsananin tabo, babu wata dabara da za ta iya cire tabo dungurumgun.

Abinda kawai ke kawar da tabo shi ne dashen fata, wanda zai rufe tabon asali, amma kuma shi ma yak an haifar da wani sabon tabon.

Don haka kafin lokacin da likitoci zasu samo hanyar kawar da tabo, babu abinda za mu iya yi akai sai dai bada labaran yadda aka yi muka samu namu tabon.

Idan kana son karanta na turanci sai ka latsa wannan Why is scar tissue different to normal skin