Sirrin da ake boye maka game da shugabanci

Wasu suna boye sirrin da ke cikin zama shugaba
Bayanan hoto,

Shugabanci abu ne mai sarkakiya a tsakanin mutane

Shekaru da dama kafin Roman Stanek ya kafa kamfanin GoodData, mai samar da manhajar nazarin bayanai a kwamfuta, da ke garin San Francisco a Amurka, shi kwararren injiniya ne.

Bayan samun karin girma a kamfanonin manhajar kwamfuta dabam-daban, wannan injiniyan ya samu kansa a 1997 a matsayin shugaban kamfanin NetBeans.

Nan take Stanek ya fahimci ya na bukatar samun kwarewar da bata danganci aikin injiniya ba domin zama ingantaccen shugaba.

Lamarin ba zai masa da sauki ba.

Lokacin da Sun Microsystems ya yi tayin sayen kamfanin a 1999, Stanek ya yi zaton zai iya tattaunawa da su shi kadai, kafin ya gano cewa kimanin mutane 100 ne Sun Microsystems ya dora wa aikin tattaunawar.

Sun sha samun sabani kuma lokaci-lokaci Stanek kan ji kar ma a fasa cinikin baki daya.

Wannan ita ce hanyar da ya dandani shugabanci, kuma lallai bai ji da dadi ba.

Idan kai ma ka na kan hanyar samun shugabanci, to ya kamata ka kwana cikin shiri.

Bayanan hoto,

Ya kamata mutum ya shirya sauraron abubuwa marasa kau a wurin aikinsa

Wadannan su ka samu shugabancin kamfani sun ce rike kananan mukamai ba ya taimakawa wurin kwarewa a shugabanci, inda kowanne hukunci da zaka yanke kan zama mai wuya.

To yaya zamu iya shiryawa shugabanci ke nan?

Ta hanyewar sabawa da mummunan yanayi.

Na farko, ka shirye tunkurar duk abinda ba shi da dadin sha'ani a kamfanin da za ka shugabanta.

Idan kai shugaban kwarai ne, dama ka nada wadanda za su rika kula da ayyukan yau-da-gobe.

Hakan na nufin batutuwan da za su rika isa gare ka sai mara sa dadi, wadanda su ka sha kan kowa.

Don haka abu na farko da zaka kware a kai shi ne kula da lamura masu wuyar sha'ani, in ji Linda A Hill, farfesa a harkar shugabancin kamfanoni a makarantar kasuwanci ta jami'ar Harvard.

Daukar mataki idan ka na shugabantar kamfani yafi wahala da sarkakiya, fiye da lokacin da ka ke shugabantar wani bangare.

Inda a da ka kan yi tunanin wadanda ke karkashinka ne kadai, idan ka zama shugaba, sai ka duba yadda matakin zai shafi sauran sassan kamfanin.

Daukar wadannan matakan ya na kara tsananta kasancewar ka yi nisa da inda matsalar ta ke.

"Komai kwarewarka a shugabanci, ka na bukatar wasu gogaggun ma'aikata da ka amince da su wadanda zasu tallafa wurin tafiyar da kamfanin," in ji Hill.

Nemo abokai

Da zarar ka samu kanka a matsayin da kai ka ke tafiyar da kamfani, sai ka yi kokarin nemo abokan da jirgi daya ya kwaso ku, in ji Mark Fagan, babban jami'i a kamfanin kididdigar kudi na Cooperman's office da ke Connecticut a Amurka.

Fagan ya yi binciken kudi a dubunnan kamfanunnuka a shekaru 31 da ya kwashe ya na aikinsa, inda ya ga wasu manajojin da su ka kasa tasiri bayan sun zama shugabanni.

Babbar matsalar da su ka fi fuskanta kuwa ita ce rashin abokan shawara.

Fagan ya ce: "Shugabanni na bukatar mukarraban da za su ba su shawara amma ba lallai mataimakansu a kamfanin ba, kasancewar matakan da za su dauke zasu iya shafar abokan aikin na su.

Mashawartan da ka ke bukata su ne shugabanni irinka wadanda ke aiki wasu kamfanonin dabam."

Zabi ya rage naka

Komai taka je taka zo dai, yanke hukuncin karshe ya na hannunka - mai kyau da mara kyau.

Daukar wannan nauyin shin abinda yafi komai wuya idan ka zama shugaba, a cewar Autumn Manning, shugabar kamfanin kula da ma'aikata na YouEarnedIt.

Wasu lokutan dole ne ka dauki matakin da zai bakantawa mutanen da ka kwashe shekaru da yawa ka na aiki da su.

Ita dai Manning ta gano inda ta ke da kwarewar da za ta iya yanke hukunci da kanta da kuma inda ta ke neman taimako.

Ta ce tafi kwarewa a fannin abubuwan da kamfaninta ke samarwa, amma idan batun lissafin kudi ya taso, sai ta nemi shawarar babban akantanta.

"A karshe dai ke za ki yanke hukunci. Idan ki ka tsaya jan kafa, komai zai iya tsayawa cik, ana jiranki."

Bayanan hoto,

Ya kamata ka shirya zama shugaba a wurin aiki

Da koyo kan iya

Lokacin cinikin NetBeans, Stanek ya koyi darussan da ke tasiri akan shugabancinsa bayan shekaru 17.

An sha samun sabani da sa-in-sa tsakanin bangarorin biyu akan 'yan kananan kalmomin da ke cikin kwangilar.

Sai da Stanek ya dauki na sa ma'aikatan da za su tattauna da daya bangaren, amma sun ci gaba da samun sabani kasancewar su na aiki ne daga ofisoshi dabam-daban.

Ko da ya kira bangarorin biyu ya hada su zama wuri daya sai aka daidaita.

Ya ce: "Abinda na koya shi ne, nisa kan kawo rashin amincewa da juna."

Idan kai ma ka na kan hanyar samun shugabanci, zaka iya iya haduwa da irin wannan matsalar farkon hawanka, amma idan ka koyi darasi daga matsalar, ka fuskanci yadda ya kamata ka tafiyar da harkarka don gaba, hakika za ka ji dadin mike kafafunka a kujerar mulki.

Idan kana son karanta wannan bayani da harshen Turanci, sai ka latsa wannan What nobody tells you about becoming the boss