Sa rai da nasara na iya kawo lalaci

Kusan kowa yana da irin wannan dabi'a
Bayanan hoto,

Sa rai da nasara na taimakawa amma kuma zai iya kashe gwiwa

Ka na son ka yi nasara? Me yiwuwa ne fata nagari ke hana ka cimma buri

Kimanin shekaru 15 da su ka wuce lokacin da Michael Stausholm ya kafa wani kamfani tare da abokinsa, abokin ya nuna masa cewa kamfanin zai samu daukaka kuma kasuwancinsu zai yi riba.

Stausholm ya amince da bayanin, kuma haka ya kara masa kwarin gwiwa har ya ji kamar fadar daidai take da cikawa. Ko ba komai ai an ce tunanika, kamanninka ko?

"Sa rai da nasara, dabi'a ce da ta ratsa jinin mafi yawan masu kafa kamfanonin kansu," in ji Stausholm, mazaunin Copenhagen wanda ya taba yin aiki a kamfanin safarar jiragen ruwa na Maersk inda daga bisani ya zama mai bada shawara ga manyan kamfanoni kan abubuwan da suka shafi dorewar harkokinsu.

Bayanan hoto,

Michael Stausholm ya ga matsalar tunani ta zazzafar hanya

Ya ce: "Idan ba ka sa rai da samun nasara, ba za ka iya kafa kamfani ba."

Amma lokacin da kamfaninsu ya karye, ya koyi darasi mai muhimmanci.

Wato sa rai da samun nasara shi ma ya na da tasa illar. "Sa rai da samun nasara kurum ba zai kai ka ko'ina ba - sai ka hada da kallon gaskiyar lamari".

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sa rai da samun nasara na cikin abubuwan da jagororin kamfanonin kasuwanci su ka sa gaba akalla tun a 1936 lokacin da Napoleon Hill ya wallafa littafin 'Think and Grow Rich'.

Bayan shekaru 20 kuma Norman Vincent Peale ya rubuta 'The power of Positive Thinking', wanda kawo yanzu an sayar da fiye da kofe miliyan 21 a fadin duniya.

A baya-bayan nan kuma Rhonda Byrne ta rubuta 'The Secret' wanda shi ma yake kara jan hankalin masu kamfanonin kasuwanci game da muhimmancin sa rai da samun nasara.

A cewar wadannan littattafan sa rai da samun nasarar, shakka ko tunanin rashin nasara na zama kalubale ga samun nasarar kasuwanci.

Sai dai kuma sababbin binciken da aka gudanar a baya-bayan nan na nuna cewa sa rai da samun nasara na da iyakarsa- kai ya na ma kawo matsaloli.

Yaudarar kai

Gabriele Oettingen, farfesar nazarin halayyar dan Adam a jami'ar New York, wacce ta rubuta littafin 'Rethinking Positive Thinking: Inside the New Science of Motivation', ta ce lokacin da ta fara nazarin sa rai da samun nasara, ta gano cewa karfin bugawar jinni na raguwa a duk lokacin da mutane su ke kyakkyawan zaton cewa za su samu rayuwa mai kyau a gaba kamar samun aikin yi ko samun karin kudi.

"Matsalar ita ce mutane ba sa zage damtse su yi kokarin cika burikansu," in ji Oettingen.

Mafi yawan lokuta, idan mutane su ka fara mafarkin cimma burinsu sai su kasa zage damtse wurin ganin sun biya bukatunsu.

Alal misali, Oettingen ta gano cewa, shekaru biyu bayan dalibai sun kammala jami'a da kyakkyawan zaton samun ingantaccen aiki, sai ka tarar su na aikin da ba su kai na daliban da suka kammala jami'a da fargabar samun aiki ba.

Masu kyakkyawan zaton ba sa aikawa da takardun neman aiki da yawa kamar na masu fargabar ba za su samu yadda su ke so ba.

Ta ce; "Idan su ka yi tunanin samu, sai su ji kamar ma burinsu ya riga ya cika," hakan ke karya musu lagon ci gaba da kokarin nema.

Bayanan hoto,

Tunanin mafita ka iya janyo mutum ya zama malalaci.

Nimita Shah, darakta a kamfanin nazarin halayyar bil'adama kan batutuwan da su ka shafi sana'a da ke birnin London 'The Career Psychologist', ta ce mutane da daman a zuwa wurinsu ne da takaicin cewa sun kasa cimma muradunsu kuma sai su fara zargin kansu cewa tunanin rashin nasarar da su ke yi na da alaka matsalar da suke samu.

Shah ta ce; "Fata nagari na iya kawo kaimi na dan lokaci, amma ya na sa mutane jin ba dadi idan tafiya ta yi nisa."

Haka Allah ya yi mu

Idan haka ne, kamata ya yi ke nan kullum mu kasance cikin fargabar cewa akwai matsala a cikin duk abubuwan da zamu yi?

Abin da kamar wuya. Fata nagari wani bangare ne na dabi'ar mutane, a cewar Tali Sharot, marubuciyar 'The Optimism Bias' kuma darakta a cibiyar bincike ta 'Affective Brain Lab' wacce ke nazarin yadda tunani yake tasiri akan kwakwalwa.

Ta na kokarin gano tasirin mummunan zato ne lokacin da ta gano cewa an gina halittar mutane ne kan kyakkyawan zato.

A gwaje-gwajenta na farko, ta nemi mutane da su yi hasashen faruwar wani mummunan abu a rayuwarsu kamar batawa da masoyansu ko kuma korarsu daga aiki.

Sai ta gano cewa mutane na maye gurbin mummunan lamari da kyakkyawan zato- misali su kan ce, na bata da masoyina amma na samu wanda ya fi shi.

"Hakan ya bata min bincikena" in ji Sharot, amma ta gano cewa mutane sun fi karkato ga fatan alheri.

Bayanan hoto,

Irin yadda tunane yake a kwakwalwar dan adam

Ta ce; "Su kan dauka cewa gaba tafi baya kyau."

Wannan sa rai da samun nasara, wanda Sharot ta kiyasta cewa ana samunsa a kaso 80% na al'ummar kowacee kasa, na taimakawa wurin ingiza mutane su yi abubuwan da su ka kamata. Sakamakon bincike ya kuma nuna cewa masu kyakkyawan fata sun fi samun tsawon rai da ingantacciyar lafiya.

Ta kuma kara da cewa fata nagari na iya taimakawa mutane wurin gyara rayuwarsu; wato wadanda su ke sa ran ganin su na motsa jiki tare da cin abinci mai kyau su kan zama masu yin hakan.

Haka kuma sa rai da samun nasara shi ke bai wa mutane damar jurewa idan suka samu koma baya.

Sai dai kuma wannan kyakkyawan fatan na sa mutane su raina hatsarin da suke fuskanta. Wannan na nufin kodayake sa rai da samun nasara na da rana, duk da haka ya na iya jawo mu kasa gane, alal misali, yawan kudi da lokacin da muke bukata wurin kafa wani sabon kamfani.

Ciza-ka-busa

Tun da yake an halicce mu ne bisa tsarin yi wa kanmu kyakkyawan fata, ashe ke nan sai mun tarbiyyantar da kanmu wurin gano matsalolin da zamu iya fuskanta a kokarin cimma nasarar abinda muka sa gaba.

Bayan binciken fiye da shekaru 20, Oettingen ta kirkiro wani ma'auni da ta kira WOOP wanda ke auna abinda muke fata, matsalalon da zamu iya fuskanta, hanyoyin da zamu iya kauce musu, da kuma yadda zamu tabbatar da burin namu.

Ma'aunin da ake iya samu a shafin intanet ko kuma manhajar wayar komai-da-ruwanka, wanda mutane za'a iya amfani da su wurin gano hanyoyin da zasu cimma manufofinsu ta hanyar gwama fata nagari tare da bada kulawa ta musamman ga abubuwan da za su iya kawo cikas.

Ga misali, ka na iya son kafa kamfani amma kuma ka san baka son tambayar mutane su ba ka kudi kumi ba ka san shafe sa'o'i masu yawa ka na aiki.

Don haka ko dai ka dauki matakan kaucewa wadannan matsaloli kamar hada kai da wanda ya kware wurin sayar da haja ko kuma tabbatar da ka gudanar da aikin cikin wani kayyadadden lokaci.

Ko kuma idan ka ga matsalar ta yi girma da yawa sai ka kwance niyyarka maimakon ka fara ka kuma kasa.

"Ka ga ke nan ka na iya sauya aniya ba tare da ka ji ba dadi ba," in ji Oettingen.

Lokacin da Stausholm ya kafa kamfanin Sprout, mai samar da fensir din da ba zai yi illa ga muhalli ba ya yi amfani da darasin da ya koya daga karyewar kamfaninsu na baya.

Duk yarjejeniyar da zai kulla ya na tabbatar an yi a rubuce, sannan kuma ya na fitar da tsare-tsaren matakan da zai dauka idan lamarin ya zo da matsala.

A yanzu haka kamfanin na sayar da fensira fiye da 450,000 a kowanne wata a kasashe 60, abinda shi kansa Stausholm bai taba zaton haka ba.

"Akwai maganganu da ake yi da yawa game da sa rai da samun nasara idan ka na da kamfaninka," in ji Stausholm.

"Kishiyar sa rai da samun nasara bas hi ne sa rai da rashin nasara ba - sai dai fahimtar abinda za ka iya yi da wanda ba za ka iya ba."

Idan kana son karanta na Turancinsa sai ka latsa nan Positive Thinking can make you too lazy to meet your goals