Ko me ya sa mutane ke jima'i da 'yar tsana?

Baya ga saduwar jima'i, wasu mutanen na kashe 'yar tsanar
Bayanan hoto,

Fim din Westworld yana nuni da yadda masu yawon bude ido suke amfani da 'yar tsana

Wani Fim mai taken 'Westworld' wato yammacin Turai, ya nemi sani dangane da irin yadda rayuwar jima'i za ta kasance a nan gaba musamman bisa la'akari da yadda fasahar kimiyya take kara bunkasa a kullum. Hakan ne ma ya sanya Brandon Ambrosino ya rubuta wannan kasida.

Misali ace kai attajiri ne wanda zai iya kashe tsabar kudi har $40,000 domin ya ziyarci garin da babu doka da oda, rana daya. Ka ga ke nan za ka iya aikata duk irin ta'asar da kake son aikatawa.

Za ka iya yin kisan kai. Za ka iya yin fyade. Sannan za ka iya huce haushinka a kan duk mutumin da ka ga dama. Koma me ka yi a irin wannan gari, babu laifi domin babu doka da oda a cikinsa.

Saboda haka, kusan za a iya cewa mutane kalilan ne kawai za su iya sanin irin abin da ka aikata a wannan garin kuma watakila ma su nemi su karfafa maka gwiwa wajen cigaba da aikata hakan.

Da alama al'amarin ya munana ko?

To amma misali idan aka ce wannan garin da muke batu akai da kuma duk irin ta'asar da aka yi, gari ne da ya kunshi 'yar tsanar Mutum-mutumin da aka kera da halayya irin ta dan adam domin kawai ta biya maka bukata, shin ko hakan ya kai munin misalin da muka bayar na farko?

Su dai mutum-mutumi komai yawansu ba za su cutar da dan adam ba. Yanzu haka dai wannan batu ne yake cin kasuwa a fim din 'westworld'.

Shi dai wannan fim ya mayar da hankali ne a kan rayuwa a wurin shakatawa wanda ke cike da 'yar tsanar ta Mutum-mutumi, a inda mutane ko kuma masu yawon bude ido suke yin duk abin da suke so da su.

Wani kwararre mai kirkirar Mutum-mutumi da ake kira Jeffrey Wright ya ce " An kirkiri 'yar tsanar ne domin gamsar da mutanen da suka ziyarce su da kuma biya musu duk wata bukata da suke da ita."

Bayanan hoto,

Irin yadda wasu mutane kan biya makudan kudi domin kashe ko kuma saduwa da 'yar tsanar

Yin Jima'i ta Intanet

"A koyaushe mutane suna biyan kudi domin yin jima'i." In ji Maeve Millay, wata magajiyar gidan karuwai a fim din na 'westworld', yayin da take magana a kan halayyarsu ta 'yar tsana.

Ta ci gaba da cewa "banbancin kawai shi ne ana kididdige kudin da za a ba mu idan aka sadu da mu kuma a biya nan take."

Abin da Maeve take son nunawa shi ne dole ne ka biya duk wata mace da ka sadu da ita.

Ita dai Maeve, wata 'yar tsana ce wanda aka kirkire ta domin ta biya wa duk mutumin da ya ziyarci wannan wurin shakatawar bukata ta jima'i.

Tana kuma jan hankalin mutanen da su ba su da niyyar saduwa da 'yar tsana sakamakon mallakar mata a gidajensu.

Bayanan hoto,

Slavoj Žižek, wani mai sukar fina-finai ne irin su Westworld

Ko akwai Banbancin tsakanin Mace da 'yar tsanar?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Bisa tsari halittar da aka yi wa 'yar tsanar mai kama da mutum, tana da farji da ke yin duk irin abin da na 'ya mace yake yi. Suna sumbartar masu saduwa da su. Suna yin kukan dadin jima'i. Sannan kuma suna nuna gamsuwa ko rashin gamsuwa da jima'i.

To amma wasu masu sukar wannan al'amari, suna ganin fim din na 'westworld' yana kokarin bayyana cin zarafin mata ta hanyar jima'i.

Suna ganin cewa irin yadda aka ci zarafin 'yar tsanar da aka yi wa lakabi da Dolores a wasan kwaikwayon wadda kuma ta fara kokarin tuna abin da maza suka yi mata a baya, hanya ce ta cin zarafi ta hanyar jima'i.

A zahiri, duk wata 'yar tsanar da aka kirkira mai halittun mata a fim din na 'westworld', to an yi ta ne domin biyan bukatar maza.

To sai dai abin tambaya a nan shi ne shin ko ana neman amincewarsu kafin saduwa da su?

Baya ga saduwa da irin wannan 'yar tsanar, akwai abubuwa da dama da ake yi musu wadanda alal-hakika ba za a iya yi wa dan adam ba, kamar kisan su da ake yi.

Bayanan hoto,

Wata 'yar tsanar Mutum-mutumi tana shan lemo

Koma dai wace irin azabtarwa ake yi wa wadannan irin 'yar tsanar ko kuma Mutum-mutumi, a kowane dare, masu kula da wurin shakatawar suna goge komi daga kwakwalwarsu.

Ana kuma yin hakan ne bisa tunanin cewa abin da ya sanya sabawa dan adam yake da muni shi ne yadda dan adam din yake iya tuna duk abin da aka yi masa.

Babu shakka, abubuwan da wannan wasan kwaikwayon yake kokarin neman sani a kai, ba abin da za a ki mayar da hankali a kai ba ne domin ba wai kawai al'marin ya shafi duniyar kimiyyar fasaha ba ne.

Wannan ne ya sanya wata masanin halayyar dan adam, Sherry Turkle wadda ta yi bincike kan alakar dan adam da kimiyyar fasaha, fadin cewa bai kamata tunaninmu kan yadda kimiyyar fasaha za ta kasance a nan gaba ba ya takaita ga rayuwar 'yar tsananar Mutum-mutumi ba.

Ta kara a cewa kamata ya yi a mayar da hankali kan irin mutanen da za mu zama a nan gaba. Misali masu kallon fina-finan batsa ne? Ko kuma masu yawan son biya wa abokan zamansu bukatunsu na jima'i ne?

To amma Ford wani mai bincike kan abin da ya sanya mutane azabtar da Mutum-mutumi, ya yi ikrarin fahimtar dalilin da ya sa mutanen suke son kashe mukudan kudi wajen kashe da yin jima'i da 'yar tsanar, wato saboda ba mutum ba ce.

Idan kana son karanta wannan labari da harshen Turanci, sai ka latsa wannan Would sex with a robot be infidelity