Ko ka san fa'idar sanya kwalli?

Sai dai kuma kyau a wata al'adar zai iya zama muni a wata
Bayanan hoto,

Al'ummar Misra sun yi suna wajen ado da nuna kyau

Shin wai mutanen Misra na da sun kasance masu koɗa kansu ne dangane da al'adunsu ko kuma dai mu ne mu ke alakanta ta'adunmu da nasu? Alastair Sooke ya yi bincike kan amsar wannan tambaya.

Ba ya ga batun kyawu, wani baje-kolin kayan tarihi da gidauniyar Bulldog Trust ta yi, a wani katafaren gida da ke tsakiyar birnin London, bai zai zama laifi ba idan har ka yi tunanin cewa al'ummar Misra na da, sun kasance masu kambama kansu da kuma son ɗamfara al'adunsu a kan mutane.

Da dama daga cikin abubuwan da aka baje-kolinsu guda 350 wadanda kuma aka samo su daga gidan tarihin Burtaniya da ba a fiya daukar sa da mahimmanci ba, na kunshe da abubuwan da suke nuna kyawu.

Abubuwan dai sun hada da kananan matazan kai da maduban hannaye wadanda aka yi su da karfen tagulla da kuma azurfa.

Sauran abubuwan turmin dakan kwalli da sauran sinadaran yin kwalliya.

Bayanan hoto,

Madubin da aka yi da karfe tagulla

Ƙarara an nuna yadda mutanen Misra na da can, maza da mata suke iya yinsu wajen gyara kansu domin su fito tsaf-tsaf.

Akwai kuma mazuban kayan kwalliya da turare da aka kera da duwatsu masu kama da lu'ulu'u, iri daban-daban.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

An kuma baje-kolin wani gashin dan adam da ke nuna cewa mutanen kasar Misra na wancan lokacin suna yin karin gashi.

Har wa yau, akwai nau'i iri daban-daban na kayan yari da suka hada da dutsen kwalliyar mata da aka ce an hako shi daga kabarin wata yarinya.

A takaice dai za a iya cewa al'ummar kasar Misra na wancan lokacin, walau mata ko maza, suna son yin ƙawa.

To sai dai kuma kasancewar duk inda ka je za ka sami irin kayayyakin da mutanen Misra suka yi amfani da su, yana daure wa masana ilimin tarihin abubuwan da ke binne a cikin kasa suna, kai.

A hannu daya dai, tana iya yiwuwa cewa al'ummar Misra na wancan lokacin suna da matukar kaunar son yin kwalliya ta kece-raini kamar yadda mutanen yanzu suke son yi.

Watakila ma daga wurin al'ummar Misrar ne muka samu tunanin mahimmancin caɓa ado.

Amma ta wani bangaren kuma akwai matsala wajen alakanta al'adunmu na son ado da na mutanen da suka banbanta da mu. Tana iya yiwuwa cewa son ado irin na mutanen Misra ya wuce batun burgewa kawai.

Caɓa ado domin jan hankalin maza ko mata

Bayanan hoto,

Al'adar sanya kwalli na da karfi a Misra a wancan lokacin

Wannan ne irin abin da masana ilimin abubuwan da ke binne a kasa suka yi imani da shi. Misali sanya kwalli da al'ummar kasar Misra suke yi, shi ne dalilin da ya sa ake yin adon kwalli a wannan zamani.

Wani binciken kimiyya da aka yi na baya-bayan nan ya nuna cewa sinadarin kwalli yana da wasu sinadarai da ke kashe kwayoyin cuta da zarar sun hadu da danshin cikin ido.

Bugu da kari, yawan sanya kwalli a ido zai taimaka wajen rage matsalar hasken rana da ke taba idanu.

Kusan duk wani abu da mutanen na Misra ke amfani da shi yana da fa'ida. Misali kamar karin gashi da suke sanyawa, yana taimakawa wajen kariya daga kwarkwata.

Batun sanya kayan yari kuwa na da alfanu ta mahangar addini.

Bayanan hoto,

Wasu abubuwan kawa na mata kirar Misra

Dangane kuma da shasshawa ko kuma kadangaruwa, 'yan mata masu rawa da karuwai suna zanawa a cinyoyinsu domin kariya daga cututtuka masu alaka da saduwa.

" A duk lokacin da na yi kokarin fahimtar ma'anar kyau ko ƙawa ga al'ummar Misra na wancan zamani, na kan rikice." in ji Joyce Tyldesley, wata mi nazari kan kasar Misra.

Joyce ta kara da cewa "tana rikicewa ne saboda komai na 'yan kasar ta Misra yana da manufa fiye da daya. Saboda haka idan ana maganar tsohuwar Misra, to gaskiya ban sani ba ko kalmar Kyau ce ta kamata a yi amfani da ita.

Bugu da kari, hoton sarkin Misra wato Fir'auna Senwosret III.

Duk da cewa idan ya tube rigarsa, jikinsa yana kama da na masu motsa jiki da kuma na matasa, amma fuskarsa koyaushe a daure take sannan kuma ta motse sannan yana da maka-makan kunnuwa.

Ka ga wannan siffa ai ba ta kyawu ba ce ga ɗa namiji.

" Manyan kunnuwan suna nuna cewa sarkin zai saurari mutane." in ji Tyldesley.

Haka al'marin yake ga sarauniya Cleopatra da Nefertiti, a uk lokacin da ake alakanta Misra da kyawu.

Sarauniya Cleopatra tana da katon hanci sannan kuma habarta ta fito waje kuma tana da tattara a fuskarta.

Bayanan hoto,

sarauniya Cleopatra ke nan wadda 'yan kasar suke mata kallon kyau

Saboda haka irin wannan siffa ba za a kira ta kyawu ba.

Daga karshe dai za a iya cewa Kyau hana ganin laifi wato idan kana son mutum ba ka ganin muninsa.

Bayanan hoto,

Sarauniya Nefertiti

Idan kana son karanta wannan labarin na Turanci sai ka latsa nan wurin How ancient Egypt shaped our idea of beauty