Gwajin sabon maganin cutar mantuwa bai yi nasara ba

Anci buri akan gwajin sabon maganin cutar mantuwa
An kawo karshen gwajin da akeyi na wani sabon maganin cutar mantuwa wanda aka ci buri a kansa ba tare da nasara ba.
Sama da mutane dubu biyu da ke fama da cutar kamfanin hada magunguna na Amurka wato Eli Lilly ya yi gwajin da su.
Wadanda suka rinka amfani da maganin mai suna solanezumab ba su nuna wata alama ta warkewa ba.
Masu bincike sun sa kyakkyawan fata akan maganin a shekarar da ta gabata, sakamakon irin bayanan da aka gani na irin alamun tasirin sa ashekarar da ta wuce.