Ko ka san asalin karin magana?

Amma ba a iya tantance asalin
Bayanan hoto,

Kowane karin magana na da asali

Karin Magana, kalmomi ne 'yan kilalan amma masu kunshe da zunzurutun ma'ana. Ana amfani da su kuma a tsakanin kowace al'ummar duniya.

Kusan za a iya cewa babu wani abin da babu karin magana a kansa.

Karin Magana na da suna iri daban-daban da suka hada da Salon Magana da dai sauransu.

Saboda haka fassara ma'anar karin magana ba abu ne mai sauki ba.

To amma wasu na fassara ta da maganganun zamani na da, da ba a iya tantance mutumin da ya kago su ba.

Idan aka kwace aiki daga hannun dan uwanka aka damka shi a hannun abokin shugaban wurin aikin, ana iya jefa karin maganar da zai dace da wannan yanayi.

Misali "Mai uwa a gindin murhu, ba ya cin tuwonsa gaya."

Idan kuma misali danka na cikinka bai yi nasara ba a wasan kwallon kafa, za ka iya cewa "Ba kullum ake kwana a gado ba."

Misali ace abokinka ya rabu da maidakinsa kuma ya kasance a cikin zullumi, za ka iya fadin "Abu kamar Jamfa a Jos."

Ga mutumin da yake magana da harshensa, za a iya cewa babbar matsalar karin magana a gare shi, ita ce yawan yin amfani da ita a yayin zantawa.

Wata kasida da aka wallafa a mujallar "Judgement and Decision Making" ta gano alakar da ke akwai tsakanin maganganu marasa ma'ana da karancin basira.

Karin Magana a kan ayyuka

An ce akwai karin magana a kusan komai da dan adam yake yi, to amma za a iya cewa b su da yawa a irin aikace-aikacen da muke yi na yau da kullum.

Karin magana da kasuwanci ɗanjuma ne da ɗanjummai saboda wasu dalilai, in ji editan wani littafi da ake kira "Book of Quotations", Fred Shapiro.

Ya ce " A harkar kasuwanci, lokaci tamkar kudi ne, kuma haka ma 'yan kasuwa sun fi son takaice magana saboda ba su da lokaci."

Hakan ne ya sanya muke jin duk ire-iren kalmomi a kullum. Karin magana 'yan kil, kamar yadda ake rubutu a kafar sada zumunta ta Twitter a wannan zamanin, suna gamsar da jama'a wajen sadarwa.

Shapiro ya kara da yadda mutane ba sa manta karin magana.

Karin magana ba ya tsufa

Wani abin da yake ba wa mutane sha'awa shi ne yadda karin magana ba ya tsufa.

John Latham, wani mai matakin ilimin PhD, ya ce karin magana na da amfani sosai wajen isar da sako saboda" suna nuna cewa batun da ake magana akai ba sabon abu ba ne, illaiyaka dai an yi amfani da fasaha wajen isar da sakon."

Asalin karin magana

Bayanan hoto,

Gano asalin karin magana tamkar neman allura ne cikin ciyawa

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Dole ne a samu wurin da karin magana ya fara. To amma ina ke nan?

Gano daga wurin da karin magana ya fara abu ne mai matukar wahala, kamar ace ana neman allurar da ta bace ne a cikin ruwa.

Yana da matukar wuya sanin shekarar da aka fara amfani da wata karin magana.

Masu nazarin kalmomi dai suna kokarin ba wa kowace kalma lokacin da aka fara amfani da shi.

Haka zalika, ba a cika samun karin magana guda daya kacal ba da za a ce shi kadai kowa yake amfani da ita.

Kamar a harsuna da dama, za ka ga kowanne karin magana yana da launi iri daban-daban.

Misali asalin karin maganar da ke cewa "macen da ba ta da namiji tamkar kifi ne da ba shi da keke," na da rudarwa.

Duk da wasu suna danganta karin maganar da 'yar Amurkar nan mai rajin 'yancin mata, Gloria Steineman, a baya-bayan nan, Shapiro ya samo wata tsohuwar ma'ana ga wani karin magana daga shekarar 1975.

Ya gano wani karin magana wanda kalmominsa suke shige da na wannan, a inda a shekarun 1950 ake fadin "namijin da ba shi da imani tamkar kifi ne da ba shi da keke."

Har wa yau, wata waka da aka yi a 1909 ta zamo misalai har guda biyu wato "namijin da ba shi da mace kamar jirgin ruwa ne da ba ya yawo a kan ruwa" da kuma "namijin da ba shi da mace tamkar kifi ne da ba shi da jela."

Rashin tsufan karin magana

Bayanan hoto,

Masana sun ce karin magana ba ya tsufa

Rashin tsufa ko kuma ace an daina amfani da karin magana ne ya janyo mutane suka fi amfani da su fiye da kalaman mutane na cikin baka.

Duk da cewa karin magana da kalaman cikin baka suna da kamanceceniya to amma akwai banbanci tsakanin rawaito kalaman Winston Churchill da kuma nanata karin magana irin ta nahiyar Afirka.

"Yin amfani da kalaman cikin baka, alamu ne na kokarin alakanta kalaman da wanda ya yi su, a inda su kuma karin magana ake yin su da manufar zurfafawa ko kuma fadar wani abu ta hanyar fasaha kuma a takaice," In ji Shapiro.

A ayyukanmu na yau da kullum, irin wannan fasaha ta kan zo ne yayin da ake kokarin karfafawa abokan aiki ko kuma ma'aikata gwiwa.

Sai dai kuma Shapiro yana ganin cewa yawan yin amfani da karin magana ka iya haifar da tsukewar tunani ga masu yawan amfani da ita.

To amma an ce "A koyaushe ba a rasa nono a ruga."

Idan kana son karanta wannan labarin na Turanci, sai ka latsa wannan We need proverbs because they reflect what we are.