Hanyar caza sabuwar mota mai aiki da lantarki

Injin cajin mota

Asalin hoton, Other

Waɗanne abubuwa ake buƙata, kuma waɗanne ne ba a buƙata, don kula da ababen hawa masu ririta man fetur?

Akwai birane da kwalejoji da jami'o'i, da suka jajirce wajen inganta muhalli kuma suna bayar da makamashi kyauta da wajen ajiye ababen hawa ga 'yan ƙasa da suka shirya sayen abin hawan maras ƙayatarwa kuma ba ya buƙatar makamashi da yawa.

Mafi yawan lokuta irin waɗannan wuraren cajin abin hawa sai ka gan su fayau, babu motoci masu aiki da lantarki (PEVs) da ke hawa hanya, ballantana su je su cika wuri.

A yau, akwai yiwuwar samun ɗumbin direbobin da ke ta kewaye-kewaye don neman wurin tsayawa. Kuma matsalar ba wai ta ababen hawa masu aiki da lantarki da suka yi yawa ba ce.

Da zafi-zafi a kan bugi ƙarfe. Idan baturinka ya fara nuna alamar ja, wurin da ke cunkushe (da ababen hawa) zai iya janyo maka irin wannan launi.

Asalin hoton, EPA/CHEMA ANGULLO

Bayanan hoto,

Masu motocin da ke amfani da lantarki ba ruwansu da layin sayen man fetur

Tun da ana samun sabbin motoci masu cin mil 300, bai kamata ma a bari cajin batur ya yi ƙasa ba. Bisa la'akari da bunƙasar fasahar ƙere-ƙere; nauyi ne na ƙashin kai da ya kamata mutum ya ɗauka wajen shawo kan matsalar.

Mantawa da caji ya ragu zuwa kashi 20 cikin 100. Nau'o'in baturan EV suna da saurin caji da zarar sun yi ƙasa; suna saurin zuƙewa da zarar ƙarfinsu ya ragu ƙasa da rabi. Ƙasa da kashi 80 cikin 100 (na caji) na zurarewa a hankali. Da yake, za ka iya yin tafiyar mil 50 cikin nishaɗi da caji, lokacin da za ka shafe wajen ƙara caji na da cin rai.

Kada ka mamaye wurin ajiye mota na kyauta, ka kyautata musammam saboda direbobin da suka fi ka buƙatar caji.

Kada ka kankane. E, ka saba ajiye mota a nan tun lokacin da ka sayi motar Bolt? Ga Tricia daga sashen lissafin kuɗi za ta buƙaci abin cajin daga lokaci zuwa lokaci. Maimakon takaicin rasa wurin ajiye motarka da ka mamaye, za ka yi farin cikin samun sabon aboki da za ta aike maka da saƙon waya cewa, ta gama caji (kamar yadda muke sa ran ku riƙa yi).

Asalin hoton, EPA/FERNANDO ALVARADO

Bayanan hoto,

Mafi yawan kananan motocin da ake caji ba sa mamaye waje mai yawa a filin ajiye motoci

Idan ba caji za ka yi ba, kada ka ajiye (motarka). Ba ma sai an faɗa ba, jigon ajiye abin hawa dai caji ne kawai. Ajiye abin hawa haka kawai ba zai taimaki ƙasa ba, ko da yake, yana iya taimaka wa birni wajen ƙara samun kuɗin shiga.

Yi amfani da kwamfuta. Akwai ɗumbin kwamfuta da ke fito da jerin wuraren caji (na kyauta da akasinsu), waɗanda ba sai an sha wata wahala ba, wajen ƙara mai - sannan akwai ɓoyayyun tashoshin caji a cikin birni. Tashoshin cajin da ake biyan kuɗi, akwai kwamfuta dab da wurin, har ma za su sanar da kai cewa ana amfani da wurin, kuma suna iya aike maka da saƙon cewa cajin motarka ya cika taf.

Yi caji yanzu, saboda lokacin da ba ka da damar yi. Ba ka tsammanin samun wurin caji a katafaren shagon unguwa lokacin da hada-hadar ciniki ta kankama. Maimakon haka, yi tunanin zuwa wurin lokacin da babu cikowa, da maryace, kamar lokacin da kake cin abincin dare ko kallon fim.

Yi hangen gaba. Fahimci cewa fasahar ƙere-ƙere da yanayin zamantakewa na sauyawa, kuma ƙaruwar motoci masu amfani da cajin lantarki (PEVs) na nuni da samar da ƙarin wuraren caji, amma ba lallai ne su zama kyauta ba, sannan da wuya a same su a wuraren da ake yawan hada-hada.

Yi hanƙoron inganta muhalli, ta yiwu ta hanyar sayen takalmi mai daɗin sha'ani.

Asalin hoton, Yui Mok/ PA Wie

Bayanan hoto,

Ababen hawa masu cajin lantarki na taimakawa sosai wajen inganta tsaftar muhalli

Ɗauki nauyin da ya rataya da kanka. Idan ka sayi mota mai aiki da lantarki don tattalin abin hannunka. Amma waɗanda ke ra'ayin kyautata muhalli, ka iya yin caji a gareji. Kana ƙara kyautata muhalli idan ka haɗa wurin cajinka da wurin zuƙar makamashin rana.

Sayi sabuwar mota. Lokacin da ababen hawa masu sarrafa kansu za su shigo. Ta yiwu masu sauke ka a bakin ƙofar inda za ka ne, sannan su tuƙa kansu zuwa wani gefen hanya don yin caji, ko ma ta hanyar amfani da faya-fayan caji da ake kafe su a suminti, ba tare da taimakon wani mutum ba.

Da zarar haka ta auku, ba za ka damu da cewa Tricia za ta aike maka da saƙon waya ba, sai dai in kun haɗu a wajen shan shayi.

Idan kana sha'awar yin sharhi ko wani abu daban kana iya duba sama zuwa shafinmu na BBC Facebook ko ka aika da saƙo a kan Twitter.

Idan kana so, sai ka shigar da adireshinka don samun muƙalu da mujallun BBC a kowanne mako, don ka karanta abubuwa 6 a wannan mako.

Wasu labarai da aka zaɓo daga shafukan BBC kan harkokin Duniya da al'ada da Birni da Tafiye-tafiye za su shigo cikin akwatin saƙonka kowacce Juma'a.