Nau’ukan abincin ban mamaki da ke gusar da warin tafarnuwa

Tafarnuwa

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Tuffa na daya daga cikin nau'ukan abincin da ke karya lagon warin tafarnuwa

Mafi yawan masu son cin burodin tafarnuwa sun gano cewa, wani abin mamaki shi ne irin karfin tasirinta da ke dadewa ana jin warinta.

Tsawon sa'o'i 24 bayan cin abincin, warin ta zai ta fita a numfashi, har ma da gumi.

A gaskiya ma ba sai mutum ya sanya tafarnuwa a bakinsa zai yi warinta ba.

A shekarar 1936, likitoci sun ruwaito a cikin Mujallar Kungiyar Masana harkokin kula da lafiya ta Amurka (AMA), cewa, majiyacin da aka ba shi miyar da aka hadata da tafarnuwa ta mazurarin abinci, ta fito a numfashinsa sa'o'i kadan da yi masa duren.

Wani likitan ya rubuta cewa, ya gano irin wannan lamarin a lokacin da yake kula da wata uwa da ta haihu tana fitar da "wani matsanancin warin tafarnuwa mai hana sakat da ya fito daga numfashinta."

Nan take bayan haihuwarta, "Na cika da mamaki tare da murmushi saboda fahimtar cewa jaririn ma yana damfare da warin tafarnuwa a numfashinsa," kamar yadda ya rubuta.

"A irin wannan yanayi na sanar da wasu mutane, sai dai sun rika tunanin ko ina zolayarsu ne."

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Tafarnuwa na shiga magudanan jini - don haka ake dadewa ana jin tasirinta a jiki

Dalilin da ya sa warin tafarnuwa ke damfaruwa ga mutanen ma da ba su ci abin da kansu ba, kamar jarirai da marasa lafiyar da ake ba su abinci ta mazurarin ciyarwa, shi ne tafarnuwa na damfare da hadaddun sinadaran sulphur, wadanda ke kwarara a magudanan jini bayan sun narke.

Da jini ya zuka, sai su gangara cikin huhu zuwa makoshi su fito ta baki. Babu irin goge hakoran da za ka yi ya kawar da shi - warin ba yana fitowa ba ne daga tafarnuwar da ta makale a baki, sai dai kawai lamarin yana aukuwa daga juyin sarrafa sinadaran jikinka.

Kawar da sinadarai, ita ce managarciyar hanyar shawo kan lamarin.

Wasu shekaru da suka wuce, Sheryl Barringer, wata kwararriya a fannin kimiyya da ke Jami'ar Jihar Ohio, wadda ta gudanar da nazari (bincike) a kan yadda tartsatsi (ruguntsimin) sinadarai ke haifar da kamshi (ko wari), ta samu dalibin da ya bukaci ta gudanar da aikin bincike kan yadda tafarnuwa ke damfaruwa a numfashi.

Akwai wasu nau'ukan bincike da aka gudanar kan nau'ukan abinci, wadanda suka hada da latas da sinadarin hada gahawa (shayin kofi) da koren ganyen salare (celery) da dankali da koren ganyen parsley da minti da nanar shayi (na'a-na'a) da ganyen basil da hular barawo.

Sabanin dalilin da ake zata Barringer da dalibai masu yawa sun bibiyi kadin yadda wasu nau'ukan abinci za su iya gusar da warin tafarnuwa, tare da hakikanin yadda suka yi abin.

Idan aka ci wasu nau'ukan abinci tare da tafarnuwa za su kawar da tasirin warin.

Latas da minti da kuma wani abin mamakin shi ne tuffa su ne aka fuskanta.

"Tuffa na daga cikin wadanda aka gano kwatsam," a cewar Barrringer.

Wani dalibi da ya ci tafarnuwa, ya dan kurbi ruwa, a matsayin gwaji, sai aka samu sakamako mai ban mamaki, inda aka samu karancin burbushin warin.

Da aka bibiya daukacin abubuwan da aka ci a wannan rana, dalibin ya tuna cewa ya ci tuffa sa'o'i kadan da suka wuce bayan an ci tafarnuwa, sai warin ya gushe.

Takardar gungun masu binciken ta fito ne a Satumbar bara, inda ta bibiyi nau'ukan sinadaran kawar da wari, inda aka kyautata zaton cewa an yi taho mu gama a rugugin sinadaran sulphur hudu da ke damfare da tarfarnuwa tare da sauran rukunin sinadaran da ake wa lakabi da phenolics.

Wadanda suka sanya kansu shiga wannan gwaji sun ci tafarnuwa tare sauran kayan makwalashe (tande-tande da lashe-lashe), sannan suka yi numfashi a cikin abin gwaji na 'spectrometer, wadda ta fito da sinadaran daga cikin numfashinsu.

Masu binciken sun cakuda nikakkiyar tafarnuwa da ruwa da sauran nau'ukan sinadaran phenolics, wadanda suka hada da sindarin "rosmarinic acid," wanda ake samu a cikin minti, sannan aka shake su daga cikin mazubin abin awo na spectrometer.

Nan take aka samu tabbacin cewa gundarin tuffa da latas da minti su suka fi karfin tasirin da wadanda aka dafa su.

Wannan ya yi nuni da sinadaran narkar da abinci, wadanda ke taimakawa a yamutsin sinadarai, amma karfinsu kan ragu idan yanayin zafinsu ya karu, ta yiwu an yi amfani da su.

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Tuffa na daya daga cikin nau'ukan abincin da ke karya lagon warin tafarnuwa

Daukacin abubuwan da aka zabo, minti ya fi karfin tasiri, a cewar Barringer.

Minti na da dimbin sinadaran phenolics da aka fara da shi. A wajen masanin kimiyyar sinadarai, abu mafi sauki a bibiyi sinadarin Rosmarinic acid da sinadaran sulphur da ke damfare a cikin tarfarnuwa, ta yadda za a iya ganowa karara cewa idan aka gutsuro nan da can aka hada za a samu sinadaran da ba su da wari.

Tuffa na da karancin sinadaran phenolics, koda yake yana matukar taimakawa.

Amma latas shi ne mafi karancin kowane sinadari da aka yi gwaji a kansa.

In da ya yi kasa da abin da ake samu a cikin koren ganyen shayi, wanda bashi da karfin gusar da wari ko kadan.

"A nan ne zan iya cewa ba mu gama fahimtar abin da ke faruwa ba," a cewar Barringer.

Kyakkyawan sinadarin narkar da abinci (enzymes) ba ya aiki a kashin kansa wajen kawar da sinadaran sulphur, kamar yadda gungun masu binciken suka gano.

Amma hadin karfin sinadaran phenolics da masu narkar da abinci (enzymes) ta yiwu suna da tasirin boye a kan latas.

Ta hanyar amfani da wannan ruguntsimin sinadaran wadda ba a gama fahimtarta ba, za ka iya kawar da warin tafarnuwa.

Matukar dai ba mu manta ba babu wata dabarar fesa kamshi da za ta sauya yanayin mutane, wadanda tamkar masana'anta ce da ke fitar rugugin sinadarai daga numfashi. Abubuwan da muke fitarwa ko gumi ba abin da muka ci jiya kawai zai bayyana ba, har ma da kwayoyin bacteriya (wadanda ba a ganinsu sai da madubin likita) da suka tare a bakunanmu, kai har ma idan muna dauke da wasu cututtuka.

Masana kimiyya na duba yiwuwar yadda za a yi amfani da sinadaran da ke damfare a iskar da muka fitar za ta yi amfani wajen gano cutar dajin huhu, ko ta hanyar amfani da na'urar lantarki ta zuko jini da fitsari ko samfurin kwayoyin halittar jiki da za su iya nuna alamun cutar dajin mahaifa zuwa lalacewar kwakwalwa.

Baya ga kawar da mummunan wari abu ne mai kyau, to yana da matukar kyau mu yi tunanin cewa akwai wani abu mai matukar muhimmanci, baya ga cewa akwai al'amuran da ke dukunkune a cikinsa.