Ko kun san cewa kaji na da matukar dabara?

Kaza

Asalin hoton, Credit: Klein & Hubert/naturepl.com

Bayanan hoto,

Wane irin wayau na tsawon lokaci a ke dauka don tsattsagar kwayar hatsi

Tsuntsun da ya fi kowane shahara a duniya na da wayau, har ma ta yiwu yana da matukar damuwa game da walwalar 'yan uwansa - al'amarin da kan bijiro da tambayoyi masu tayar da zaune tsaye a harkar noma.

Akwai wani abu mai rikitarwa game da kaji.

A fadin duniya yawansu ya kai biliyan 19, al'amarin da ya mayar da su daya daga cikin nau'ukan halittu masu kasusuwa a fadin duniya.

Sai dai mutane da dama ba su cika hulda da tsuntsayen ba, musamman a lokacin da suke raye.

Kaji na da karsashi, inda suke nuna sanin abin da suke ciki, har ma su juya akalar junansu.

Wannan lamari ya haifar da ce-ce ku-ce mara kan gado game da kaji.

Kamar yadda yake kunshe a wasu nau'ukan bincike, mutane na fafutikar daukarsu ne tamkar kowane irin tsuntsu.

A gaskiya ma su wakilai ne na tsuntsayen gida masu nauyin jiki (ba kasafai suke yin nisa ba), wadanda suka hada da talo-talo da kurciya da dawisun Asiya.

Wannan kuma sanannen abu ne a wajen mutane da suke ganin kaji ba su da basira ba su ma da wasu "cukurdaddun al'amura na dabi'u" manya da ke bukatar zurfin tunani kamar na sauran dabbobi irin su birai da gwaggon biri.

Wannan ita ce fahimtar da wasu suka tabbatar da ita wajen kwatanta kaji a sananniyar al'ada, al'amarin da ke bai wa mutane kwanciyar hankali wajen cin kwayaye ko naman kaza da aka samar ta hanyar kiwatawa.

Amma kaji wasu ire-ire ne daban, sabanin yadda ake dauka suna yin dukum.

Asalin hoton, Entertainment Pictures / Alamy Stock Photo

Bayanan hoto,

Zakaran Heihei da ya fito daga Moana tabas mashiriricin gaske ne.

Sukan iya kididddige ala'amura, su nuna sanin abin da suke ciki, har ma su yi tasirin juya akalar junansu wajen tallafar juna kwatancin salon mulkin 'Machiavelli' (wani littafi da ya shahara a wajen masu nazarin salon mulkin al'umma).

A gaskiya ma, kaji na da matukar wayau, ta yadda takaitacciyar hulda da wadannan tsuntsaye na iya kawar da gurguwar fahimtar da aka dade da yi musu.

Ban taba tunanin cewa kaji na da cikakken wayau ba tare da saurin fahimta sai daga bisani.

A wani bincike da aka wallafa a shekarar 2015, Lisel O'Dwyer da Susan Hazel sun gabatar da darussa ga dalibai masu neman digirin farko a Jami'ar Adelaide ta Autiraliya.

A matsayin hanyar fahimtar fannin alkiblar tunanin da cikakkiyar fahimta, an sanya dalibai gwaje-gwajen da suka hada da bai wa kaji horo.

Kafin a fara karatu a ajin, daliban sun cika wasu takardun neman bayanai.

Mafi yawansu sun ce ba su cika zama tare da kaji ba.

Suna yi musu kallon halittu masu saukin lamari, kuma babu yadda za a yi su nuna gajiya da takaici ko farin ciki.

Bayan shafe sa'o'i biyu ana horar da kajin, daliban sun samu cikakkiyar gamsuwa cewa kaji na damfare da jin wadannan al'amura uku a zuciyarsu (gajiya da takaici da farin ciki).

"Kaji na da matukar wayau fiye da yadda ake kallon su a da," kamar yadda wani dalibi ya yi sharhi a takardun bayanan da suka biyo baya.

Wani kuwa cewa ya yi: "Ban taba tunanin cewa kaji na da cikakken wayau ba tare da saurin fahimta sai daga bisani."

Asalin hoton, Credit: Tony Heald/naturepl.com

Bayanan hoto,

Wani nau'in zakara (Gallus gallus) da aka fi samu a Kudu maso gabashin Asiya.

Kamar yadda yake kunshe a wani bincicke da ba a wallafa ba, ODwyer ya sake maimaita kwatankwacin irin wannan binciken tare da ma'aikata a gonar kiwon kaji, ya kuma samu sakamako iri guda.

"Tabbas mun samu rukuni biyu mabambanta, mun same su da al'adu iri daya, da kuma sauyin dabi'a iri guda," inji ta.

Masu bincike sun yi nuni da cewa kaji na iya yin kirga, su kuma yi ayyukan lissafi da suka hada da Tarawa da debewa da sau darbawa

Yanzu ta shirya gudanar da bincike kan tasirin cin abin cin kaji da mutane ke yi, alal misali, ko mutane sun fi cin kajin da suka kiwata da jin cewa sun fi karbuwa da kwanciyar hankali.

Nazarin O'Dwyer daya ne kawai daga jerin wadanda Lori Marino ya dauko daga cibiyar kula da dabobi ta Kimmela da Kanab, a Utah, don sake bibiyar basirar kaji da aka wallafa a shekarar 2017.

"Wannan makala aikin hadin gwiwa ne tsakanin gonar Santuary da Cibiyar Kimmela, wanda aka yi wa lakabin "Aikin wani," a cewar Marino.

Manufar aikin ita ce fadakar da al'umma game da kajin da ake kiwonsu gwargwadon bayanan binciken kimiyya da aka tattara.

Marino ya ce binciken kimiyya ya bayyana karara cewa kaji na da wayau da dabara fiye da yadda mutane da dama ke tsammani.

Asalin hoton, Ernie Janes

Bayanan hoto,

Sababbin kyankyasa 'yan tsaki na da matukar wayau

Alal misali akwai makalun da aka wallafa shekaru 10 da suka gabata na Rosa Rugan ta Jami'ar Padova da ke Italiya, tare da abokamn aikinta.

Wajen bin kadin rayuwar 'yan tsakin da aka kyankyashe, masu binciken sun yi nuni da cewa kaji na iya yin kirge, su kuma gudanar da ayyukan lissafi

Ta yiwu kaji na iya aiwatar da aikace-aikacen da suka hada da "zurfafa tunani."

An samar da 'yan tsakin ne ta hanyar kyankyasa da abubuwa biyar - mazuban roba daga na'urar kyankyasar kwayaye.

Bayan kwanaki kadan, sai masana kimiyya suka dauko wadannan abubuwa biyar, inda suka yi nazarin 'yan tsakin, suka boye uku a bayan mahanga ta farko, suka saka na biyu a wata mahangar.

Akwai yiwuwar wadan an tsaki su tunkari mahangar karara fiye da sauran abubuwan.

Sake bibiyar gwajin kaifin tunanmi da iya Tarawa da debewar 'yan tsaki.

Bayan da aka boye kaya a bayan shinge, masana kimiyya sun fara mayar da kayan tsakanin mahangai biyu, injin da 'yan tsaki za su iya gani.

Sai ''yan tsaki suka nuna basirar bibiyar yawan kayan da ke bayan manhanga, kuma akwai yiwuwar su tunkari mahangar da aka boye mafi yawan kayan .

Kaji na da basirar fahimtar kidayar lissafi tun sa'adda suka dan tasa, kodayake takaitacciya ce, a cewar Rugani.

Asalin hoton, Credit: Pete Cairns/naturepl.com

Bayanan hoto,

Kaza na da kwakwalwa mai kaifin tunani

Tana jin cewa, ta yiwu a ce kaifin tunaninta ya fi na sauran dabbobi daukacinsu, maimaikon a ce kaji kawai.

"Irin wannan basirar tana taimaka wa dabbbobi a muhallinsu, misali kan yadda za su kai ga samun dimbin abinci, ko gungun ''yan uwansu da za su yi huldar zamantakewa tare, " inji ta.

Idan zakara ya samu abinci mai dadin dandano, ya yi ta kokarin burge kaji ta hanyar taka rawa.

Kaji na da kokarin "zurfafa tunani" - wato, su yi kintacen abin da zai auku nan gaba - ta yadda za su samu tara dimbin abinci, kamar yadda bayanin ke kunshe a wani nazari da aka gudanar a shekarar 2005 karkarshin jagorancin Siobhan Abeyesinghe, wanda a lokacin yake tare da Jami'ar Bristol ta Birtaniya.

Abeyesinghe ya bai wa kaji zabin tsattsaga kwaya guda, wanda zai ba su damar samun abinci bayan an samu tsaiko sau biyu, ko tsattsaga kwaya ta biyu, wanda zai samar musu da abinci na dogon lokaci bayan an samu tsaiko sau shida.

Akwai tabbacin cewa wadannan tsuntsaye za su kara tsattsaga a karo na biyu, al'amarin da zai basu dammar samun abinci a lokacin da aka samu tsaiko na tsawon lokaci.

A wata fahimtar, a iya cewa sun iya shawo kan matsala - wata dabi'a da masana kimiyyar halittu ke ganin haske ne da ke nuni da fahimtar halin da suke ciki.

Kuma kaji na da rudarwa a halin zamantakewa.

Asalin hoton, Ernie Janes

Bayanan hoto,

Kaji na da wuyar sha'ani a harkokin zamantakewar rayuwa

Wasu nau'ukan nazari da aka gudanar sun yi nuni da cewa, tsuntsayen sun gamsu da yadda ya zame wa duniya dole ta tarairayi 'yan uwansu, kuma za su iya yin amfani.

Kaji mata su kan yi saurin gano manufar zakaru da ke yin irin wannan yaudarar akai.

Idan zakara yana neman abinci sai ya samu mai dadin dandano.

Yakan yi ta kokarin jan hankalin kaji, ta hanyar rawa tare da yi musu inkiya su zo ga abinci.

Ko da yake wasu kananan zakarun sukan yi irin wannan waka da rawa tare da kasadar akwai yiwuwar manyan zakaru su kai musu hari.

Saboda haka idan karfafan zakaran da ke kusa, sai karamin zakara ya yi rawarsa a kubu, ta yadda zai ja hankalin kaji ba tare da ankarar da kakkarfan zakara ba.

Sai dai kuma wasu daga cikin zakarun ta yiwu su yaudari kaji ta hanyar inkiyar kiransu zuwa ga abinci, har ma a lokacin da ba su samu komai ba.

Lamarin babu mamaki ganin cewa kaji na da wayon gano cewa rawar da zakarun ke takawa ta yaudara ce kai da kai.

Akwai wasu alamu da kaji ke yi, wadanda ke nuna cewa suna tausaya wa juna.

Asalin hoton, Klein & Hubert/naturepl.com

Bayanan hoto,

Kaji na iya aikewa da sakonni

A jerin nau'ukan nazrin bincike da aka dauki shekara shida ana yi.

Joanne Edgar na Jami'ar Bristol da ke Birtaniya da abokan aikinta sun yi nazari kan yadda kaji ke daukar mataki da zarar sun ga iska na kada wa 'yan tsaki daga abin da kajin suka koya daga gogewarsu ta rayuwa, cewa wannan matsala ce kankanuwa.

Kaji na iya daukar mataki saboda fahimtar da suke da ita game da abin da ka iya takura wa dan tsako.

Duk lokacin da 'yan tsaki suke numfashi da kyar, sai zuciyar kaji ta fara bugawa, inda za su yi ta kiran 'yan tsakin akai, akai.

Sai dai ba sa aikata hakan idan iska na kadawa kusa da 'yan tsakin ta yadda ba za su dame su ba.

A wani bincike da aka wallafa a shekarar 2003, kaji sun saba da cakuduwa da junansu a akurki mai launi, inda iska mai takurawa ke kadawa, sai kuma akurki mai launi na biyu, wanda isaka ba ta kadawa.

Sai kajin su nuna alamun damuwarsu ga halin da 'yan tsaki ke ciki a wani akurki "mai hadari," koda tsakin babu iskar da ta far musu, kuma ba su ma da masaniyar cewa akwai hadari tattare da su.

Wannan na nuni da cewa kaji na da fahimtar mayar da martani ga abin da ke takura wa dan tsako, sabanin daukar mataki kan alamun damuwar masu tasawa.

Asalin hoton, Ernie Janes

Bayanan hoto,

Ana kiwon kaji a kasashe da dama

Ana dai ci gaba da bincike a cewar Edgar.

"Har yanzu ba mu tantance ba, kan ko cewa kaduwa da dabi'ar da kaji ke nunawa idan suka hango tsaki ko suna nuni ne ga damuwa, ko kawai wani jan hankali ne."

Da zarar 'yan tsaki sun suke, sai kaji zuciyarsu ta fara bugawa, inda suke kira a kai, akai ga tsakin, al'amarin da ke tayar da hankali sosai kan yadda ake kiwon kajin.

"Akwai yanayi da dama inda ake baje dabbobin gona a fili da ware wasunsu daidaiku, al'amarin da ke haifar musu da jin zafin ciwo da damuwa," a cewar Edgar.

"Yana da matukar alfanu a tantance ko suna samun cikakkiyar kulawa da za su rage matsalolin a irin wadannan lokutan."

Marino na jin cewa ta yiwu wannan lokacin da za a tattauna kan wadannan tambayoyin.

"Abin da aka fahimta game da kaji (ba su san halin da suke ciki ba, kuma ba su da wayau) lamarin ya auku ne saboda karsashin da aka samu na yin watsi da basirarsu da sanin yanayin da suke ciki saboda kawai mutane su ci namansu.

Gaskiyar da ba a cika gamsuwa da ita ba, game da kaji, ita ce suna da kaifin basira fiye da yadda mutane suke zato.

Sai dai, saura ya rage ga masu sayen nama idan suka samu fahimta ko za su sauya dabi'arsu wajen sayen naman.