Ka san yadda za ka iya layar-zana?

Gyalen layar zana

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Gyalen bad da kama

Masu zayyanar tufafi sun fara kirkiro sabbin hanyoyin da mutum zai kauce wa yadda za a iya ganinsa, abin da ya hada da zane-zane a tufafi ta yadda za ka iya yi wa hatta na'urori ko manhajojin gane fuskar mutum bad da bami, su kasa gane ka.

Bel Jacobs ya yi mana nazari.

Ka dauka cewa yau ga shi kana rayuwa a wani lokaci da komai ya baci, inda ake aikata abubuwa na rashin gaskiya da makamantansu. Ga na'urorin daukar hoto na tsaro a ko'ina a tituna, suna daukar hotunan mutanen da ke kai-kamo, amma kuma kai kana sanye da wani hirami ko mayafi da ka yafa a fuskarka, wanda yake da zane na musamman da aka tsara domin batar da kama, ta yadda wannan zane-zane zai susuntar da hatta na'urar daukar hoton tsaro a wuraren. Wannan salo na zane-zane na mayafin yakan batar da kamannin ido ko hanci ko bakin mutum, wanda ta hakan ta yi bad da kama, ka sirrinta kanka tare da samar da kariya.

A watan Janairu na wannan shekara ta 2017 ne mai zayyana Adam Harvey, da ke birnin Berlin na Jamus tare da hadin guiwar dakin bincike na kimiyya na Hyphen-Labs da wasu kwararrun mata masu zayyana ko zane-zanen gyale da mayafi ko gyale suka hadu inda suka kaddamar da irin wadannan kaya masu dauke da fasahar batar da kama.

Harvey ya kirikiro zayyan da tsare-tsare da ado ko shafe-shafen fuska da gyaran gashi masu susuntar da manhajojin gane fuskar mutum, da kuma tufafi ko kayan sawa da ba sa daukar zafi, wadanda kananan jirage marassa matuka, na leken asiri ba sa iya ganowa.

Asalin hoton, Adam Harvey

Bayanan hoto,

Fasahar HyperFace, wadda ke sauya fuska ko ido ko hancin mutum a kasa gane shi

Ita wannan fasaha ta zayyana tana susuntar da kwamfuta ne, inda take gabatar mata da fuskokin mutum kusan 1,200 - Harvey ya samu wannan fasaha ne daga irin halitta ko baiwar da wasu dabbobi ko halittu suke da ita ne ta sauya kama ko rikidewa domin boye kansu idan suna fuskantar wani hadari ko barazana.

Daya daga cikin ma'aikatan dakin binciken kimiyya na Hyphen-Labs, da suke aikin fasahar, Ashley Baccus-Clark, ya ce yanayin yadda siyasa take a yanzu, ya tilasta su masu zayyana da masu bincike da kuma masu kirkire-kirkire su gano wasu hanyoyin sanya ido ko tsaro.

Kuma hakan yana da danganataka ne da yadda al'amura ke kasancewa a 'yan watannin da suka gabata, game da tsaro da sirri da kuma fita a bainar jama'a, musamman a kan mata bakaken fata da kuma al'ummomi bakaken fata.

Zaben Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya masu kirkira na bangaren masu sassaucin ra'ayi bullo da hanyoyi da tsare-tsare na batar da kama ga jama'a.

Duk da cewa akwai fitattun mutane irin su Kim Kardashian wadanda suka yi fice a duniya ta hanyar sana'ar da ta shafi bayyana kansu ga jama'a, da yawanmu, mun fi kaunar sakaya kanmu daga idon jama'a.

Kuma duk da cewa intanet na dauke da hanyoyi da dama na samar da tsaro, masu zayyanar tufafi da sauran abubuwan amfanin jama'a na bullo da wasu hanyoyi na kare siffa ko jikin mutum, wadanda hanyoyi ne da suka kunshi ado da fasaha, wanda hakan ke nuna mana irin yanayin duniyar da muke ciki a yau.

Asalin hoton, Project KOVR

Bayanan hoto,

Rigar da ke kare sirrin mutum yadda za a kasa gane shi

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tsaro na daga cikin abubuwan da aka ba wa muhimmanci a fannin watsa labarai tun tsakiyar shekarar 2013, lokacin da jami'in Hukumar Tsaro ta Amurka Edward Snowden ya yi tonon silili kan yadda hukumar tsaron ta Amurka take tattara bayanai cikin sirri a kan jama'a.

Tun daga wannan lokacin aka samu bayanai kan yadda Facebook da Google da kuma Microsoft suka rika mika wa hukumar tsaron ta Amurka bayanan sirri na mutanen da ke amfani da shafukansu.

Daya daga cikin manyan kamfanonin duniya da ke kera layukan wayar salula Gemalto, shi ma ya ce ya yi amanna hukumomin tsaro na Amurka da Birtaniya sun rika satar shiga taskarsa.

Wannan ne ya sa kwararru da dama da suka hada da kamfanoni irin su Project KOVR na Holland suka karkata wajen nemo hanyoyin da jama'a za su rika amfani da su a kullum wajen kare bayanansu, ko kuma su rika tafi-da-gidanka da bayanasu, ta yadda za su tabbatar da tsaronsu.

Damar da muke da ita, a matsayinmu na mutane, ta yadda za mu bayyana wani bayani a kanmu da kuma zabar lokacin bai kamata mu yi hakan ba, na daya daga cikin abubuwan da suka sa muka tabbata mutane, kamar yadda mai zayyana Leon Baauw, wanda na daya daga cikin wadanda suka kirkiro shirin KOVR tare da Marcha Schagen.

Ya ce bincikensu ya ta'allaka ne a kan maganar cewa, ''menene tasirin kasancewar mutum a bayyane a ko da yaushe?' Ta yaya za mu sauya yadda muke tafiyar da al'amuranmu ko dabi'armu?''

Asalin hoton, Project KOVR

Bayanan hoto,

Rigar da ke kare sirrin bayanan katin mutum na banki da katin-sheda

Baauw ya ce; ''yuwuwar amfani da tufafi wajen tabbatar da tsaro maimakon ado da kariya kadai ga mutum na kara tabbata. Ya kara da cewa abu ne sananne tufafi a ko da yaushe tufafi suna ba mu kariya daga illa ko barazanar muhalli, to amma me zai hana su ba mu kariya kuma wadda ta shafi bayanai?''

Daga irin wadannan kayayyaki na zamani abubuwa ne da suka shafi ado da kuma al'ada, wadanda ke zaman hanyoyin tabbatar da tsaro da sirrin jama'a da ake neman gani zamani ya zo da su.

Kowanne daga cikin irin wadannan kayayyaki na Fabrica, yakan ja hankalin wanda ya sa shi, ta wata siga, abin da ke shafar aikin kwakwalwa ko ya kan sauya aikin kwakwalwar. Saboda haka idan har nazarin hoton aikin kwakwalwa zai kasance gaskiya, hakan zai samar da hanyar da za a iya nazari ko sanin tunaninka.

Daga cikin irin wadannan abubuwa da aka yi na gwaji, har da malafa wadda ke mika sako ta hanyar kokon kan wanda ya sanya ta, da kwalar riga da ke sadarwa tsakaninta da mutumin da ya sanya rigar ta hanyar wani dan motsi na lantarki, da kuma fuskar batar da kama, wadda ke daukar hankalin wanda ya sanya ta da wani dan hasken fitila da ke haskawa ya dauke lokaci zuwa lokaci.

Asalin hoton, Fabrica

Bayanan hoto,

Daya daga irin kayan ado da batar da kamannin mutum, da kuma hana satar tunanin mutum da za a iya yi nan gaba

Tunanin kirkiro wadannan abubuwa na tsaro da kare sirri har yanzu na zaman kamar wani abu na mafarki ko wanda ba zai yuwu ba a zahiri, amma tsare-tsaren wadanda Fabrica da Harvey da kuma ayyukan Project KOVR, na nuna muhimmanci da damuwar da masu zayyana ke da ita kan yadda abubuwa za su iya kasancewa a nan gaba.

Misali shi ne, Harvey, ya nuna cewa fasahar HyperFace, wadda ake sanya wa a fuska, wata alama ce ta yadda za a kai ga yi wa kwamfutar da ke gane fuskar mutum, layar zana.

Editan shafin fasahar tufafi na FashNerd Mano ten Napel ya ce; ''Idan ana maganar sabbin fasahohi, wasu mutanen suna ganin yawancin kamfanoni ba sa daukar matakan bayar da kariya da sirrinta bayanan jama'a, wanda hakan ne ya sa muke bukatar ganin an samu yanayi na bayar da kariya garemu, wanda hakan a takaiceyake nufin ya kamata a ga hakan a tufafi ko kayan da muke sanya wa a jikinmu.

Abu ne mai sauki a yi tsinkaye ko tunanin yadda a nan gaba mu'amullarmu da intanet ba za ta zama tamkar wata hanya ta bayyana sirrinmu ba.