Za ka iya rayuwa da abinci daya kawai?

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Kayan abinci daban-daban

A ko da yaushe ana gaya mana muhimmancin cin abinci mai gina jiki (wanda ya kunshi sinadarai daban-daban). To amma ya za ka yi idan ka samu kanka a yanayin da abinci iri daya kawai kake iya samu - Me za ka yi da zai sa ka dade a duniya.

Veronique Greenwood ta yi mana nazari.

Mutum ba zai iya rayuwa ba da biredi kadai, domin idan ya kasance biredi kawai yake ci, yayin da ya kai kusa da wata daya sama da haka a wannan hali, zai fara samun larurar ciwon gabbai da yankwanewa.

Abinci mai kyau yana dauke da sinadaran da jiki ke bukata daban-daban kuma wadatattu. Hatta nau'in abinci na musammn da masu bukatar rage kiba suke ci, wanda ake cire wasu sinadaran a cikinsa, yana dauke da wadatattun sinadaran da jiki ke bukata.

Duk da haka, idan abu ya yi kamari, mutum ya samu kansa a yanayin da abinci daya kawai yake iya samu, to za a iya cewa wani abin cin ya fi wani nau'in kayan gina jiki?

Misali, za ka iya samun dukkanin sinadaran da jikinka ke bukata daga dankali ko ayaba ko wani abu daya?

Idan za a yi wannan misali ko gwaji na rayuwa da cin abu daya kawai, ba za a yi maganar nama ko yawanci 'ya'yn itace ko kayan lambu ba, domin nama ba shi da muhimman sinadaran gina jiki irin su bitamin (vitamin), yayin da su kuma 'yayan itace da kayan lambu, ba su da isasshen sinadarin maiko (fat) da kuma mai gina jiki (protein), ko da kuwa ka ci su ne da yawa, ba za ka samu isassun wadannan sinadarai ba.

Jiki ba ya bukatar wadannan sinadarai masu yawa kamar yadda kai kake tsammani, kafin ya zauna lafiya , ko ya ra yu, amma kuma kana zubr da su a rashin sanin muhimmancinsu.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption An gano cewa dankalin-turawa yana da sinadarin furotin da bitamin da yawa

Mai bincike a kan yankin Tekun Akatik (arctic), Vilhjalmur Stefansson, ya yi rubutu a kan wani rashin lafiya da mutanen yankin arewacin Canada suke fama da shi (rabbit starvation), inda mutanen da ke cin 'yan kananan dabbobi kawai, kamar zomo, suke kamuwa da wata cuta kamar ta tamowa ko yunwa, wadda almunta sun hada da zawayi da ciwon kai da rashin katabus da mutum ke samun kansa cikin kusan mako daya.

Domin kare mutumin da ya kamu da wannan cuta daga mutuwa a sakamakonta, dole ne maras lafiyar ya rika cin abin cin da ke dauke da sinadarin da ke samar da maiko ga jiki (fat), in ji Stefansson, kamar yadda ya rubuta.

Masana na ganin idan mutum ya dogara ga nau'in sinadarin abinci daya kamar na protein, wajen sama wa jikinsa karfi ko makamashin da yake bukata, ya yi watsi ko ya bar kayan abincin da ke da sinadarin maiko(fat) ko masu ba wa jiki karfi carbohydrates, wannan zai iya sa hanta ta kai ga ta rasa karfin sarrafa sinadarin na protein.

Idan kuma ya kasance mutum ya rasa nama da yawancin kayan lambu a abincinsa, to abin mamaki zai iya amfani da dankali in ji masaniya kan abinci Jennie Jackson, ta Jami'ar Glasgow Caledonian.

A shekarar da ta wuce ne ta yi rubutu a kan Andrew Taylor, wani dan Australia da ya yi shekara daya ba shi da wani abinci in ban da dankali, domin ya rage kiba da inganta lafiyarsa.

Abin da ya sa dankali ya zama daban a tsakanin sauran kayan abinci shi ne, duk da cewa abin ci ne mai bayar da karfi ga jiki, mai dauke da sinadarin sitaci (starch), yana da sinadarin protein mai yawan gaske, wanda hakan ya sa yake da wasu sinadaran masu matukar muhimmanci ga jiki, in ji Jackson, wanda hakan ya sa Jackson ya iya yin shekarar cur da cinsa kadai ba tare da ya gamu da wata matsala ba, ko da yake yakan hada da dankalin da muka fi sani da dankalin-hausa (sweet potatoes).

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Fiya yana da sinadarai da yawa, amma bai kai na dankalin-turawa ba

Bayan tasiri ko maganar muhimmancinsa ga gina jiki, akwai kuma wasu matsalolin da za su iya tasowa ko za su hana dogaro g abinci daya kawai a rayuwar mutum, domin shi jikin dan adam yana da tsari ne da ba a yi shi domin haka ba.

Idan aka ce ka saba bada cin abinci daya ko a kwana a tashi za a kai ga yanayin da zai gundire ka, za ka kasa cinsa in ji Jackson, wanda hakan zai kai ga yanayin da za ka kasa cin abincin.

Haka kuma maganako dabarar cewa mutum zai iya rayuwa da abinci daya muddin dai, yana dauke da kusan dukkanin sauran sinadaran da jiki ke bukata, ba tare da ya gamu da wata larura ba, ita ma ba ta tabbata ba.

Domin masu bincike a farkon karni na 20, sun gudanar da gwaji a kan wasu beraye, inda suka rika basu abincin da ba ya dauke da wasu sinadarai, domin su ga ko berayen za su kamu da wani rashin lafiya ko ma za su mutu.

Ta wannan hanya ne muka ma gano wasu sinadaran, wadanda a da ba mu ma san da su ba. Sannan wannan zai nuna maka abin da bera ba zai iya rayuwa ba tare da shi ba, akalla na wani gajeren lokaci.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Naman zomo ba shi da maiko sosai, wanda hakan ya sa yake sa matsalar rudewar ciki

Sai dai zai iya kasancewa ba za a iya ganin wasu daga cikin alfanun cin abinci mai dauke da sinadarai daban-daban ba, (wanda ake gani a tsawon lokaci), a irin wannan gwaji in ji Jackson ba (domin ko shakka babu mutane ba beraye ba ne). Bayanai sun tabbatar cewa abincin da aka sanya wa kayan lambu da yawa ya fi wanda aka sanya wa kadan amfani, amma kuma ba a san dalilin hakan ba.

Watakila abincin da ba ya dauke da kayan lambu irin su alayyahu da sauran ganyaiyaki zai iya sa mutum ya gamu da hadarin kamuwa da ciwon daji, amma kuma Jackson ta ce, ''ba mu san abincin da za mu iya cewa shi ne ke haddasawa ko haifar da wannan ko waccan matsala ba.''

''Saboda haka idan za ka iya gano illa ko sinadarin da za ka rasa idan ba ka ci wani abin ci ba, ba lalle ba ne kuma ka san abin da za ka rasa daga garesu ba.'' In ji masaniyar.

Duk da cewa cin abinci daya a kullum zai iya sa ka daina bata lokacinka da kuma rage maka kai kawo wajen neman kayan abinci, to amma kuma fa wata hanya ce ta saurin kamuwa da wata cuta da kuma gajiya da abinci daya.