Cin barkono yana da amfani ko illa?

Tsananin zafin barkono Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Barkono yana da zafi kamar na wuta

Da yawa daga cikinmu muna da sha'awar cin yaji ko barkono a abincinmu duk da tsananin zafinsa, kamar na wuta. To amma cinsa yana da wani amfani ko illa ga lafiyarmu?

Yadda za ka ga wasu mutane suna cin abinci ko wani kayan kwalan da makulashe mai yaji har ka ga suna face hanci da kwankwadar ruwa kuma ido na hawaye saboda zafin yajin, wani abin sha'awa ne ga wasu mutanen.

To amma shin duk da irin yadda irin wadannan mutanen suke fama da yajin a lokacin da suke cin abincin, a iya cewa ba ya musu illa?

Duk da cewa cin abinci mai yaji a kullum da wasu ke yi ba lalle ya yi musu illa ba, wasu da suka nemi dandana hakan ba su ji da dadi ba.

A shekara ta 2014 wasu 'yan jarida biyu daga wata jarida ta birnin Brighton na Birtaniya, mai suna Argus, sun je wani gidan abinci na kwalan da makulashe wanda ya yi fice wajen iya abinci da borkono, domin shedar da kwarewar.

Kowanne daga cikin mutanen biyu ya zabi ya ci wani kayan kwalan da makulashe da ke da yaji domin ya sanin wanda ya fi dadi.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Zafin wani barkonon yana sa wa mutum yanayi kamar na ciwon zuciya

Daya daga cikin mutanen ya kasa jure zafin yajin, inda nan da nan ya nemi madara ya rinka sha domin ya daina jin zafin yajin, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

Shi kuwa dayan cin abin ke da wuya sai kawai ya gamu da ciwon ciki mai tsanani, sannan ya ji kamar hannunsa ba ya aiki, ya fara karkarwa, kuma numfashinsa ya fara daukewa.

Dukkanin mutanen dai sun rika jin zafi da ciwo abin da ya sa har suka dangana da asibiti domin a yi musu magani, domin dayansu ma cewa ya yi ji ya yi kamar zai mutu.

Wasu mutanen da suka yi gasar cin wasu nau'ukan barkonon da suka fi zafi a duniya, a Denmark, sun rika yin amai a gaban jama'a, bayan zufa da shakuwa da suka rika yi.

Shi kuwa Matt Gross a bayanin da ya bayar a kan zafin barkono, inda ya ci barkonon da ya fi zafi a duniya ( Carolina Reapers), ya ce sai da ya kai sa'a 14 kafin ya dawo hayyacinsa bayan da ya ci barkonon guda uku a cikin dakika 21.85.

Tasirin cin barkonon ya hada da alamun ciwon zuciya, wanda daga baya aka ga hakan. Illar cin barkono dai da za a iya gani a fili ita ce ta zafin da ake ji a jiki, in ji Bruce Bryant, masanin kimiyya a Monell Chemical Senses Center da ke Philadelphia.

To wai me yake sa mutum ya ji wannan zafi ne idan ya ci barkono? Idan har cin barkono zai sa mutum ya ji kamar wuta ce a bakinsa, me yake jawo hakan?

Idan aka koma kan nazarin yadda sinadarai ke haduwa su haifar da wani abu daban, musamman kwayar halittar wani sinadari (capsaicin) da ke aika wa kwakwalwa sakon zafi kamar na wuta.

Masana na ganin wannan kwayar halitta ta samu ne domin zama mai gadi ko bayar da kariya daga kwayoyin cuta (fungi) ga tsirran da suke samar da ita. To amma kuma abin mamaki ga dan adam a jikinsa wannan kwayar halitta tana zaburad da jijiyoyin halittarsa ne masu aika sakon zafi na wuta ko makamancin na wutar kamar na barkono zuwa kwakwalwa.

Su dai wadannan kwayoyin halitta ba ruwansu da cewa wai zafin na wuta ne ko na barkono, illa dai kawai su sanar da kwakwalwa kawai.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Da wuya cin barkono ya yi maka wata illa ta tsawon lokaci

Bruce Bryant ya ce zufa hanya ce ta yadda jiki ke sanyaya kansa, saboda haka ne jijiyoyin aikawa da sako kwakwalwa da aka zaburad da su, suke fitar da wasu abubuwa da suke sa jijiyar jini ta bude, abin da ke sa a ji wannan zafi (na wuta ko barkono),wanda hakan wata hanya ce ta kai jini wurin da wannan zafi ko konewa ke afkuwa, a matsayin taimakon gaggawa.

Saboda haka ne a duk lokacin da aka ci yaji ko barkono, wadannan jijiyoyi ko halittu masu aike wa da sako ko taimakon gaggawa, wadanda suke baki ko cikinka, ko kuma wani wuri a jikinka za su shiga aikinsu na kai wannan dauki, ko abin zai kashe ka ne ko kuma zai ruda maka ciki ne, su dai za su yi aikinsu.

Dangane da haka, shi dai cin barkono ko yaji, in ban da zafi ko rudewar jiki ko ciki ta dan wani lokaci kama daga sa'o'i ko kwana daya ko makamancin haka, ba shi da wata illa ta wani lokaci mai tsawo.

Masana kimiyya kamar yadda Bryant ya ce sun gano cewa, yawan ba wa kananan dabbobin da ke shayarwa abu mai yaji ko barkono na tsawon lokaci, zai iya sa jijiyoyin da ke aika wa kwakwalwa sakon zafi su mutu.

Abin ban sha'awa shi ne daman akwai wani nazari da aka yi wanda masana ke ganin kwayoyin halittar barkonon, wata hanya ce ta gargadin hana dabbobi masu shayarwa cinsa.

Tsuntsaye wadanda su kuma suke 'ya'yan barkono gaba daya har ma su watsa a wasu wuraren ta hanyar kashinsu, ba lalle ne suna dauke da wadannan jijiyoyin aika wa kwakwalwa sakon zafin ba, ta yadda har za su ji zafin a baki ko wani sashe na jikinsu.

To amma kuma sabanin duka wannan duk da cewa shi ma mutum dabba ce mai shayarwa, kwayoyin yaji ko barkono za a iya cewa sun gamu da wani yanayi na yadda jikin yake iya jure zafinsu akalla zuwa wani mataki.

Wanda hakan kuma ya sa mutum bai dauki barkonon a matsayin wani babban abokin gabarsa ba, ballantana har ya nemi hanyar ganin bayansa.