Ka san kimiyyar da ke tattare da kashin kare da mutum da giwa?

Giwa na kashi Hakkin mallakar hoto David Hosking/Alamy
Image caption Duk da girman kashin giwa, lokaci daya yake fita da na mutum da kuma na kare

Kusan tsawon lokaci daya mutane da karnuka da giwaye ke dauka wajen yin kashi duk kuwa da babban bambancin girmansu, David Hu da Patricia Yang sun yi mana nazari domin gano abin da ya sa haka.

Mutanen kasar Sin (China) na zamanin da suna amfani da tsarin gano rashin lafiyar da ke damun mutum ta hanyar nazarin yadda kashinsa yake, kamar girma da siffa da kuma yanayin tauri ko laushin kashin.

Haka su ma mutanen Misra da Girkawa da kusan duk al'ummomin zamanin da suna amfani da irin wannan tsari wajen gane irin larurar da ke damun maras lafiya.

Hatta a zamanin yau, likitanka zai iya tambayarka, lokaci na karshe da kaje bandaki, da kuma yadda ka yi kashin da yadda launi ko kamanninsa yake, ka yi masa bayani dalla-dalla.

Ba shakka wannan ba abu ne da kowa zai iya sakin jiki ya yi magana a kansa ba, to amma a nan ne maganar kimiyya ta shigo ciki, domin abin da ba ma son mu yi magana a kai shi ne zai iya cutar da mu, kamar yadda bincike ya nuna cewa cutukan da suka shafi kashi, kamar su gudawa da sauransu na jawowa Amurkawa asarar dimbin kudade a duk shekara.

Sai dai a nan ba wai yadda za a shawo kan irin wadannan matsaloli ba ne babban abin da muka sa a gaba ba, game da yadda ake yin kashi ba. Wani abu ne na daban, wanda ya ma fi matsala.

Tsawon lokaci na samu kaina a aikin nazarin yadda halittu ke zuba kashinsu, inda na wasu ke kasancewa kamar kwallo ko kwayar wani abu, wasu kuwa nasu yana zama kamar maciji, ko kuma wani ruwan tabo.

Ba kamar mutanen da ba, a yau mu ba mu yarda cewa za a iya hasashen gobe ba daga yanayin kashin yara. Amma kuma mun yarda cewa yana da kyau mu san dalilin da ya sa kowa ne kashi yake da siffarsa ta daban.

A matsayinmu na masu nazari kan kimiyyar abubuwan da ke da ruwa, mun hada hannu da kwararren likitan hanji Daniel Chu, da wasu dalibai biyu Kaminski da Morgan LaMarca, wadanda suka dauki hoton bidiyo na lokacin da wasu dabbobi masu shayarwa 34 ke kashi da kuma tattara kashin nasu, a gidan namun daji na Atlanta, domin su yi nazari a kai.

Mun gano cewa yawancin giwaye da sauran dabbobi masu cin ciyawa, kashinsu ruwa-ruwa ne, yayin da yawanci damisa da dabbobin da ke cin nama suke kashi dunkulalle.

Haka kuma mun yi nazarin bambancin warin kashin dabbobin, daga wanda ya fi wari zuwa wanda ba shi da wari sosai. Tarin yawan dabbobin da ake da su a gidan namun dajin ya kuma ba mu damar iya nazari a kan mizanin da muka tsara na lokacin da dabba ke dauka tana kashi.

Sannan mun kuma sanya kashin a wata na'ura da za ta iya auna yawan sinadarai masu ruwa da ke cikinsa da kuma wadanda ba na ruwa ba, wato na kwaya-kwaya.

Abin da kuma muka fahimta a nan shi ne, manyan dabbobi suna kashi mai tsawo kuma cikin sauri. Misali giwa tana kashin da tsawonsa ya kai na santimita (centimeter) shida a tsawon a cikin dakika daya, wato kusan saurin linki shida a kan yadda kare yake yin kashinsa.

Shi kuwa mutun yana kashinsa ne a tsakanin santimita (centimetre) biyu a cikin dakika daya.

Gaba daya wannan na nuna cewa, tsawon lokacin da dabbobi ke dauka suna kashi kusan daya ne, wato kusan dakika 12 (da kari ko ragin dakika 7), duk da cewa yawan tarin kashin ya bambanta sosai.

Kusan kashi 66 cikin dari na dabbobi suna daukar tsakanin dakika 5 zuwa 9 suna kashi. Abin mamaki wannan tsakanin lokacin ya yi kankanta, idan aka yi la'akari da cewa kashin giwa ya kai yawan lita 20, kusan linki dubu na kare. To amma ta yaya irin wadannan manyan dabbobi za su iya kashi da sauri haka?

Amsar da muka gano tana tattare ne a abubuwan da ke cikin wani ruwa mai yauki mai kamar majina da ke jikin bangon babban hanji.

Kaurin wannan ruwa ko majina kamar silin gashin mutum yake, siririntakar ta yi tsanani ta yadda sai dai mu iya auna shi ta hanyar auna kashin yayin da ruwan ke tashi a matsayin tiriri.

Duk da sirintakar, ruwan yana da santsi sosai matuka. Hakan ne ya sa kashi yake fita da sauri. Saboda haka idan komai lafiya yake, tsawo da kuma kaurin kashi yakan dogara ne ga, yadda karamin hanji da kuma hanyar takashin mutum ko dabba suke.

To idan muka hada tsawon kashi da kuma abubuwan da wannan ruwa mai santsi mai kamar majina ya kunsa, daga nan muke iya gane yadda halitta ke kashi.

Manyan dabbobi suna da kashi mai tsawo, da kuma majina ko wannan ruwa mai kauri, ta yadda za su iya fitar da kashin da karfi kuma cikin sauri. Idan babu wannan ruwa mai yauki to da kashi ba zai iya yuwuwa ba.

Idan aka samu wani sauyi a wannan majina ko ruwa da ke jikin bangon babban hanji, to za a iya samun matsaloli ko rashin lafiya da dama.

Bayan burinmu na sanin kwakwaf na kimiyya, nazarinmu a kan yadda ake kashi yana da amfani a rayuwarmu ta yau da kullum.

Domin ta wadannan bayanai ne muka iya tsara kunzugu na manya wanda 'yan sama-jannati ke amfani da shi, domin su 'yan sama-jannati suna son kasancewa sanye da kayan musamman irin na tafiya zuwa sararin samaniya amma kuma kunzugun da za su yi amfani da shi a kayan na kawo musu cikas kan hakan.

To ta hanyar wannan nazari ne, inda muka yi amfani da sanin kaurin ruwan da ke cikin kashi, muka tsara kunzugun da yake hana kashi taba fatar mutum.

Wannan kunzugu na musamman da muka yi ya zo matakin kusa da karshe na gasar hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka, NASA, wadda aka yi a farkon shekaran nan.