Ka san baiwar tamatar kudan zuma?

Hakkin mallakar hoto SMUDGE 9000 CC BY SA 2.0
Image caption Sarauniyar kudan zuma tana saduwa da mazaje da yawa, kuma da sun sadu da ita sai su mutu

Idan ana maganar saduwa ce ta namiji da mace tsakanin kowace halitta muna daukar namiji da cewa shi ne ya fi yawan sha'awa. Amma kuma kamar yadda labarin bajintar kudan zuma ya nuna mana, ga alama mata ne za su ciri tuta a wannan fage.

Nick Fleming ya yi nazari

Mun san cewa mazajen dabbobi suna son saduwa da mata da yawa domin samun haihuwa da yawa.

Kuma muna daukar cewa mata sun fi tsantseni saboda sun fi mayar da hankali wajen haihuwar 'ya'ya kuma ba sa kara damarsu ta hayayyafa domin yawanci suna zama ne da namiji daya.

Wadannan na daga cikin muhimman batutuwan da nazarin samuwar halitta ya mayar da hankali a kai. Kuma su ma sun kauce hanya ko kuma a ce ba su fahimci lamarin ba.

Labarin nazariyyar halin halittu da ke nuna cewa namiji hariji ne mace kuwa tana da son zabi ko tsantseni ya dogara ne kan abin wasu suka kira nazariyyar Darwin da Bateman.

A wani littafi da ya rubuta (The Descent of Man and Selection in Relation to Sex), Charles Darwin daya daga cikin wadanda suka kirkiro nazariyyar asalin halitta, ya bayyana yadda maza suke da sha'awa sosai kuma suke bin mata sosai.

Su kuma matan in banda kadan daga cikinsu ya ce, ''su na da yanga da jan hankali kuma yawanci sai a dauka suna son gudun namiji ne.''

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tarin kudan zuma

A 1948 masanin kimiyyar kwayoyin halitta na Ingila Angus John Bateman ya wallafa abin da a yanzu aka fi sani da gwajin da aka samu yawan mata da maza daidai na wasu kwari (fruit flies) wadanda aka sa su a kwalabe.

Masanin ya zabi kwari ko kudajen da suke da wasu kamanni kamar fuka-fukai da suka dan nade da kananan idanuwa da kuma gashi mai kauri domin ba shi damar zaben irin 'ya'yan da za su haifa.

Daga nan sai Bateman ya ayyana cewa akwai bambanci mai yawa tsakanin maza da mata a fannin haihuwa da saduwa.

Yayin da saduwa da yawan mata ke kara damar yuwuwar yada kwayoyin halitta ko kamannin namijin ba haka lamarin yake ba a bangaren mata.

Wannan nazarin ya yi tasiri sosai a kan masana kimiyyar samuwar halittu har tsawon shekaru gommai.

Ba shakka wasu daga cikinsu sun nuna misalan yadda wasu jinsun halittun inda nazari ya nuna an samu akasin abin da Darwin da Bateman suna nuna na rawar da maza da mata ke takawa a bangaren jima'i.

Amma kuma ba a kai ga gane cewa nazariyyar Bateman ta dogara ne ga gwaji da kuma alkaluman da ke da matsala ko aka yi kura-kurai ba, har sai bayan da aka wallafa wasu kasidu biyu a shekara ta 2007 da 2012.

Hakkin mallakar hoto USGS BEE INVENTORY AND MONITORING LAB
Image caption Namijin kudan zuma, yana mutuwa da ya yi jima'i da Sarauniya

Patricia Adair Gowaty ta jami'ar California a Los Angeles ta maimaita ainahin irin nazarin da ya yi.

Ta nuna cewa tsarinsa kawai zai iya nuna iyaye ne idan 'ya'ya suna da kamanni na uwa da uba, kuma bayanansa ko alkaluma za su kasance daidai ne kawai idan wadannan 'ya'ya suka kasance suna da inganci kamar wadanda suke da kamanni daya ko kuma babu wannan klamanni, wanda kuma ba haka suke ba.

Kuma dukkanin wannan na nuna cewa alkaluma da sakamakon nazarin Bateman ba daidai suke ba.

Wannan cikin sauki shi ya kawo mu kan kudan zuma. A farkon rayuwarsu sarauniyar kudan zuma tana saduwa da mazaje daban-daban wadanda suke mutuwa da zarar sun zuba maniyyinsu.

Sarauniyar tana adana wannan maniyyi ta yi ta amfani da shi har tsawon rayuwarta. Su kuma matan kudan zuman masu aiki (worker bee) wadanda suke saduwa da namiji fiye da daya sun fi samar da zuma.

Ana ganin wannan harijanci (saduwa da maza da yawa) yana taimaka musu wajen samun kariya daga cututtuka ta hanyar bunkasa kwayoyin halittarsu.

Saboda haka ba abin mamaki ba ne a lokacin da Hector Cabrera-Mireles, wanda a lokacin yake jami'ar Florida ya sake bibbiyar nazarce-nazarcen da aka yi a baya domin gano tamatar kwaron da ta fi saduwa da maza ya mayar da hankali kan kudan zuma.

Tamatar kudan zuma na Turai an gano tana saduwa da namiji sau 20 yayin da ta yankin Asia ta ke yin jima'i sau 30.

Sai dai Dakta Cabrera-Mireles ya ayyana cewa tamatar katon kudan zuma na Kudu da Kudu maso gabashin Asiya ita tafi saduwa da maza da yawa, inda a bincikensa ya gano cewa mata suna saduwa da maza har 53.

Sai dai kuma a wani nazarin mai binciken ya gano cewa tamatar wani nau'in buzuzu da ake kira 'cobalt milkweed' da Ingilishi tana jima'i har sau 60, sai dai masanin bai zabe ta ba a matsayin wadda ta fi yawan jima'i ba domin takan sadu da namiji daya fiye da sau daya.