Ka san cewa arzikin dare daya kan sa kadaici?

Mai arzikin dare daya cikin kadaici

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Idan ka samu arziki dare daya, sai ka kasa gane abokananka na gaskiya

Bayan sama da shekara 30 na aikin hidima a cikin jirgin sama da Sandy Stein mai shekara 65 ta yi, yanzu dai Allah ya tarfa wa garinta nono, ta yi arzikin dare daya. Sai dai dunkiyar ta zo mata da wani sauyi na rayuwa, na zaman kadaici.

Stein tana shekara 53 ne a lokacin da ta kirkiro dan wani abu da za ka makale mukullayenka a jiki sannan ka makala shi a jikin jakarka ta yadda a duk lokacin da za ka dauko mukullayen naka, wannan abin za ka jawo, ba sai ka bude jakar kana ta neman mukullayen ba.

A wannan shekara ta sayi mota mai tsada, ta dauki ma'aikata nata na kanta a karon farko, sannan kuma ta samu dala miliyan hudu a cinikin da ta yi.

Abubuwan da suka same ta sun kasance tamkar mafarki. Abin mamaki a wurin Stein shi ne, duk wannan gagarumin ci gaba da ta samu, ya tabbata ne a dalilin zaman kadaici a gida.

Saboda mijinta ya sake ta, domin shi ne ke daukar dawainiyar iyalin amma kuma sai ya kasance yana bakin ciki da ci gaban da ta samu lokaci daya, in ji ta

Wasu daga cikin kawaye da abokan Stein su ma sai suka rika yi mata kyashi, da bakin ciki suna fadan abubuwa marassa dadi a kanta, kamar yadda ta ce.

Yayin da wasu mutanen ba za su hakura da fafutukar ganin sun yi kudi ba, wadanda suka yi sa'a suka samu, sukan ce, dukiya kan sa mutum ya shiga kadaici, kuma mutane a kullum kwadayin zama kamarsu suke yi, amma su kuma lamarin ba haka yake ba a wurinsu.

Arzikin dare daya yakan shafi rayuwar mutum ta kowane fanni, abin ma yakan damu wasu mutanen, in ji Dakta Stephen Goldbart, na cibiyar nazari da bayar da shawarwari kan harkokin kudi ta Money, Meaning & Choices Institute, wanda ke harka da attajirai.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Yawancinmu muna kaunar yin arziki dare daya, amma kadan ne muka san hakan kan haifar da kadaici

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ya ce abu ne mai sauki ka fara samun kanka cikin matsalar yin kudi dare daya, ta yadda za ka rika tunanin matsayinka, tsakanin maras kudi a da da kuma mai kudi a yanzu, kari kuma da matsalar kadaici da bacin rai da za ka rika fama da su a lokaci daya.

Matsalar 'yan uwa da abokai

Tsawon lokaci yawancinmu muna cike da buri da kuma tunanin yadda za mu yi kudi. To amma idan har muka dace hakan ta tabbata muka samu kudin dare daya, sai ka ga abin ya zo mana ba shiri, domin za ka ga mun kasa jure halayyar wadanda ke tare da mu, yadda za ka ga sun sauya yadda suke daukarka.

Ko da yake daman ba abu ba ne da ka dade kana nazari ko tunani a kai, saboda haka idan ka ga abokai da 'yan uwa sun fara neman tsoma baki ko shiga harkokin kudinka, ko suna son shiga harkokin rayuwarka, sai abin ya ba ka mamaki.

Duk wannan abu ne mai wahala da zai zo maka cikin sauri, in ji Goldbart, wanda yakan yi aiki da kwararrun 'yan kasuwa a Silicon Valley.

Kudi yana sauya mutane

A daya bangaren, kudi na sa mutane su sauya hali. Wani lokacin sabbin mutanen da suka yi kudi dare daya, ko da sun sani ko ba su sani ba, sukan yi wasu dabi'u kamar almubazzaranci, ko barin wasu halaye da za su iya haddasa sabani ko rashin jituwa tsakaninsu da dadaddun abokansu, da abokan aiki, kamar yadda masaniya a kan harkokin kudi Megan Ford ta ce.

Ta kara da cewa, abokanai za su iya kasa bin irin sabon tsarin rayuwar da ka samu kanka a ciki, sanadiyyar dukiyar da ka samu dare daya, sai ka ga sun yi kokarin bijirewa, wanda hakan zai kara cewa ka cikin kadaici.

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Dukiya kan sa mutum cikin kadaici

Jurewa halayyar abokanai da dangi kusan shi ne babbar matsala. Za ka ga wasu sabbin abokanai na ta kokarin kulla alaka ko matsowa kusa da kai, idan ka yi arziki lokaci daya. Abokanai da 'yan uwa za su yi ta kokarin kusantarka, in ji Golbart.

To me za ka yi idan abokanai da dangi suka fara maka bambadanci da neman gindin zama a wurinka? Yawancinmu za mu shiga zargi ne. Za mu rika cewa, ina wadannan abokanan da 'yan uwan suke a lokacin da nake fafutukata, ina aiki tsawon dare?

Abin da mutum zai yi a nan daman ba wani sabo ba ne, yadda za ka ga ya yi kokarin kaffa-kaffa da wasu, daga cikin abokan da 'yan uwa. Za ka ga ya fi mu'amulla da wasu saboda bai san wanene na gaskiya ba.

Masanin ya ce, za ka ga duniyar mutumin (wanda ya samu kudin dare daya) ta kankance, ya karkata ga mutanen da suke da kudi kamarsa.

Abu ne mai wuya wannan dabi'a ko hali ya bar ka, ko da kuwa dukiyar ta ci gaba da bunkasa, wato ka zama dadadden attajiri. Sanin abokin gaskiya yana da wuya. Kuma idan har ka yi rashin sa'a ka hadu da macuci wato abokin karya, sai ka kara nesanta kanka daga mutane in ji Ford. Ta ce abu ne mai wuya ka iya tantancewa tsakanin abokin gaskiya da na karya.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Dukiyar dare daya kan sa mutum ya kasa gane abokanan gaskiya

Mutanen da suka yi arzikin dare daya, na cewa kadaicin da suke samun kansu a ciki na kasancewa ne sakamakon sauyin bukatu. Kamar yadda Stephan Goss, masani kan hanyoyin ba wa mawallafa shawara, mai shekara 28, dan Switzerland, wanda ya koma San Diego a Amurka ya ce, shi sabbin abokanai ya nema wadanda ke irin sabuwar rayuwarsa, amma kuma bai yi watsi da tsoffin ba gaba daya.

Duk da cewa Goss bai yi watsi da tsoffin abokanansa da suka taso tun suna yara ba a Switzerland da kuma a jami'a a Amurka, yana kokarin yin sabbin abokanai 'yan kasuwa.

Ko da yake ba haka lamarin yake ba ga Stein, arzikin dare dayan, ga alama ba ya haifar da wani babban sauyi ga mutanen da suka girma, kuma wadanda suka jima suna aiki, musamman saboda cewa wadanda suke kusa da su, daman suna tsammanin mutumin da ya girma ya kai wadannan shekaru a ce ya mallaki dukiya, in ji Goldbart.

Babu wani sauyi da aka samu a kawance ko mu'amullar Stein wadda ta gurbata tsakaninta da wasu abokanan na da, amma ta ce abin da ta yi shi ne, kokarin yin sabbin abokanai.

A yanzu dai Stein tana aiki da cikakkun ma'aikata biyar, kuma ta ce ta kulla kyakkyawar alaka da amana tare da su. Bayan tsawon lokaci ta fahimci su wane ne abokanta na gaskiya a lokacin da take aikin cikin jirgi, ta nemo su kuma tana yi musu alheri.