Ka san yi wa kanka magana ba hauka ba ne, alama ce ta nasara?

Mutum na magana da kansa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ta hanyar magana da kanka ka fi samun kwarin guiwa da tunani da kuma kwanciyar hankali

Eugene Gamble ya shafe kusan tsawon rayuwarsa ta aiki a matsayin likitan hakori a Landan, inda shiru kuma cikin natsuwa da kwazo yake yi wa mutane aiki a hakoransu.

Kwatsam , shekera uku da ta wuce sai kawai ya yanke shawarar barin wannan aikin da kusan tsawon rayuwarsa abin da ya sani kenan domin ya koma kasuwanci.

To sai dai akwai matsala daya, matsalar ita ce bai iya kasuwanci ba. Yayin da ya ga duk hanya ko kasuwancin da ya bullo wa sai ya kasa, sai guiwarsa ta yi sanyi.

Da zai iya komawa aikinsa na likitan hakori, to amma ya kuduri aniyar lalle sai ya yi nasara a fagen kasuwanci. Daga nan ne ya dauko hayar wani kwararre da zai horad da shi a kan dabarun kasuwanci, wanda shi kuma ya ba shi wata shawara ta daban.

Gamble wanda ke ba wa masu kudi shawara kan zuba jari a harkokin gidajen haya, ya ce, ''mutumin sai ya gaya min cewa in rinka fito da maganata fili ina yi ni kadai''. Wato magana da kansa a fili.

Gamble ya ce abin ya zamar masa banbarakwai, domin wani abu ne sabo a wurinsa. Ya kara da cewa bai yi tunanin hakan zi yi wani amfani ba, to amma yana fara gwadawa sai ya ga amfanin hakan.

Abin zai iya zama wani bako ko banbarakwai domin ana daukar mutum ya rika magana shi kadai kamar wata alama ce ta tabin hankali.

To sai dai akwai tarin bincike da ke nuna cewa mutum ya rika magana da kansa ko shi kadai, yakan sa mutum ya yi saurin tuna abu, da ba shi karfin hali, da mayar da hankali kan abin da yake yi da sauransu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Magana da kanka na sa ka kware a tattaunawa

Masani a kan tunanin dan adam, mataimakin farfesa Gary Lupyan, na Jami'ar Wisconsin, wanda ya yi nazari a kan yadda idan mutum yana sauraren kansa yana magana hakan zai taimaka masa hadda, ya ce, yin hakan (wato mutum ya rika magana da kansa), ba hauka ba ne.

Ya ce duk abin da za ka furta ba lalle ne ka san shi ba, za ka ba wa kanka da kanka mamaki.

A sakamakon nazari da binciken da ya yi a wannan fanni, wanda kusan shi aka fi karantawa ya sa mutane suna kallon abubuwa a kwanfuta, inda ya sa wasu daga cikin su rika fadar sunan abin da suke kallo da karfi, yayin da ya sa sauran su yi shiru ka da su furta sunan. Ka san sakamakon da aka samu?

Wadanda suka fadi sunan abin a fili ko da karfi, su suka iya ganin abin a kwamfutar da sauri.

A wani binciken irin wannan da aka yi , shi ma an sa mutane su fadi sunayen wasu kayan abinci a fili. Daga nan kuma sai aka kawo hotuna aka sa su nuna abubuwan. Wadanda suka fadi sunayen abubuwan a fili su suka yi saurin ganinsu.

Ya ce duk da cewa mun san yadda ayaba take amma fadin kalmar a fili na taimaka wa kwakwalwa ta samu karin bayani ko masaniya a kan ayaba, abin da ya hada da yadda take a zahiri.

Mai binciken ya ce, ba shakka za mu iya gano ayabar a kantin kayan abincin, ko da ba mu furta sunanta ba a fili, amma za mu fi gano ta da sauri idan mun furta sunanta.

Mutum na jin sauki idan ya yi wa kansa da kansa magana

Wata tsohuwar malamar koyar da ilimin tunanin dan adam, Anne Wilson Schaef, wadda yanzu marubuciya ce da kuma gabatar da jawabi, yawanci takan sa mutanen da take koyawa jawabi su rika magana da kansu.

Bayan karfafa wa daliban nata haddarsu, ta yadda suke iya tuna abu da wuri, hakan ya kuma sauya yadda galibinsu ke ji. Misali idan ran maras lafiya ya baci, sai ta bukace shi ya fadi abin da ya bata masa rai a fili ( da karfi). Daga nan sai ka ga wannan bacin ran ya kau.

Tana ganin hakan abu ne da yake da alaka da wanda yake sauraron. Ta ce, dukkaninmu muna bukatar mu yi magana da wani wanda yake da sha'awarmu da basira, wanda ya san mu sosai wanda kuma yake goyon bayanmu, kuma wannan ba kowa ba ne illa mu kanmu.

Ta ce, kusan ba wanda muka fi sani kamar mu kanmu. Saboda haka sanin kanmu da yadda muke ji ka iya taimaka mana mu gyaru.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gabatar da kanka da wakilin suna na ''shi'' zai iya sa a dauke ka mai ji da kai, amma Kross ya ce hakan zai sa ka fi kwazo

A shekara ta 2014 Ethan Kross na Jami'ar Michigan ya yi wani rubutu wanda a ciki yake cewa magana da kanmu ka iya ba mu kwarin guiwa da jin dadi a kan kanmu, wanda hakan zai iya taimaka mana mu yi maganin wani kalubale da ke gabanmu. Amma sai mun furta kalmomin da suka dace kafin hakan ya yi aiki.

Kross tare da wasu abokan bincikensa, sun gudanar da gwaje-gwaje da dama, inda suka sa mutane su bayyana wani yanayi ko hali da suka shiga, ta hanyar amfani da sunansu ko kalmomi kamar ''kai'' da ''shi'' da ''ke.''

Daga nan ya gano cewa mutum ya yi magana da wakilin suna na ''kai'' ko ''shi'' ko ''ke'' yana nufin shi kansa, hakan na taimaka wa mutum ya kwantar da hankalinsa da tunaninsa fiye da wadanda suka yi amfani da kalmar wakilin suna ta ''ni''.

A wani nazarin Kross wanda ya gabatar da sakamakon binciken nasa a Harvard, ya bukaci mutane da su gabatar da kansu ( a ciki) da wakilin suna na ''kai'' ko ''shi'' a yayin da suke shirya wani jawabi da za su gabatar, sai ya gano hakan ya sa mutane sun fi kwantar da hankalinsu da kwarin guiwa, tare da tunani da kyau da kuma iya yin aiki fiye da wadanda suka yi amfani da kalmar wakilin suna ta ''ni''.

Sakamakon ya ba wa Kross mamaki, har ta kai yana sa karamar 'yarsa tana magana da kanta wato ita kadai, inda take gabatar da kanta da kalmar wakilin suna ta ''ita'', a duk lokacin da ranta ya baci. Maimakon ta ce ''ni'' sai ta ce ''ita'', misali ; ''Me ya sa na yi haka?'', sai ta ce, ''Me ya sa ta yi haka?''

Duk da cewa har yanzu Gamble bai fara gabatar da kansa da kalmar wakilin suna ta ''shi'' ba, saboda yana ganin hakan kamar wani bakon abu, mai ba shi horo ya shawarce shi da ya rika amfani da kalmomi na karfafa zuciya da tabbatar da iko ko matsayi, misali, ''ka yi kawai ko ma me zai faru ya faru''. Ya dauki wanna shawara kuma ya ce tana aiki.

Kwarewa wajen gabatar da jawabi

Wannan dabara ta magana da kai, ta sa Gamble ya kware wajen gabatar da jawabi. Kafin ya gana da wani attajirin mai zuba hannun jari, yakan yi nazarin abin da zai gabatar masa, inda yakan yi ta karanta abin da ya rubuta a fili, ya saba da kalmomin da ke ba shi matsala.

Ya ce ta hanyar sauraren kansa yana karatu, hakan na sa ya iya tsara maganganunsa da tunaninsa da kyau, kuma yana tuna bayani ko abin da zai gabatar da kyau.

Wani lokaci mutum ya yi magana shi kadai da karfi ba abu ne da za a ji dadin yi ba, kuma ba za mu so a ganmu ko da yaushe muna magana da kanmu ba a bainar jama'a, wanda abin da ya sa yawancinmu ba ma yin hakan kenan.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yara na magana da kansu ko da yaushe - kila akwai abin da suke yi wanda ba mu sani ba

Yara su kuwa suna yi, domin bincike da dama ya nuna cewa, tsarin mutun ya rika magana da kansa na taimaka wa yara. Domin a wani nazari na shekara ta 2008 a gano cewa yaro dan shekara biyar da ke magana da kansa (magana shi kadai) da karfi, ya ci kwazo a aikin da ya shafi kwakwalwa, fiye da idan ya yi shiru.

Gamble yana ganin wannan tsari ya taimaka masa sosai ya ginu tare da samun kwarin guiwa fiye da da, duk da cewa akwai wasu abubuwan da suka taimaka masa ya yi nasarar juyewa daga likitan hakori zuwa dan kasuwa mai harkar gidaje.