Ka san yadda ya kamata ka wanke hannunka kuwa?

Wanke hannu da sabulu Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Bayan wanke hannu da sabulu akwai matakan da za ka bi na raba hannun da kwayoyin cuta

Wanke hannu bayan an je bandaki abu ne da yake da muhimmancin gaske ko ma ya zama wajibi. To amma wace hanya ce ta fi dacewa a bi wajen wanke hannun, ko wane tsari ne mafi kyau?

Da ruwan zafi ko na sanyi ya kamata a yi? Da sabulu ko toka ko wani abu daban ya kamata a yi? Claudia Hammond ta yi mana nazari kan wannan lamari.

Idan aka yi maganar wanke hannu, sai ka dauka magana ce mai sauki kawai, to amma ba haka abin yake ba. Duk da cewa akwai sheda da yawa da ke nuna muhimmanci da amfanin wanke hannu, bayan an je bandaki, ko kafin cin abinci, ko yin wani abu da hannun, kamar shiga motar da mutane suke da yawa da sauran abubuwa da mutum zai iya diban datti a hannunsa, kiyasi ya nuna cewa kashi biyar cikin dari ne kawai na mutane suke wanke hannunsu da kyau.

Wani nazari da aka yi a kan mutane 3,000 ya gano cewa kashi 10 cikin dari ( 300) na mutanen ba su wanke hannunsu ba sam-sam bayan da suka shiga bandaki, kuma ko da sun wanke ma kashi 33 cikin dari ba su yi amfani da sabulu ba.

Wannan matsala ce saboda, za mu iya yada cuta daga hannunmu zuwa hancinmu da bakinmu, domin za mu taba fuskarmu da hannun bayan da muka fito daga bandaki, kuma daga nan kwayoyin cutar za su shiga cikin cikinmu.

Masu bincike a Amurka da Brazil sun gano cewa, mukan yi amfani da tafin hannunmu mu taba abubuwa ko wurare kusan sau 3.3 a cikin duk sa'a a daya, a wurin da ake da jama'a, sannan kuma muna taba baki ko hancinmu kusan sau 3.6 a duk sa'a daya.

To a hakan haka za ka ga lalle yana da muhimmancin gaske mu rika tsaftace hannunmu da kyau. Sai dai abin a nan shi ne akwai batutuwa da dama ko ma almara kan yadda ya kamata mutum ya wanke hannun nasa.

Shin sai ruwa yana da dimi ko zafi ne zai wanke maka hannu da kyau?

A wani bincike da aka yi a kan mutane 500 a Amurka, kashi 69 cikin dari na mutanen sun yi amanna cewa dimi ko zafin ruwa yana da tasiri ko taimakawa wajen wanke datti a hannu.

Gaskiya ne cewa zafi yakan kashe kwayoyin cuta, to amma fa sai ruwan ya yi zafi sosai kuma a bar shi ya dade a kansu kafin ya iya kashe wasu kwayoyin, wanda kuma idan har ya kai wannan zafin zai iya kona ka.

Sannan wani gwaji da aka yi na kimiyya ya nuna babu wani bambancin gaske tsakanin wanke hannu da ruwa mai sanyi ko zafi ko dimi dangane da yawan kwayoyin cutar da ke barin hannun. Sai dai kada mu manta da cewa a dabi'ar dan adam, mutum ba zai yarda ya sa hannunsa ya dade a cikin ruwan zafi ko na sanyi ba, wai domin ya wanke hannunsa da kyau, domin ba zai yarda da abin da zai cutar da shi ba.

Amma idan da ana son kashe kwayoyin cutar ne ba shakka idan aka zuba wa wasu ruwa mai zafi suka dade a ciki za su iya mutuwa.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Bincike da dama ya nuna amfani da takardar goge hannu da ake jefarwa bayan amfani daya ta fi amfani

Ko ruwan magani na wanke hannu na musamman ya fi sabulu amfani?

Wani nazari da aka yi a kan wannan a shekara ta 2007 ya nuna cewa sinadarin (triclosan) da yake cikin yawancin magani ko ruwan wanke hannu na musamman bai fi sabulu rage yawan kwayoyin cuta ( bakteriya) da ke hannun mutum ba. Wani nazarin na kwanan nan da aka yi a shekara ta 2015 ma ya kara tabbatar da wannan sakamakon.

A halin da ake ciki ma, karin bincike da nazari da aka yi a baya bayan nan ya nuna cewa amfani da sinadarin triclosan a ruwan magani na musamman na wanke hannu yakan iya kara wa kwayoyin cuta na bakteriya juriya, su zauna a hannun, wanda wanna kuma zai iay haddasa matsala ta sanadiyyar samun karin kwayoyin halitta (hormone) a jikin mai rai dan adam ko dabba, wanda hakan ya sa aka hana amfani da sindarin na triclosan a ruwan magnin wanke hannu a Amurka da Turai.

Bayan wanke hannu, yana da kyau ka yi amfani da tawul ko wani kyalle ko wani abu domin busar da hannunka?

Bincike da dama da aka yi ya fifita amfani da irin takardar nan ko auduga ta musamman, wadda ake amfani daya kawai da ita, wajen goge hannunka ya bushe bayan ka wanke, maimakon ka yi amfani da tawul ko wani kwalle. Domin shi kansa kwalle ko tawul mai lema matattara ce ta zaman kwayoyin cuta.

To mu dawo kan maganar amfani da sabulu da ruwa mai sanyi ko mai dimi ko zafi.

Kana bukatar tsanewa da busar da hannunka bayan ka wanke?

Idan kana sauri ba kasafai za ka iya tsayawa ka busar da hannunka ba bayan ka wanke shi. To wannan ba wata matsala ba ce idan har ba ka taba wani abu ba da hannun lokacin da kake fita daga bandakin.

Amma idan har ka taba wani abu, to zai iya kasancewa ka debi wasu kwayoyin cutar, domin su daman sun fi hawa jikin mutum cikin sauki idan da ruwa ko danshi.

Haka kuma idan ba ka busar da hannun naka ba, bayan ka wanke shi, ka rasa damar raba kanka da ragowar kwayoyin cutukan da ka iya ragewa a tafin hannun naka.

To duk ma dai tsarin da ka zaba na wanke hannunka da busar da shi, muhimmin abin da masu bincike suka gano shi ne, ka dauki tsawon lokacin wankewar fiye da yadda kake tsammani.

Ka wanke hannuwan da sabulu mai kunfa da kyau, ciki da bai, tafi da tsakanin yatsu da karkashin farce akalla daga tsakanin dakika 15 zuwa 30.