Ka san dakin da ya fi shiru a duniya?

Dakin gwaje-gwaje na Microsoft, wanda ya fi ko'ina shiru a duniya Hakkin mallakar hoto Microsoft
Image caption An dauki kusan shekara biyu a zayyana da ginin dakin

Kamfanin Microsoft ya gina wani daki da yake shiru ba a jin karar komai, ta yadda hatta kasusuwan jikinka ma za ka ji motsinsu. Kuma dakin na taimaka wa wajen kirkiro kayan laturoni da za a bullo da su nan gaba. Richard Gray ya yi mana nazari.

Idan LeSalle Munroe ya tsaya cik na dan wani lokaci a cikin ofishinsa, wani abu mai tsoratarwa yakan faru. Zai iya jin karar tafiyar jininsa a cikin jikinsa da motsin idanuwansa a cikin kwarminsu.

Yayin da wasu mutanen ke aiki a wurin da ke cike da karar kwamfuta da sauran na'urori da surutai da kai-kawo na abokanan aiki, Munroe yana cikin wurin da babu wani motsi ko kara. Ofishinsa shi ne wurin da ya fi shiru a duk duniya.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Hatta karar tafiyar jinin jikinka za ka iya ji a dakin

Shi dai wannan daki na musamman yana boye ne can a karkashin Gini na 87 a hedikwatar kamfanin Microsoft da ke Redmond a birnin Washington, inda dakunan binciken kimiyya na manhajar kamfanin suke.

A nan ne aka kirkiro fitattun kwamfutoci da manhajar kamfanin irin su Surface computers da Xbox da Hololens. Injiniyoyin kamfanin ne suka kirkiro tare da gina dakin ( anechoic chamber), domin ya taimaka musu wurin gwajin sabbin na'urorin da suka kirkiro. Kuma a shekarar 2015 dakin ya kafa tarihin zama wurin da ya fi zama shiru a duk duniya.

Ta yadda za ka kara fahimtar yanayin wurin karara, shi ne, idan mutum ya yi rada tana linkawa kusan sau talatin a kara, yayin da karar numfashin mutum kuma ke linkawa sau goma.

Munroe ya ce, ''Idan aka rufe kofar dakin yanayin wani ne na daban wanda ba ka taba ji ba, idan ka tsayar da numfashinka za ka iya jin zuciyarka tana bugawa da tafiyar jininka a jiki. Ni kaina ba kasafai nake zama a ciki ba da kofar a rufe.''

Hakkin mallakar hoto Microsoft
Image caption Ba karar da take daga waje da za ta shiga dakin

Sai da aka dauki kusan shekara biyu ana zayyanawa da gina dakin, inda a yanzu Munroe da abokan aikinsa ke aiki a kullum na kirkiro da kayayyakin fasaha na kamfanin Microsoft.

Hatta samo ginin da ya dace inda za a yi wannan daki sai da aka dauki kusan wata takwas ana gwaje-gwaje domin samun wurin da yake shiru ba hayaniya ko wata kara da za a iya yinsa.

Dakin dai an yi shi ne can a cikin tsakiyar wasu dakuna wadanda kowanne bangonsa ya kai kaurin inci 12, wanda hakan ya sa ba wata kara daga waje da za ta shigo cikinsa.

Idan jirgin sama na yaki zai tashi a kusa da ginin gidan da dakin yake abin da za ka ji a daki na karshe da wannan ofis yake ciki bai wuce kamar rada ba.

An tsara gin ofishin ta wata hanya ta musamman ta yadda ba inda gininsa kai tsaye ya taba ainahin ginin gidan da yake ciki. In ji Hundraj Gopal, babban injiniyan al'amuran da suka shafi mutane na kamfanin na Microsoft.

Wannan daki ko ofis yana da fadin kafa 21 ta kowane bangare. Kuma a dukkanin bangarorinsa shida an shinfida masa abin da ke hana sauti wucewa mai tsawon kafa hudu, wanda ke hana amsa amo na duk wani sauti da aka yi a cikin dakin.

Ita kanta kofar da sauran duk wasu tsare-tsare na dakin an yi su ne na musamman ta yadda ba wani sauti ko kara daga ciki da zai fita ko kuma ya shigo ciki daga waje.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Saboda shirun dakin an ce za ka iya jin karar kasusuwan jikinka idan kana tafiya

Gopal ya ce; ''Ga duk wanda yake bukatar irin wannan daki zai iya saye akwai shi.'' Sirrin abin kawai shi ne yadda muka yi dabara da bata lokaci wurin sarrafa hanyar da iska za ta kai ga dakin.

Kafin jami'an littafin bajinta na duniya na Guiness Book of Records su je wurin su yi nazarinsa har ya zama na daya a duniya (-20.6), dakin bincike na kimiyya na Orfield Laboratories da ke Minneapolis shi ne ke da wannan bajinta ta dakin da yake mafi shiru a duniya (-9.4 decibels).

Gopal ya ce; ''Ba wai mun yi niyyar gina wurin da shi ne ya fi shiru ba a duniya. Niyyata mu yi wurin da babu hayaniya ko iya karar da kunnen mutum zai iya ji (0 decibels).

Za ka dauka cewa wurin da yake shiru kamar wannan, zai kasance wuri ne da yake lami lafiya. To amma ga wadanda suka taba shiga dakin lamarin ba haka yake ba ko alama.

Gopal yakan ba wa bakin da suka ziyarci hedikwatar ta Microsoft damar ziyarar dakunan bincike da gwaji na kamfanin, har ma da wannan daki na musamman.

Kuma yawancin mutanen ba sa jin dadi idan suka shiga dakin, ta yadda wasu nan da nan da shigarsu dakin sai su nemi hanyar fita, in ji Gopal.

''Sukan ce ba za su iya zama a dakin ba. Kusan kowa za ka ga ba ya jin dadi. Suna iya jin numfashin wadanda suke can gefe a dakin, da kuma kugin cikin mutane. Wasu mutanen ma 'yan kadan sukan ji juwa ko jiri.''

Wannan zai zama kamar wani abin mamaki kasancewar yawancinmu muna kokarin samun kanmu a wurin da za mu kaurace wa hayaniyar yau da kullum da ke damunmu.

Amma Peter Suedfeld, masanin tunanin dan adam a jami'ar British Columbia, ya kwatanta lamarin da rashin sabo, inda ya ce kamar shiga dakin da yake da duhu ne dudum.

''Da farko za ka ga ba ka ganin komai, amma da ka dan jima a ciki sai idonka ya saba da duhun ka fara gani.''

Idan ka kaurace daga wurin da ake jin kara ko sauti na yau da kullum, to za ka iya jin hatta motsin kasusuwa ko gabban jikinka a lokacin da kake motsi, har ma ka ji karar ta dame ka matuka.

Amma Gopal ya ce; ''Duk da haka akwai wadanda suke jin dadin kasancewa a dakin, suna ma daukar kamar yanayi ne na daidai da zaman natsuwa na ibada.''

Sai dai ya ce mafi dadewa da ya gani wani ya yi a dakin daga cikin masu ziyara shi ne sa'a daya, shi ma din domin tara kudin bayar da agaji ne.

Ya ce, ''ina jin idan ka dade a dakin ka za ka ji ya dame ka. Duk yawun da ka hadiya za ka ji karar hadiyar ta dame ka.''

Hakkin mallakar hoto Microsoft
Image caption Microsoft na amfani da dakin wurin gwaje-gwajen na'urorinsa

A wurin Munroe wannan shirun na dakin yana da wani amfanin wanda shi ne mafi muhimmanci, fiye da jin karar jikin mutum.

Akwai karar da kayan da aka harhada aka tashi na'ura suke yi lokacin da lantarki ya shige su, wanda kila karar zai iya damun mai amfani da na'urar.

Ya ce: ''Ta wannan hanya muke iya gano inda karar ke fitowa sai mu duba yadda za mu yi mu dakatar ko rage karar.

Haka kuma akan yi amfani da hanyar wajen saitawa ko dadada karar da misali danna wayar salula ke haifarwa ta yadda za ta yi dai ga kunnen mutum maimakon ta sa ya ji ba dadi, idan karar ta kasance wata iri.

Hatta masu bincike a fannin lafiya sukan nemi izinin amfani da dakin na Microsoft domin gunar da wasu gwaje-gwaje.

Sai dai Gopal yana taka-tsantsan wajen barin a yi amfani da dakin a fannin likitanci da ya shafi kwakwalwa ko masu larurar tabin hankali, domin abu ne da ke bukatar matakai na izini daga hukuma, saboda hadarin dake tattare da sanya mutumin da ke da larurar kwakwalwa a irin wannan daki.

Ainahin tasirin dakin akan Munroe da Gopal na bayyana ne idan sun fita daga dakin bayan sun dan jima a ciki.

Munroe ya ce; ''Da ka bude kofa za ka ji kamar wata kara mai karfin gaske tana ta bugun kunnuwanka. Kamar ka shiga wata sabuwar duniya ne, za ka ji karar da idan da haka kawai ne ba za ka ji ba, kuma zai sa ka fahimci wani abu.''