Ka san sirrin samun rayuwa mai tsawo? Cin abinci kadan

Kayan abinci mai gina jiki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sai dai yana da wuya mutane su iya kauce wa wasu kayan abincin a yau

Rage yawan abincin da kake ci a kullum zai iya yin babban tasiri a rayuwarka, har ka samu tsawon rayuwa, kamar yadda wadansu nazarce-nazarce masu dadi na kimiyya suka tabbatar.

Ga nazarin Alex Riley

Wani mutum da wata mata sun shirya zamansu na tattaunawar masoya na farko a wani babban wurin cin abinci.

Mutumin mai shekara 33, ya sheda wa matar bai taba yin aure ba kuma duk kusan tsawon shekarun nan ba shi da ko wata budurwa, kuma ko da yake bai fada ba, amma ya san cewa an san yana neman yin aure ne ya samu iyali.

A nata bangaren matar ta gaya masa cewa shekararta 52, ta yi aure amma, auren ya mutu, kuma tana da 'ya'ya da suka dan zarta shekara 20. Mutumin ba shi da wata masaniya, amma yana ganin matar kusan sa'arsa ce ko ma ya girme ta.

To wannan shi ne burin Julie Mattison ta cibiyar nazari a kan girman mutane ta Amurka( National Institute on Ageing (NIA)).

Ta yi fatan samun wani lokaci da za gano hanyar da shekarun mutum za su zama shekaru ne kawai a baki, amma ba tsufan mutum ba, kamar yadda ake gani a yanzu.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Za a dauka wannan abu ne mai wuyar gaske, to amma tuni duniya ta fara gagarumin kokari wajen cimma wannan buri, ta hanyar ci gaban da aka samu a fannin likitanci da kuma tsarin rayuwa mai inganci da jama'a ke bi.

Misali a shekara ta 2014, wani bincike da aka gudanar kan harkokin lafiya a Amurka ya nuna cewa kashi 16 cikin dari na mutanen da suka kai tsakanin shekara 50 da 64,a kullum sukan yi fama da cutuka masu tsanani iri daban-daban.

Shekara talatin baya yawan mutanen da suke da wannan matsala a Amurkar kashi 23 cikin dari ne, wato an samu raguwarsu a gaba, sakamakon wani cigaba. Wannana na nufin kenan bayan samun tsawon rayuwa, mutane na kuma yin rayuwa mai tsawo cikin koshin lafiya akalla idan an kwatanta da wadancan shekarun.

Wannan ya kasance kamar yadda John F Kennedy ya fada a jawabinsa na farko a kan tsufa a 1961, a fadar gwamnatin Amurka, White House, inda ya ce za a iya kara rayuwa a kan shekaru, maimakon a kara shekaru a kan rayuwa.

To me ya kamata mu yi domin tsawaita rayuwarmu da kuma tabbatar da ingancinta fiye da yadda take a yanzu?

Masana kimiyya a fadin duniya na kokarin bin hanyoyi daban-daban domin gano wannan sirri, amma a wurin Mattison da abokan bincikenta, sirrin shi ne sauya yanayin cin abincinmu.

A wurinsu sun yi amanna hanyar samun ingantacciyar rayuwa idan mutum ya tsufa, ba tare da ya rika fama da cutuka ba, ita ce rage yawan abincin da muke ci.

Tun shekarun farko-farko na 1930, bincike ya nuna cewa ragin kashi 30 cikin dari na abincin da wasu dabbobi da kwari ke ci a duk rana, a rayuwarsu dindindin yana sa rayuwarsu ta inganta kuma ta kara tsawo.

Wadannan halittu da aka gano hakan a rayuwar tasu sun hada da tsutsotsi da kudaje da beraye da birai. Kuma ana ganin shi kansa dan adam idan ya bi wannan tsari zai ci moriyar hakan shi ma.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin kayan cin da kake saye na da tasiri ga inganci da tsawon rayuwarka

Maganar cewa abin da mutum ke ci yana da tasiri a kan yanayin lafiyarsa, magana ce da ta girmi duk wani bincike na zamanin yau.

Kamar yadda abin yake a duk wani fage na kimiyya, an fara samun cikakken bayanin hakan ne daga lokacin zamanin da na Girka.

Hippocrates, daya daga cikin likitoci na farko da suka ce cutuka abubuwa ne na rayuwa kamar komai ba wasu abubuwa ba ne na iska ko wani abu makamancin haka, ya lura cewa cutuka da dama suna da alaka da cin abinci da yawa.

Misali a zamanin da na Girkawa mutane masu teba ko kiba sun fi mutuwa suna matasa a kan takwarorinsu sirara.

To haka aka dauko wannan tsari a tsawon shekaru aru-aru, inda a karshen karni na 15, wani mai hali Alvise Cornaro, wanda ke wani kauye a kusa da birnin Venice a Italiya ya gwada tsarin a kansa.

A lokacin Cornaro yana da shekara 40, ya rage yawan abincin da yake ci a kullum zuwa gram 350 (1000 calories), inda yake cin burodi da kwai da biskit ko farfesu. Nama kuwa ya zabi ya rika cin na akuya ko shanu ( maraki) ko na kaji ko kuma makwarwa. Kifi kuwa yana saya ne daga hannun masunta da suka kamo daga rafi.

Cornaro wanda ya rage yawan abincin da yake ci amma ba nau'in abincin ba, ya yi ikirarin cewa ya samu kyakkyawar rayuwa har zuwa mutuwarsa sama da shekara 40 bayan da ya rungumi wannan tsari.

Ko da yake ya sauya ranar haihuwarsa lokacin da ya tsufa, inda ya ce ya kai shekara 98, amma ana ganin yana wurin shekara 84 ne a lokacin da ya mutu- duk da haka ya yi tsawon rayuwa sosai ganin cewa a karni na 16 ne lokacin da ake daukar mai shekara 50 zuwa 60 a matsayin tsoho.

Tsarin na Cornaro yana da ban sha'awa amma kuma ba wani fage na kimiyya da ya dauki abin da ya gano a matsayin hujja kwakkwara.

Ko da kuwa kamar yadda ya ce ya dade kuma bai yi fama da wata larura ko laulayi na tsufa ba kusan tsawon shekara 50, wanda kuma abu ne mai wuya hakan, amma duk da haka za a iya la'akari da shi, sai dai ba za a iya amfani da shi ba a matsayin misali na dukkanin mutane.

Amma dai wani nazari na asali da aka yi a shekarar 1935 a kan fararen beraye,ya nuna rage yawan abincin da suke ci da kusan tsakanin kashi 30 zuwa 50 cikin dari ya sa sun samu karin tsawon rayuwa, ta hanyar jinkirta lokacin mutuwarsu daga laulayi da cutuka na tsufa.

To amma ba shakka ba lalle ba ne abin da ya yi aiki a kan bera ko wata dabba a ce ya yi a kan dan adam.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Idan aka takaita yawan abincin da wannan jinsin birin yake ci yana samun tsawon rayuwa

Yin wani gwaji na tsawon shekaru a kan tare da dan adam tun daga farkon lokacin da ya girma zuwa mutum abu ne mai wahala idan ma har za a iya in ji Mattison.

Domin idan ka fara gwaji da mutum yana tsakanin shekara 40 zuwa 50, kana da karin akalla wata shekara 40 ko 50 ko ma sama da haka.

Ga kuma wasu dabi'u da yanayi na rayuwar mutum da za su iya shafar sakamakon binciken; misali motsa jiki da shan taba da yin maganin cutuka da yanayin lafiyar kwakwalwa, wadanda dukka abubuwa ne da ba za ka iya raba mutum da su ba a tsawon wannan lokaci da kake bincike a kansa.

Wannan ne ya sa a kusan karshen shekarun 1980 aka shirya gudanar da wasu bincike guda biyu daban-daban na tsawon lokaci.

Daya a NIA daya kuma a Jami'ar Wisconsin- inda aka jarraba tsarin na rage yawan abincin da ake ci a kan birai jinsin da ake kira Rhesus da Ingilishi.

Shi wannan jinsin biri bayan kusan kashi 93 cikin dari da kwayoyin halittarsa yake daidai da namu (mutane), yanayin tsufanmu iri daya ne, yadda mutum ke tankwarawa (doro) da sakin fata da tsokar jiki da kuma furfura.

Kamannin suna da yawa da dan adam, yadda shi ma idan shekaru sun ja mutum ke gamuwa da matsalar cutar daji ko ta sukari da cutar zuciya.

Wannan nau'in biri ya dace sosai a yi amfani da shi wajen nazarin idan za a kwatanta da mutum in ji Rozalyn Anderson, ta jami'ar Wisconsin.

An gudanar da gwajin rage yawan abincin da ake ci da kashi 30 cikin dari a kan irin wadannan birran su 76 a Jami'ar Wisconsin inda aka samu irin wannan sakamakon na tsawon rayuwa. Ba tare da cutuka galibi da ke da alaka da tsufa ba.

Misali shi ne na wani biri da ake kira Sherman mai shekara 43 daga NIA. Mattison ta ce tun lokacin da aka dora shi a kan irin wannan tsari na rage yawan abinci, kusan ya samu garkuwa daga abubuwan da ke da alaka da tsufa.

Yayin da wasu biran jinsinsa wadanda ba su kai shi shekaru ba suke kamuwa da cutuka suke mutuwa, shi kuwa kusan ba ya tsufa.

A shekara 20 da aka gudanar da gwajin a kan wadannan birrai kashi 13 cikin dari ne daga cikinsu kawai suka mutu a sanadiyyar abubuwan da suka shafi tsufa.

Su kuwa birran da ba a dora su a wannan tsarin ba kashi 37 cikin dari ne suka mutu, kusan linki uku kenan na wadancan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bai kamata a ce rayuwar tsofaffi ta fama da cutuka da rashin lafiya ba ce

To sai dai Anderson ta ce, idan har za a iya jinkirta tsufa, to kenan duk cutukan da ke da alaka da tsufan za su iya bin sahu, to amma tunkarar kowace cuta daya a lokaci daya ba zai iya kara tsawon rayuwar mutum ba, domin dai mutum zai iya mutuwa a sanadiyyar wani abin daban.

Misali idan ka yi maganin cutar daji gaba daya, hakan ba yana nufin ka yi maganin mutuwa a sanadiyyar cutar bugun zuciya ba ko cutar sukari ko cutar kwakwalwa ta mantuwa ba.

To amma a daya bangaren idan ka yi maganin tsufa hakan zai kasance ka yi maganin dukkanin sauran matsalolin (cutuka) a lokaci daya.

Ko da yake tsarin na rage yawan abincin da muke ci da kashi 30 cikin dari , ba shi da wani cikakken bayani amma dai a yanzu shi ne mafi tasiri wajen inganta lafiya. Bugu da kari ba kamar tsarin amfani da magunguna ba wajen neman inganta lafiya, shi wannan tsari ba shi da matsalar illar magunguna a jiki in ji Roberts.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The secret to a long and healthy life? Eat less