Ka san rubutu na sa ciwo saurin warkewa?

Rubutu a kan damuwa Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Bincike ya nuna cewa idan mutum ya yi rubutu kan damuwarsa na rage yawan lokacin da yake ziyarar likita

Shin idan mutum ya yi rubutu a kan wani rashin lafiya ko wani rauni ko matsala da ke damunsa, hakan zai iya taimaka masa ya samu sauki?

BBC ta gudanar da bincike a kan hakan. Ga abin da Claudia Hammond ta gano.

A shekarar 1986 James Pennebaker, farfesa a fannin tunanin dan adam ya gano wani gagarumin abu a fannin ilimi, wanda zai iya tayar da masu bincike na nan gaba tsaye domin su gudanar da daruruwan nazari ko bincike.

Malamin ya bukaci dalibansa su dauki minti 15 suna rubutu a kan babban raunin da suka taba ji, in kuma ba su da wannan, to su yi rubutu a kan mawuyacin halin da suka taba shiga.

An bukace su da su saki jiki su rubutu komai, dangane da lamarin ko da kuwa ba su taba fada wa kowa abin ba a baya. Haka farfesa ya sa su suka rika yi tsawon kwana hudu suna yin abu daya. Wannan ba abu ne mai sauki ba.

Pennebaker ya gaya min cewa kusan dalibai 20 sukan karke da kuka idan suna rubutun saboda tunanin abin da ya faru da su, amma kuma idan an tambaye su ko za su iya ci gaba da rubutun, a ko da yaushe suna ci gaba da rubutun.

A daya bangaren kuma sai aka ware wasu daliban aka sa su su yi rubutu a kan wani abin na daban, ba mai tayar da hankali ba, kamar wata bishiya ko dakin kwanansu na makaranta.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Rubutu a kan abin da ke damun mutum na sa ciwonsa ya warke da wuri

Daga nan sai malamin jami'ar ya jira wata shida yana sa ido kan yadda daliban suke zuwa asibiti (sau nawa suke zuwa). Ranar da ya ga sakamakon, daga nan ya fita daga dakin binciken, ya je wurin wani abokinsa da yake jiransa a cikin mota ya gaya masa babban abin da ya gano.

Abin da ya gano shi ne, daliban da suka yi rubutu a kan wannan sirri nasu, na abin da yake damunsu a rai, sun rage zuwa wurin likita a cikin watannin da suka biyo baya.

Tun daga wannan lokacin ne aka fara zurfafa nazari a kan alakar abin da a yanzu aka bayyana rubutun bayyana halin da mutum yake ciki, da kuma garkuwar jiki.

Nazarce-nazarcen da suka biyo baya, sun duba irin tasirin da irin wannan rubutu ke yi a kan komai kama daga cutar matsalar numfashi (asthma), zuwa cutar daji ta nono, zuwa ciwon kai na bari daya da sauransu.

A wani dan karamin nazari da aka yi a Kansas, an gano cewa mata masu cutar daji ta mama sun rage zuwa wajen likita saboda larurarsu ta ragu ta cutar watanni, bayan da suka yi irin wannan rubutu na bayyana abin da ke damunsu.

Ko da yake ba a ko da yaushe ba ne wannan sakamako yake kasancewa, amma dai a mafi yawan lokaci yana tabbata musamman a kan abin da ya shafi warkewar rauni.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Ka yi tunani kawai a kan abin da ke damunka ka yi rubuta a kai zai iya taimaka wa lafiyarka

To me zai sa a ce rubutu kawai a takarda zai sa mutum ya samu saukin rauni ko abin da yake damunsa? Da farko an dauka irin abun nan ne na cewa idan mutum ya furta damuwarsa sai wannan damuwar ta ragu, kamar wanda wani abu ya dame shi yake kuka, idan ya yi wannan kuka sai damuwar ta ragu ko ma ya samu waraka.

To amma sai Pennebaker ya fara da nazarin irin kalmomin da mutane suke amfani da su a rubutun nasu.

Malamin ya gano cewa irin kalmomin da mutane suke amfani da su, sun sauya a cikin lokutan nan hudu da suka rika yin rubutun, su yi su kara yi.

Wadanda ciwon nasu ya yi saurin warkewa sun fara amfani da kalmar ''Ni'' da yawa, amma a zagaye na gaba sai suka koma amfani da kalmar ''shi'' ko ''ita'' abin da ke nuna suna kallon matsalar daga wani bangare.

Haka kuma sun rika amfani da kalmomi kamar ''saboda'' abin da ke nuna sun fara fahimtar abin da ke nufin sun fara ankara da abin da suke yi, saboda haka sai suke gabatar da shi kamar a matsayin labari.

Daga nan ne sai Pennebaker ya fahimci cewa kawai rubuta abin da ke damunka kamar kana bayar da labari, hakan yana tasiri a garkuwar jikinka.

Bayan ranar farko ta rubutun yawancin mutane sun ce tuno musu baya ya sa sun ma fi jin zafin abin fiye da yadda suka ji da farko.

To wannan damuwa na sa jikin mutum ya rika samar da kwayoyin halitta na yaye damuwa ta dan lokaci kenan, wanda hakan kenan yake kara karfafa garkuwar jikin?

Ko kuma samun sauki ko raguwar damuwar ne bayan rubutun na kwanaki hakan ke kawo wa mutum amfanin garkuwar jiki? Ya zuwa yanzu dai ba wanda ya san komai a kai.

Rubutu a kan abin da ke damunka ba wai yana kara karfin garkuwar jikinka ba ne har abada, domin idan mutumin da ya amfana da wannan abu, ya sake jin rauni bayan 'yan watanni bayan nazarin farko, za a ga ciwon bai riga na wasu saurin warkewa ba.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Rubutun zai iya tasiri bayan an ji maka raunin, kamar bayan an yi maka tiyata

Yanzu kuma wani sabon bincike da aka yi a New Zealand ya nuna cewa ba lalle ba ne ka yi rubutun kafin ka ji raunin. Ko da daga baya ne ka yi rubutun tsarin zai yi aiki.

Wannan na nufin kenan mai yuwuwa wannan rubutu da kake yi kan abin da ke damunka, ba wai sai kawai za a yi maka tiyata ba, ko da a rauni da mutum kan iya ji na yau da kullum zai iya yin aiki, wato dai mutum zai ji sauki da wuri.

Ko ma dai mene ne yake sanadin wannan sauki na ciwo ko damuwa, duk da shekarun da aka yi aka kuma tabbatar yana aiki, ba kasafai ake amfani da tsarin ba a asibitoci.

Haka kuma an gano cewa tsarin yana tasiri ne a jikin wasu fiye da wasu mutanen, amma kuma duka ya dogara ne ga yadda suka rungume shi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The puzzling way that writing heals the body