Me ya sa mutane da birai da beraye ke jin dadin cakulkuli?

Wata mata na yi wa biri cakulkuli Hakkin mallakar hoto Cyril Ruoso/naturepl.com
Image caption Yadda biri ke yi (dariya) idan an yi masa cakulkuli na nuna irin kusancin da yake da shi na halitta da dan'adam

A haka idan ka kalli abin sai ka ga cakulkuli ba shi da wata ma'ana. Amma kuma sai ka ga yana sa mutane da yawa da wasu dabbobin dariya sosai. Josh Gabbatiss ya yi wa BBC nazari

Cakulkuli na daya daga cikin fagen da ke da fadi da kuma zurfi a kimiyya. Kamar yadda Robert Provine, na Jami'ar Maryland a Baltimore ya bayyana.

Malamin jami'ar ya yi nazari a kan dabi'u da dama wadanda ke da ban mamaki ko kuma wadanda babu fahinta sosai ko wata masaniya a kansu, kamar su shakuwa da hamma da tusa, to me ya sa cakulkuli ya zama daban?

Cakulkuli ya wuce duk yadda kake tsammani ko tunani in ji masanin. Ya ce abu ne da ya shafi komai daga kariya ko garkuwar jiki da tsarin sadar da sako na jiki da sauransu.

Kamar dai a kan sauran wasu dabi'un na adam masu wuyar fahimta, nazari a kan birrai ka iya taimaka mana mu fahimci yadda cakulkuli yake.

Hakkin mallakar hoto Enrique López-Tapia/naturepl.com
Image caption Dariya na da ma'ana da yawa

Akwai cakulkuli da kuma tafiyar-tsutsa (yaburbura), kuma kowanne da yanayin yadda yake.

Da farko a kawai yaburbura (tafiyar tsutsa) wadda za a rika yi maka da yatsu ana bin jikinka a hankali kamar wani abu na tafiya a jikin naka, wanda kuma za ka ji tafiyar na ratsa maka jikin ko'ina.

Provine ya ce yana ganin wannan kusan yanayi ne na yadda kadangare da sauran kwari da ma kusan duk halitta ke kare jikinsu daga wata barazana, wato ta yadda idan aka taba jikin naka sai ko 'ina a jikin ya ji ya san ga wani abu nan ya hau jikin domin ya shirya samar da kariya ko yakar wannan barazana.

Misalin yadda suke kawar da wannan barazana ko farmaki shi ne yadda za ka ga, sun yi susa ko sun karkada kunne duka wannan yana daga cikin irin wannan cakulkuli.

Sai kuma cakulkuli irin na mutane da sauran dabbobi masu shayar da nono, wadanda su kadai suke da wannan. Shi wannan yana sa dariya, kuma yana da alaka da wasa, wanda abu ne da ya kebantu da dan'adam da dabbobi masu shayarwa kawai.

Hakkin mallakar hoto Panther Media GmbH/Alamy
Image caption Yawancin mutane suna jin yaburbura (tafiyar-tsutsa)

A haka za a dauka cakulkuli abu ne da ya shafi jijiyoyin jikin mutum wadanda ke da alaka da tabawa da kuma ciwo. To amma abin ya wuce haka, domin cakulkulin da yake sa dariya kamar wata hanya ce ta wasa ko raha tsakanin mutane ko halittun da suke yi.

Kuma wasa ne na ban dariya wanda shi kadai ne za ka iya yi wa yara (na mutum) da 'ya'yan biri. Marina Davila-Ross ta Jami'ar Portsmouth a Birtaniya za ta tabbatar da haka saboda tana da masaniya sosai a kan yadda birrai da jarirai ke kyalkyala dariya idan ana musu cakulkuli.

Hakkin mallakar hoto Oleksiy Maksymenko/Alamy
Image caption Yaburbura (tafiyar-tsutsa) na sa nishadi sosai

Yadda ta ware wasu masu kula da gidan namun daji ta sa suka rika yi wa jariran birai cakulkuli, da kuma wasu uwaye (mutane) su kuma ta sa su suka rika yi wa jariransu cakulkulin ta yi nazari kan dangantakar da ke tsakanin dariya a wurin mutane da kuma birrai.

Daga nan ne a nazarin da ta wallafa a 2009 ta tabbatar da cewa dariyar da mutum ke yi ta samo asali ne daga yanayin tsarin magana na jiki wanda ya samo asali daga kakannin da mutum ya hada da birrai (wato asalin mutum). Wannan bincike ya bi diddigin asalin ba wai dariya ba kadai har ma da cakulkuli.

Kafin ka ga biri a ce yana dariya, yana bukatar ya yi wasa da abokansa ko 'yan uwansa. Kuma cakulkuli na daga wasan da 'ya'yan birrai suka saba yi, haka su ma mutane. Wannan irin wasan shi ne ke sa mutum ma ya rasa a bin da zai yi, wanda hakan kuma sai ya sa a kasa yin komai (numfashi), wannan kasa yin komai din shi ne yake haifar da dariya.

Hakkin mallakar hoto Georgette Douwma/naturepl.com
Image caption Dan kurmau yana yi wa kifi cakulkuli

''Wannan kara na 'ha-ha' na dariya shi ne nake kira ainahin karar da ake yi lokacin da numfashi ya yi wuya a iya yi , sakamakon wasan banza. Idan ka yi wa gwaggwan biri cakulkuli, za ka ji dariyarsa kamar huci,'' in ji Provine. Wannan alama ce da gwaggwan biri ke nuna cewa 'wannan wasa ne, ba wai fada ba ne.'

Chakulkuli a wurin dabbobi irin su birrai wata hanya ce ta kara dankon zumunta ko abokantaka. Duk da cewa dariyar mutum ta fi fita sosai fiye da ta birrai, ta nan Provine yake ganin ta samo asali.

Hakkin mallakar hoto Theo Webb/naturepl.com
Image caption Wata biranya tana yi wa danta cakulkuli

Duk da cewa cakulkuli da dariya ba su ne abin da yawancin masu gudanar da binciken kimiyya suka sanya a gaba ba, wasu nazarce-nazarce sun nuna akwai wasu dabbobi masu shayarwa (kare, giwa) da su ma suke da wannan alaka ta yin abin da za a iya bayyanawa a matsayin kamar cakulkuli da dariya.

Sai dai ba abu ne mai sauki ba a ce an gudanar da wani nazari da za a tabbatar da cewa wadannan abubuwan da sauran dabbobin suke yi daidai suke da cakulkulin da muke yi da kuma dariyar, saboda hadarin yin hakan, in ji Provine.

Ta hanyar fahimtar farin cikin dabbobi za mu iya inganta rayuwarsu, musamman ma idan muna tsare da su. To amma bayan wannan, babban abin koyo daga bincike a kan cakulkuli, shi ne cewa dabbobi wasu irin halittu ne masu wuyar sha'ani, wadanda su ma za su iya yin wasu dabi'u kamar namu.

Saboda haka fahimtar wannan zai iya nuna mana dangantakarmu da su, da kuma nuna muhimmancin zama mutum. Most people are ticklish to some extent (Credit: Panther Media GmbH/Alamy)

Idan kana son karanta wannan labarin na Ingilishi latsa nan Why humans, chimpanzees and rats enjoy being tickled