Wa ya san dalilan da ke sa kare birgima a cikin kashi mai wari ?

Kare na birgima a kashi Hakkin mallakar hoto Jane Burton/naturepl.com
Image caption Me ya sa kare yake yin wanka a cikin kashi?

Me zai sa a ce wata dabba kamar kare da wasu makamantansa birgima a cikin kashi ko kan wani mushe mai wari wanda zai sa a yi saurin ji ko ganin karen da ya zo wuri?

Richard Gray ya yi wa BBC nazari

Gari ya waye rana ta fara dagawa, sai kukan kwari da tsuntsaye kake ji, abin gwanin sha'awa wannan yanayi na hantsi. Can a gefe daya kuma dan karenka yana ta tsalle-tsalle nan na can yana wasa.

Ya shinshina nan ya shinshina can, sai kawai ka ga ya tsaya ya kwanta yana birgima a kan ciyawar kamar yana wanka, bayan dan lokaci sai ya taso da gudu ya dawo wurinka.

Kana dukawa ta shafa shi sai kawai ka ji wani wari ya bugi hancinka. Ashe a cikin kashi karen ya je ya yi wannan wanka ko birgima.

Wannan wani abu ne da yawanci masu karnuka suke ganin karnukan nasu suna yi a lokacin da suke tattaki da su. Abin tambaya a nan shi ne me ya sa karnuka suke matukar sha'awar birgima a cikin kashin wata dabba?

Kare da sauran dabbobi danginsa (kyarkeci da kura), dabbobi ne da suke da baiwar jin kanshi ko wari akalla linki dubu a kan yadda mutum ke iya jin wari ko kanshin abu in ji Simon Gadbois, kwararre a kan halayyar dabbobi da jin kanshi ko wari a Jami'ar Dalhousie da ke Halifax, a Nova Scotia.

Ya ce; ''abin mamaki ne matuka yadda wadannan dabbobi suke son wanka da kashi ko wani abu mai warin da ni kaina ba na iya jure masa.''

Gadbois wanda ya yi nazari a kan kuraye da kerkeci da dila a Canada ya kuma yi amfani da karen gida wajen gano wasu dabbobin a dawa.

Za ka ga a duk lokacin da suka tafi dawa, daya daga cikin karnukansa masu jin kanshi ko wari sosai, wadda yake kira Zyla, tana son yin birgima a cikin kashin wata dabba mai kama da gafiya wadda kashinta yake da doyi sosai. Kuma idan karyarnan ta yi wanka da kashin nan sai ta yi makonni tana warinsa.

Gadbois ya ce shi bai san dalilin da ya sa wannan karya take son yin haka ba. Za ka dauka tanayin hakan ne kila domin ta fi jin kanshi ko wari na yadda za ta gano dabbobin nen da muke zuwa farauta, amma kuma sai ka ga ko kusa hakan bai kara mata wani kwazo kan hakan ba.

Tun kusan shekara 15,000 da ta wuce dan'adam ya mayar da kare ya zama dabbar gida daga daji, kuma tun lokacin mutum yake rayuwa tare da shi. Wanda za ka yi tunanin cewa akwai tarin nazarce-nazarce da aka yi a kan dabi'unsa, amma abin mamaki babu wani bincike da aka taba yi a kan abin da ya sa kare yake son birgima a cikin kashin wasu dabbobi.

Hakkin mallakar hoto Petra Wegner/naturepl.com
Image caption Kare na son birgima musamman a cikin kashi mai doyi

An mika wannan tambaya ga masu ziyarar wasu shafukan BBC na Ingilishi kan ko za su iya bayar da bayani kan dalilin wannan dabi'a mai ban takaici ta karnuka da danginsu, inda suke wanka da kashin dabbobi ko mushen kifi ko na wata dabba wanda kuma yake wari ko ma doyi.

Yawancin amsar da jama'a suka bayar ita ce suna ganin dabi'a ce da karen da sauran dabbobin suka yi gado tun suna rayuwarsu ta daji, kafin mutum ya dawo da su gida.

Misali Vesa Valenius da James Turner dukkaninsu suna ganin kare ya yi gadon wannan dabi'a ne daga dila, wadda dabbar dawa ce dangin kare wadda kuma take wanka da kashi domin ta batar da warinta lokacin da take kokarin kama wata dabbar.

Wannan haka yake dila na birgima a cikin kashin wasu dabbobin ko ma mushen dabbobi. Amma daya daga cikin kadan daga binciken da ake da su a kan wannan dabi'a, da aka wallafa a 1986 ya bayar da sakamako ne mai ban mamaki.

Masana sun gudanar da nazari a kan wannan dabi'a a kan wasu rukunan dila guda biyu da ke gidan namun daji, inda aka ajiye abubuwa daban-daban masu wari iri-iri.

Abin mamaki sai aka ga wadannan dila ba su damu su yi wannan birgima a cikin kashin dabbobi masu cin ciyawa ba, kamar tinkiya ko doki. Haka kuma abinci mai wari ma bai ja hankalinsu sun yi birgima a cikinsa ba.

Abin da ya ja hankalinsu shi ne wari ko kanshin da ba na gangariya ba, kamar na turare ko bakin mai na mota. Saboda haka ne sai abin ya zama da mamaki a ce dabba ta zabi ta yi amfani da warin wani abu da ba shi da alaka da muhallinta, domin ta boye warin jikinta saboda ta kama wata dabba da take ci.

Hakkin mallakar hoto Robin Chittenden/naturepl.com
Image caption Kashin dila

Masu binciken sun kuma gano cewa wadannan dila-dila suna son warin kashin wasu dabbobin masu cin ciyawa kamar wani jinsin damisa ko zaki mai cin ciyawa (cougars) da kuma bakin tunku (black bear).

A ci gaba da binciken an kuma gano cewa dila kan yi birgima a kan kashin wasu dabbobin na dawa wadanda su kuma suke farautar dila. A kan haka ne aka kawar da waccan fahimta ta cewa dila na birgima a kashi ne domin boye wari ko kanta daga kananan dabbobi da take farauta.

Bayan haka ma kuma wani binciken ya nuna cewa a yawancin lokaci dila yana bin dabbar da zai kama ne ya kure mata gudu, amma ba yin kwantan-bauna ba, don haka ba ya bukatar a ce yana boye warinsa domin ya samu damar farautar abincinsa.

Hakkin mallakar hoto Angelo Gandolfi/naturepl.com
Image caption Kerkeci na goga jikinsa a jikin wani mushe

Samantha Harrison na daga wadanda ke ganin wannan dabi'a ta dibar wari na iya kasancewa wata dabara ta batar da sawu ko boye kai da dabbobin ke yi.

Za a iya cewa sakamakon binciken da aka yi wanda aka wallafa a 2016 na Max Allen na Jami'ar Wisconsin a Madison ya mara baya ga wannan tunanin.

A nazarin da ya yi bayan da ya sanya wata kyamara a wani daji na yankin Santa Cruz a California, wadda ta rika daukar hoton abubuwan da wasu dila suke yi ya ga yadda wadannan dila suke yawan ziyarar inda mazan zakuna ko damisa suka yi fitsari, sai a ga dila na goga kumatunsa a inda aka yi fitsarin.

Allen na ganin dilan na yin haka ne domin ya samu warin da zai kare kansa daga wasu dabbobin manya masu farautarsa, domin kada su ji warinsa su san inda yake. Masanin na ganin idan dila ya debi warin wannan fitsari na zaki ko damisa, wadannan sauran dabbobi da suka fi karfinsa za su ji warin zaki ko damisa wanda hakan zai ba su tsoro, kuma kafin su gane yaudara ce, dilan ya samu ya gudu.

Ba shakka wannan wani bayani ne mai kyau, amma kuma ba ta bayyana dalilin da ya sa manyan dabbobi kamar dila ko kerkeci su ma suke goga jikinsu a fitsarin da wasu manyan dabbobin suka yi ba, domin daukar warin.

Hakkin mallakar hoto Patricio Robles Gil/naturepl.com
Image caption Dila na daya daga cikin dabbobin dawa da ke birgima a kan kashi ko mushe

To shi kuwa Stephen Harris na Jami'ar Bristol ta Birtaniya wanda ya yi nazari a kan dila, bai yarda da wannan fahimta ba ta cewa dila na amfani da warin fitsarin zaki ko damisa domin ya boye kansa daga wasu manyan dabbobin da ke farautarsa. Maimakon haka yana ganin dilan na yin haka ne domin shi ma ya sa warinsa a wurin.

Haka shi ma Pietr Maynard ta Facebook ya gaya mana cewa yana ganin karensa na yin haka ne domin yarufe warin da yake wannan wurin, domin ya sheda wa sauran karnuka cewa a shirye yake ya kare wannan yanki a matsayi nasa.

To amma shi kansa wannan bayanin ma ana ganin yana da rauni , domin kare ba a kuncinsa kadai yake goga warin ba, jikinsa kusan gaba daya yake goga wa.

Kamar yadda Philippa Baines ta gaya mana yadda karenta Holly yake birgimar wanka a cikin kashin shanu.

Goodmann na da wata fahimtar, ita tana ganin, kila wata hanya ce da dila ko kare ke nuna wa sauran 'yan uwansa inda ya je.

Marigayi abokin aikinta shi ma masani kan dila, Erich Klinghammer yana ganin dabi'ar wata hanya ce ta gaya wa dangi game da wani abinci mai dadi da dilan ya ci lokacin da ya je yawo.

A wani gwaji da ta yi Goodmann ta gano cewa a duk lokacin da suka samu wani nama, dila ko danginsa yakan yi birgima a kan naman kafin ya ci. Saboda haka tana ganin yana yin hakan ne domin ya gaya wa 'yan uwansa ta yadda za su bi wannan warin da ke jikinsa su je wurin naman.

Ita ma kura an ga tana yin birgima a kan mushe, kuma idan ta yi hakan tana jan hankalin 'yan uwanta. Haka kuma wani nazari da aka yi a kan dila a Ethiopia, an ga yana birgima a kasa bayan ya ci abinci, ko da yake anga suna yin birgimar ma ko wanka a cikin kashin mutum, ko kuma inda mutane suka zauna.

Hakkin mallakar hoto Roland Seitre/naturepl.com)
Image caption Kerkeci ma na jin dadin birgima a cikin abu mai wari

Sai dai kuma Gadbois na ganin kila dai wannan wata hanya ce ta tabbatar da 'yan uwantaka, kamar yadda ya yi nazari a kan garken dila a Canada, inda ya ga jagora a garken ne ke fara birgima a kan abin me wari, daga baya kuma sauran suma su bi baya. A nan ana ganin sun yi haka ne domin garken ya zama suna wari iri daya, domin tabbatar da 'yan uwantaka.

Wannan tunanin shi ne ma ake gani yake tattare da jinsin karen dawa na Afirka, inda mace take birgima a kan fitsarin namiji wanda yake daga wani garken da take son ta shiga cikin garken.

Akwai kuma wadansu bayanan daban-daban da ake gani sune dalilin wannan dabi'a ta kare da sauran dangoginsa.

Robert Reppy da Krystal Parks na ganin kamar yadda Micheal Fox masani a kan halayyar dabbobi a littafinsa Dog Body, Dog Mind, ya ce, kamar yadda mu mutane muke sa turare haka su ma dabbobin suke wanka a cikin abu mai wari domin ya zamar musu kamar turare domin kawar da warin jikinsu.

Hakkin mallakar hoto Christophe Courteau/naturepl.com
Image caption Karen daji na Afirka

A karshe dai Gadbois na ganin dabi'a ce kawai da dabbobin suka yi gado tun daga iyaye da kakanni, wadda take da wani amfani a lokacin kila, amma kuma yanzu wannan amfani ya kau, kuma duk da haka suka ci gaba da yinta.

Hakkin mallakar hoto Ulrike Schanz/naturepl.com
Image caption Wasu na ganin wanka da kare ke yi a cikin kashi gado ne na kaka da kakanninsa

Wanna shi ne ya kara dawo da mu kan maganar cewa a gaskiya dai ba mu da wata masaniya kan wannan dabi'a ta wanka a cikin kashin dabbobi mai wari ko kuma wani mushe da kare da danginsa ke yi. Wari dai kawai wani muhimmin abu ne na rayuwarsu wanda ba mu san alakarsu da shi ba.