Me ya sa susa take da daɗi?

Biri na yi wa biri susa Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Biri ma na jin dadin susa sosai

Ko yaya muka ji wani ɗan ƙaiƙayi a jikinmu sai mu ɗan sosa domin mu ji daɗi. Idan ƙaiƙayin ya ci gaba mukan yi ta susar domin jin wannan kaikayi ya dena. To me ya sa farce ke raba mu da ƙaiƙayin nan da nan, har mu ji daɗi?

Jason G Goldman ya bincika

J R Traver ta fara susar jikinta tun tana 'yar shekara 40, kuma za ta ci gaba da sosa jikin nata har zuwa karshen rayuwarta na wasu shekaru 40 din. Matar wadda kwararriya ce a kan namun daji tana ganin cewa ita da wasu danginta mata biyu suna da wasu 'yan mitsi-mitsin kwari ne a jikin fatarsu.

Bayan shekara 17 tana fafutukar ganin bayan wadannan 'yan mitsi-mitsin halittu daga jikinta, masaniyar kimiyyar ta rubuta wata kasida a kan wannan matsala ta jikin nata a wata mujalla ta abubuwan da suka shafi lafiyar fata ta Washington, ga alama domin ta samu wanda zai taimaka mata kan matsalar.

Domin neman maganin matsalar ta ziyarci likitoci na fannin jiki daban-daban da sauransu. Har ma kuma ta yi ta amfani da wasu magungunan kwari masu hadari akai akai domin kashe kwarin.

Ta rika amfani da farcenta tana kwarzane fatarta tana fitar da 'yan mitsi-mitshin kwarin daga jikinta, abin da ya sa har ta rika ji ma kanta ciwo.

Wani likitan ma har shawara ya ba ta kan a duba yanayin tunaninta, amma ta tabbatar masa cewa matsalar tata ba ta bukatar wannan aiki nasa.

Matar ta rubuta cewa, ''har zuwa yau, ba wani magani da ya kawo min karshen wannan larura.''

To a yanzu dai mun gano cewa Traver da 'yan uwanta biyun nan, ba su da wasu kwari ko kananan halittu a jikin fatarsu da ke sanya musu wannan kaikayi, duk tsawon shekara 40. Tana dai fama da wata larura ce ta kwakwalwa, wadda ke sa mutum ya rika ji kamar ga wani abu a jikinsa da yake iya gani, wanda ke sa masa wannan kaikayi.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Susa kila wata hanya ce ta yaki da wasu kwari a jikinmu

Shi dai kaikayi gaba daya abu ne da kusan kullum kowane mutum a duniyar nan ya kan ji shi, wanda kuma ba wanda zai iya ce maka lalle ga yadda yake ko menene shi.

Fassarar da yawancin likitoci da masu bincike suke amfani da ita ta kaikayi, tun shekara 350 wani likita dan kasar Jamus, Samuel Hafenreffer ya yi ta.

Likitan ya rubuta cewa, ''duk wani abu da zai sa ka sosa jikinka ( kana sane ko ba ka sani ba), shi ne kaikayi.'' Wannan fassara ce da za a iya dogara da ita, amma watakila ba za a iya cewa mai amfani ba ce sosai.

Da farko idan ka duba za ka ga kaikayi da ciwo kusan suna da alaka. Ita dai fata tana tattare da karshen jijiyoyi ne, wadanda aikinsu shi ne su sanar da laka da kwakwalwa ( jiki ) idan wani abu mai cutarwa ya zo jiki ko kusa da jikin mutum.

Karamin hari shi ne yake zama kaikayi, wanda kuma yake da girma shi ne jiki yake jin ciwo, wannan kamar yadda wata nazariyya (intensity theory) ta bayyana kenan.

Wata nazariyyar (specificity) kuwa, tana ganin lamarin ba haka yake ba, domin a ganin masu wannan ra'ayi, kowanne tsakanin kaikayi da ciwo, yana da jijiyoyin da suke sanar da jiki a game da shi.

Yawan Susa

Shi dai kaikayi abubuwa daban-daban ne ke haddasa shi. Akwai dan kaikayi irin wanda yawancinmu muka saba da shi, kamar na cizon wani kwaro. Akwai kuma mai tsanani, wanda ke samun mutum a dalilin wasu cutuka na fata. Wasu cutukan na cikin jiki kamar na koda da kanjamau da sauransu su ma ana ganin suna haddasa wa mutum tsananin kaikayi.

Akwai kuma abubuwan da suka shafi matsalar kwakwalwa ko tunani da ke sa mutum kaikayi, amma kuma ba su kai, matsalar da ke sa mutum ya rika jin tunanin bukatar sosa jikinsa ba haka kawai.

Samun kai a cikin irin wannan yanayin na yawan sosa jiki ka iya illa ga fata, kuma yawan susar zai iya kara matsalar ne.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Kusan kowa a duniyar nan kullum sai ya ji ƙaiƙayi a jikinsa, amma ba mu san dalili ba

Susa wani dan karamin ciwo ne, amma dan ciwon da muke ji idan mun karta farcenmu a jikin fatarmu wato mun yi wannan susa, hakan na taimaka mana mu daina jin kaikayi, kamar yadda sanya zafi ko sanyi ko wani magani (mai sinadarin da ake samu a jikin barkono), ko ma birbishin lantarki zai yi mana maganin kaikayin.

Wannan na nufin kenan magungunan da ake amfani da su domin rage ciwo, a zahiri suna sa kaikayi kenan. Duk da rudanin da ke tsakanin ciwo da kaikayi akwai bambanci na zahiri tsakanin abubuwan biyu.

Idan abu ciwo ne, to jikinmu yana mayar da martani ne ta hanyar janyewa daga abin. Misali ka sa hannunka a wurin wuta, za ka ji jikinka yana ta so ka janye.

Shi kuwa kaikayi yana sa mutum ya kai hankalinsa ne wurin da kaikayin yake, maimakon gudunsa. Kula da wurin da kuma sosa shi ya fi amfani wajen cire kwaron da ya hau maka jiki a kan wancan tsarin jikin na gujewa abu.

Kamar hamma shi ma kaikayi kan iya yaduwa tsakanin mutane

Ga yadda abin ke faruwa : Idan wani abu ya damu fatarka misali cizon sauro, sai kwayoyin halittar wurin su saki wani sinadari. Sakin wanan sinadari, shi ke sa jijiyoyin kai sako da ke jikin fata su sanar da lakar mutum, wadda ita kuma daga nan sai ta sanar da kwakwalwa game da wannan abu da ke damunka a fata, kai kuma sai ka sosa wurin.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Zafin susa daban yake da na wuta

Kana jin kaikayi zuwa yanzu? Idan kana ji, to ba wani abu ba ne, illa cewa, kamar hamma, shi ma kaikayi yana iya yaduwa ko kuma yana iya samunka idan kana maganarsa ko wani abu a kansa.

Likitoci suna cewa, suna jin kaikayi bayan sun yi wa masu larurar kazzuwa magani. Haka kuma wasu masu bincike sun taba gabatar da lacca a kan kaikayi, kawai domin su ga ko mutanen da suke sauraron laccar za su ji kaikayi, kuma hakan ta tabbata.

Wasu na'urorin daukar hoto da aka boye sun nuna yadda masu sauraron laccar suke susa, idan ana magana kan kaikayi fiye da yadda idan ana magana akan wani abu na daban.

An ga yadda birai suke susa idan sun ga 'yan uwansu suna susa, abin da ke nuna cewa asali akwai wani amfani da muke samu idan mun ga 'yan uwanmu suna susa.

Ita susa ma ana ganin yawanci aba ce da za a iya jin dadinta sosai, ba mai sa ciwo ba. A wata kasida ta 1984, wadda aka wallafa a mujullar lafiya ta abubuwan da suka shafi fata, wadda George Bishop, na jami'ar Washington, ya rubuta, ya ce, ''ana iya matukar jin dadin susa da karfi wadda za ta iya sa zafi, a wurin da yake kaikayi.''

Kuma duk da cewa idan wanda kake kauna ya sosa maka baya za ka ji dadi sosai, susar za ta iya zama babbar matsala a wjaen mutanen da ke fama da wata cuta mai nasaba da kaikayi.

Masu kyazbi sukan ce suna sosa jikinsu har sai sun ji susar ba dadi, ba wai sai kaikayin ya ragu ba.

''Farin ciki,'' in ji Ogden Nash, ''shi ne ka yi susa duk lokacin da ka ji wani dan kaikayi.'' Mai waken na Amurka ga alama ya fadi gaskiya fiye da yadda ya ma sani a wannan kalami nasa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why it feels so good to scratch an itch