Jima'i tsakanin macizai na da ban mamaki

Macijin ciyawa na saduwa da matarsa Hakkin mallakar hoto Sven Zacek/naturepl.com
Image caption Macijiya daya na saduwa da macizai da yawa

A da mun dauka cewa idan ana maganar yadda maciji ke jima'i namiji shi ne ke nuna iko da kwazo, mace na sallama kanta ne kawai, to amma yanzu mun gano cewa lamarin ba haka yake ba sam-sam.

Sandrine Ceurstemont ta yi wa BBC nazari

Lokacin da Jesús Rivas na Jami'ar New Mexico Highlands a Las Vegas ya daga wata kasa (macijiya) a lokacin tana cikin yanayi na jima'i domin ya duba ta, ya ga abin mamaki.

Yadda ya ga jikin maciyar ya kumbura, alama ce da ke nuna cewa ta hadiyi wani abinci ne, saboda haka sai Rivas ya jira ta, ta amayar da abin da ta hadiye.

Saboda shi maciji idan ya koshi da yawa, kuma ya sa mu kansa a cikin wata barazana sai ya amayar da abin da ya hadiye domin ya iya samun damar da zai gudu.

To amma maimakon ya ga mushen wani abu ya fito daga bakin macijiyar kamar wani bera ko wani abu sai kawai ya ga jela kamar ta maciji ta fara fitowa daga bakin kasar.

Abin da ya faru shi ne ita wannan kasa ta cinye namijin micijin da ya sadu da ita ne. Wannan abin da masanin ya gano alama ce da ke nuna irin gurguwar fahimtar da muke yi a kan yadda macizai ke jima'i.

Kafin wannan masana kimiyya sun dauka cewa matar maciji ba abin da take yi a lokacin saduwa illa ta mika kanta kawai ga namijin, sai dai yanzu an gano cewa tamatar ita ce ma take da iko fiye da namiji a lokacin.

Wannan bai zo da mamaki ba, domin macijiya ta fi maciji girman jiki da alamar karfi, saboda haka za ta iya fin karfinsa har ma ta hadiye shi. Hakan dai ya saba da yadda sauran dabbobi suke, ta yadda za ka ga maza sun fi mata girma, amma kuma hakan ya bambanta ga yawancin yadda macizai su ke.

Hakkin mallakar hoto Tony Phelps/naturepl.com
Image caption Mijin kasa da matar

A tsakanin kadangaru da tsuntsaye da dabbobi masu shayarwa, mazan da suke da girma sun fi iya kare muhallinsu tare da korar abokan neman matansu. Amma yawancin mazan macizai ba sa nuna irin wannan kishi da aka san mazaje da su.

Maimakon haka a lokacin neman matar da za su sadu da ita, sai dai kawai kowane maciji ya rika tura jelarsa yana kokarin sanya mazakutarsa a cikin matar, amma ba wai ya yi fada da abokan nema ba. Wato dai yawancin macizai ba sa kishi a wurin neman mata. Wannan zai iya kasancewa dalilin da girman miciji ba shi da wani amfani a wurinsa.

Wannan ne ya sa ake ganin kila abin da ya sa matar miciji take kasancewa babba, domin girman jiki yana da alaka da yawa ko karin haihuwa da kuma 'ya'ya masu girma, wanda hakan zai fi sa su rayu.

Wani nazari da aka yi a 2016 ya nuna cewa girman jiki zai iya kara karfin garkuwar jikin 'ya'ya. Ga alama kuma wannan yana ba maza sha'awa, domin miciji ya fi son matar da take da girma.

To sai dai kuma ba a san dalilin da ya sa mazan suke son mace mai girma ba, domin macizai ba su da wani ido mai gani sosai da sosai, saboda haka ba a san yadda miciji yake iya gane babbar mace ba daga nesa.

Hakkin mallakar hoto Franco Banfi/naturepl.com
Image caption Koriyar kasa

Kila abin da za a iya amfani da shi a nan shi ne, na cewa mata su ne suke fara neman maza, maimakon namiji ya nemi mace. Bayan da mace ta farfado daga dogon barci ko suman nan da aka san kasa na yi, sai ta yi saba ta zubar da fatarta tsohuwa, ta yi sabuwa, a wannan lokacin takan fitar da wani sinadari da kanshinsa kan jawo hankalin namiji zuwa wurinta.

Wannan wari ko kanshi yana tayar da hankalin namiji (miciji) in ji Rivas, ya sa har ya san yadda macen take, babba ce ko karama.

Wani abin da kuma muka yi wa bahaguwar fahimta game da yadda miciji ke saduwa, shi ne yanayin yadda suke yin jima'in nasu.

Hakkin mallakar hoto Franco Banfi/naturepl.com
Image caption Koriyar kasa

Kafin yanzu mun dauka cewa miciji daya yana saduwa da mata macizai da yawa ne, to amma ashe ba haka lamarin yake ba. Yawanci ashe mace daya tana iya jan hankalin macizai maza da yawa a lokaci daya, kamar yadda wani nazari da Mark O'Shea da abokan aikinsa a Jami'ar Wolverhampton a Birtaniya da suka yi a 2016 ya gano.

Hakkin mallakar hoto Tim Laman/naturepl.com
Image caption Micijin kan bishiya

Za ka iya ganin kasa ta yi likimo a cikin tabo ko saman ruwa, maza na ta yi mata kwarkwasa, inda za ka iya ganin maza kusan 12 a kusa da ita wanya ya samu damar shigarta zai iya kasanacewa da ita har tsawon wata daya a haka.

A wani wurin kamar Manitoba da ke Canada, za ka ga macijiya daya kawai za ta iya daukar hankalin macizai kusan dari daya suna ta hawan zuna, kowanne so yake ya sami matar. Matsalar saduwar ta irin wadannan macizan ita ce, ba a san wane maciji ba neyake nasarar samun saduwar; amma tun da saduwa ce ta yadda za su nade juna, dole ne macen ta zaba.

Hakkin mallakar hoto Francois Savigny/naturepl.com
Image caption Yadda kasa ke saduwa da juna

Bisa nazarinsa LeMaster ya ce a karshe dai matar macijin ce za ta bude farjinta domin saduwar, idan ta zabi wanda take ganin ya yi mata. Kuma macen tana iya tsuke farjin ya zuwa iya lokacin saduwar da take so, saboda haka idan ta ji namijin bai yi mata yadda take so ba, sai ta sake shi.

Har yanzu ba san mizanin da matar ke amfani da shi ta zabi wanda take ganin ya fi wani ba. O'shea na ganin kila wanda ya fi karfi ko ya fi kasancewa da ita shi ne wanda a karshe za ta zaba, ta yadda za ta samu 'ya'ya masu karfi.

Amma kuma ana ganin kila akwai wasu abubuwan da matar take amfani da su wajen zabar namijin. Rivas na ganin kila matar na amfani da yadda za ta taba jikin mazan ne ta bambance.

Ko ma dai ya matan suke zabar mazan, ba lalle ba ne su zabi daya ba kawai, saboda sukan yi jima'i da maza da yawa. Sai dai sabanin yadda aka fahimta a da,shi namiji yana tsayawa ne a wurin mace daya, yayin da ita kuma mace take saduwa da maza da yawa.

Rivas yana ganin maza suna bata lokaci wajen zabar mace, wanda hakan tsari ne da aka sani da yanayin da maza da yawa za su kasance da mata daya. Masanin ya ce yana ganin tsarin auren da mace ke zama da maza da yawa kila wata al'ada ce ta iyaye da kakanni ga macizai.

Ba a san dalilin da ya sa mata suke yin haka ba a tsarin saduwar macizai. Amma wani tunani da aka yi shi ne ana ganin saduwar da mazaje da yawa na ba wa mace damar tara maniyyi da yawa, wanda kuma yake zamar mata kamar abinci a jiki.

Amma kuma Rivas na ganin saduwar da maza da yawa, wata hanya ce ta yadda maniyyin da ya fi kyau zai fitar da sauran ta yadda mai kyau din zai hadu da nata ta haifi 'ya'yan da suka fi karfi da lafiya.

Macijiya za ta iya adana maniyyi a cikinta tsawon watanni ko shekaru, da haka kuma wannan maniyyin zai yi gogayya ko da da wani sabon maniyyin ne, ta yadda a karshe wanda ya fi inganci zai kawar da wanda ba shi da inganci.

To ta yaya maza suke yin nasarar samun saduwar?

Hakkin mallakar hoto Huw Cordey/naturepl.com
Image caption Tarin jan miciji

Wata macijiyar idan ta sadu da namiji takan fitar da wani wari daga jikinta wanda idan namiji ya ji ba zai bata lokacinsa ba yana nemanta. Amma wasu mazajen su ne suke kokarin hana wasu neman matar bayan sun neme ta, amma da wata dabara.

Misali shi irin wannan jinsin micijin, idan ya sadu da micijiya, sai ya sanya mata wani da zai toshe farjinta. Wannan shi ya sa idan micijin ya sadu da mata babba, sai su dade a hade, amma kuma maimakon namijin ya yi ta zuba mata maniyyi, sai ya zuba mata wannan ruwan da zai daskare ya toshe mata farji ta yadda wasu da wuya su iya saduwa da ita.

Sai dai wannan abin ba lalle ba ne ya zauna, zai iya ficewa. Amma kuma ana ganin abin yana da wani amfanin bayan toshe farjin, domin yana da tarin maniyyi a cikinsa, wanda ake ganin a hankali a hankali yana narkewa ya shiga cikin matar. Ana ganin kila wannan wata dabara ce da micijin ke yi ya yada mata maniyyinsa.

Haka kuma namiji zai iya samun kasancewa a gaba da sauran mazaje a wurin matar, idan ya kasance na karshe da ya sadu da ita. Miniyyin wanda ya sadu da ita a karshe shi ne yake kasancewa a saman sauran, kuma shi ne zai shige ta da farko. Kila wannan ne ya sa kasa ke dadewa wurin saduwa, wato idan suka kulle namiji da mace.

Rivas na ganin kila wannan dalilin ne ya sa wasu mazan sai su tsay domin su zama su ne na karshen saduwa da tamata. To amma kuma shi mijin kasa ba ya tsayawa a wuri ya dade idan ya yi jima'i saboda hakan na jefa shi cikin hadarin da matar za ta cinye shi.

Hakkin mallakar hoto Huw Cordey/naturepl.com
Image caption Tarin jan miciji

Ba ko da yaushe ba ne matar take cinye namiji, amma dai ba a san yadda take zabar namijin da za ta cinye ba, bayan saduwar. Amma ana ganin tana yin hakan ne domin bayan ta yi cikin takan yi azumin wata bakwai, wanda kila wannan hadiyar za ta kasance abincinta kenan na tsawon wannan lokaci na goyon ciki.

Wani abu kuma da maciji shi ne dabba ce da ke da sirri sosai domin 'yan kadan ne a duniya aka iya samun damar nazari kan rayuwarsu. Amma dai kusan yadda saduwarsu take ta yi kusanci da ta gizo-gizo, yadda mata sun fi maza girma.

Kuma akwai gogayya tsakanin mazaje domin saduwa da mata, su kuma matan suna da yadda suke zabar namijin da zai sadu da su. Idan kuma namiji bai yi hankali ba, matar sai ta cinye shi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Snake sex is every bit as peculiar as you would expect