Me ke sa wasunmu kwakwalar hanci?

Wani yaro na kwakwalar hanci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

manya da yara na da dabi'ar kwakwalar hanci

Ka sanya dan yatsa kana kwakwalar hancinka, abu ne mai ban haushi da kazanta wanda kuma zai iya yin illa ga lafiyar mutum, saboda haka abun takaici ne yadda mutane da yawa suke yin hakan, in ji Jason Goldman.

Yawancinmu muna yin hakan, to amma fa kadan ne daga cikinmu za su yarda cewa suna yi. Idan aka gan mu muna yi mukan ji kunya da kuma nadamar yi.

Amma kuma sai mu rika kyara ko bata rai idan muka ga wani yana yi a bainar jama'a. Wannan abu dai ba wani ba ne illa, dabi'ar nan ta kwakwalar hanci domin fitar da tasono.

To shin wai ma dai kwakwalar hancin wani abu ne da ya kai munin da muke daukarsa idan muka ga mutum yana yi?

Shin ya muninsa ko yawansa yake a tsakanin jama'a? Kuma me ya sa ma mutanen suke son lalle sai sun kwakwalo tasonon sun ga yadda yake ko ma dandanonsa yake?

Wani cikakken binciken kimiyya na farko da aka fara yi a kan wannan dabi'a an fara shi ne a nan kusa, a shekara ta 1995, inda wasu masu binciken kimiyya Amurkawa Thompson da Jefferson suka yi.

Masu binciken sun aika da wata takardar wasika ta bincike ga mutane 1,000 a garin Dane da ke Wisconsin da tambayarsu a kan dabi'ar.

Daga cikin 254 da suka amsa tambayar da ke kunshe a wasikar kashi 21 cikin dari sun amsa cewa lalle kam suna wannan dabi'a ta kwakwalar hanci, yayin da kashi 1.2 cikin dari kuma suka ce suna yi amma sau daya akalla a kowace sa'a.

Biyu daga cikin mutanen da suka amsa musu tambayar, sun nuna cewa dabi'ar ta zama jiki a wurinsu har ma tana shafar rayuwarsu ta yau da kullum.

Kuma wani abu da ya ba su mamaki, wasu mutanen biyu sun ce abin ya ratsa su sosai har ta kai sun bula 'yar fatar da ke cikin hancinsu wadda ta raba tsakanin kofofin hancin.

Asalin hoton, Thinkstock

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wannan dai ba wani cikakken bincike ba ne domin daya bisa hudu na yawan mutanen da suka tambaya ne suka ba su amsa. Amma duk da yadda mutane suke kyamar dabi'ar a al'adance aba ce da mutane da yawa ke yi.

Bayan shekaru biyar kuma wasu likitocin India Chittaranjan Andrade da BS Srihari da ke babban asibitin kula da masu tabin hankali da ke Bangalore suka yanke shawarar gudanar da wani binciken a kan dabi'ar ta kwakwalar hanci.

Sun lura cewa yawancin dabi'ar mutane ta fi yawa a tsakanin yara da matasa fiye da a kan manya.

Saboda haka suka shirya gudanar da bincikensu a tsakanin yara da matasa maimakon magidanta ko manya domin sanin yadda yawan dabi'ar yake tsakanin mutane.

Haka kuma ganin cewa da alamu binciken da wadancan likitocin Amurkan suka yi a Wisconsin ya gamu da san-rai ko rashin fadin gaskiya daga wasu mutanen da aka tambaya, sai suka yi nasu binciken a ajujuwan makarantu, inda suke ganin za su fi samun amsoshi daban-daban.

Sun mayar da hankalinsu a kan wasu makarantu hudu a Bangalore, daya ta 'ya'yan talakawa da biyu wadanda dalibansu na iyayen yara masu matsakaicin hali ne, makaranta ta hudu kuma ta 'ya'yan masu hali ce.

A gaba dayan binciken Andrade da Srihari sun tattara bayanai daga matsa 200, inda kusan dukkanninsu suka ce suna kwakwalar hanci akalla sau hudu a kowace rana

Wannan ba shi ne kadai abin da sakamakon ya bayyana ba. Abin ban sha'awar shi ne yanayin yin dabi'ar a tsakanin yaran ko matasan.

Kashi 7.6 cikin dari na daliban ne suka ce suna kwakwalar hancin nasu sama da sau 20 a duk rana, amma kusan kashi 20 cikin dari suna ganin suna fama sosai da wannan matsala.

Yawancinsu sun ce suna yinta ne domin sosa hancinsu idan yana yi musu kaikayi, ko su cire wani tasono, amma kuma 24 daga cikinsu wato kashi 12 cikin dari, sun ce suna kwakwalar hancin ne saboda suna jin dadin yin hakan.

Asalin hoton, Thinkstock

Bayanan hoto,

Manya na kwakwalar hanci

To ba da dan yatsa ake wannan dabi'a ba kadai kamar yadda daliban suka bayyana a wannan bincike.

Goma sha uku daga cikin daliban sun ce su har wani tsinke-tsinke suke amfani da shi domin kwakwalar hancin nasu, kuma tara daga cikinsu sun ce fensir suke sa wa a hancin su kwakwalo, wasu taran kuma suka ce ai su har cin tasonon da suka kwakwalo ma suke yi.

Babu wani bambanci a wannan dabi'a tsakanin 'ya'yan talakawa da masu hali dukkaninmu mun zama daya a nan.

Sai dai akwai bambanci tsakanin maza da mata, inda maza suka fi yi yayin da su kuwa mata ake ganin suna ganin kazantar abin.

Haka kuma bincike ya nuna maza na iya daukar wasu dabi'un marassa kyau kamar cin farce ko cizgar gashinsu.

Dabi'ar kwakwalar hanci ba abu ne maras kyau ba kawai domin idan abin yayi tsanani ya kan haddasa babbar matsala ga mai yi kamar yadda Andrade da Srihari suka gano lokacin da suka yi nazari.

Wani mutum da likitoci suka yi wa aikin toshe bular da ya yi a fatar da ta raba kofofin hancinsa biyu abin ya kai har kofar ta ki rufewa gaba daya saboda mutumin ya kasa barin wannan dabi'a ta kwakwalar hancin.

Haka ita ma wata mata mai shekara 53 wadda ta ke matukar kwakwalar hancin nata har ta kai da ta yi wa hancinta kofa a tsakani daga ciki.

Akwai kuma wani mutum mai shekara 29 wanda shi kuma yake yawan cizge gashin hancinsa bayan kwakwalar, lamarin da ya kai har likitoci suka kirkiri wani suna na wannan dabi'a ta shi biyu.

Asalin hoton, Thinkstock

Bayanan hoto,

Manya ma na jin dadin kwakwalar hanci

Tsananin wannan dabi'ar ta shi ta cire gashin hancin nasa ta yi tsananin har ta sa hancin nasa yake masa radadi, abin da ya sa yake amfani da wani ruwan magani domin samun saukin radadin.

Wannan ya sa har cikin hancin nasa ya sauya launi zuwa irin na ruwan maganin, inda har ba a gane gashin hancin nasa saboda wannan launi, abin da ya sa, ya sarara da cire gashin.

Likitocin da suka yi nasarar yi masa maganin wannan matsala sun bayyana dabi'ar tasa da cewa wani yanayi ne na matsalar aikin jikinsa.

Da yawa daga cikinmu ba za mu damu ba cewa dabi'armu ta kwakwalar hanci, ba lalle wata al'ada ba ce ta daban ta halayyar jikinmu.

Duk da cewa dabi'ar cin farce da ta cire gashin hanci ba abubuwa ba ne da ake dangantawa da wata matsala to amma hada dabi'un biyu a wurin mutum daya hakan wata matsala cekamar yadda likitoci ke gani.

Amma kuma hakan ba yana nufin su masu kwakwalar hanci kadai ba sa fuskantar wani hadari ba, domin a 2006 wasu masu bincike na kasar Holland sun gano cewa kwakwalar hanci ka iya samar da wurin da kwayoyin cuta za su tare a hancin mutum, kamar yadda suka gano a wani asibiti.

To idan aka yi la'akari da dukkanin haduran da ke tattare da wannan dabi'a ta kwakwalar hanci da kuma yadda take bata wa mutane rai idan suka ga wani na yi, to sai mu ce, wai me yasa muke kwakwalar hancin ne?

Babu dai wata cikakkiyar amsa akan wannan tambaya, amma kamar yadda Tom Stafford ya rubuta a baya bayan nan akan dabi'ar cin farce, ya ce, ''watakila muna yin hakan ne saboda jin dadin da muke yi idan mun gyara jikinmu,

da kuma cewa hanci yana kusa a duk lokacin da muka bukaci taba shi.''

Ko kuma dai, kwakwalar hanci wata alama ce ta lalaci.Domin ko ba komai a ko da yaushe muna da isassun yatsun da za ka yi amfani da su ka gyara hancinka idan kana jin bukatar hakan.Wanda hakan ya fi yadda za a ce mutum

yana da takaradar nan mai laushi ta face majina ko gyara hanci.

Abu ne mai kyau ganin yadda har yanzu wasu masu bincike suke kokarin gano dalilan da ke sa muke kwakwalar hancinmu da kuma illolin hakan.

A shekara ta 2001 likitocin Indiyan nan Andrade da Srihari sun samu kyautar lambar yabo ta Nobel akan binciken da suka yi, wadda kyauta ce da ake ba wa wadanda suka yi wani bincike da ke sa mutane dariya kafin daga bisani ya sa mutane tunani.

A wurin bikin ba su lambar yabon, Andrade ya yi wata magana, inda ya ke cewa,'' wasu mutane suna cusa hancinsu cikin harkokin wasu mutanen. Ni kuma na dauki dabi'ar shigar da harkokina cikin hancin mutane.''

Likitan ya yi amfani da salon magana na Turanci ne da ke amfani da kalmar hanci wato nose da cusawa wato poke da ke nufin, shiga sharo ba shanu ta Poke nose, ta yadda zai bayar da wata ma'ana ta ban dariya da shi yake nufi.Idan kana son karanta wannan a harshen Inglishi latsa nan Why do we pick our nose?