Yadda na yi kokarin hana kaina wata dabi'a da azabar wutar lantarki

Amfani da waya a gado Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Fatana shi ne na daina amfani da waya idan na kwanta

Kokarin hana kaina wata dabi'a da wutar lantarki ya ci tura. Ko sanya wa jikinka wutar lantarki ta ja ka ko kuma biyan wata 'yar tara idan ka kauce hanya daga wani abu da kake yi ka nemi shiga wani, hakan zai iya kyautata rayuwarka?

Domin kaucewa dabi'arta ta amfani da waya a gado Tiffanie Wen ta jarraba ta gani.

Domin ganin ta rabu da dabi'ar amfani da wayarta a lokacin da za ta kwanta barci, Teffanie Wen ta jarraba hakan da kanta.

A hannuna ina sanye ne da wani dan awarwaro mai launin ja da kuma wata alama ta gargadin jan wutar lantarki. An makala masa wani dan mitsitsin batiri, wanda zai iya fitar da wutar lantarkin da za ta ja ni da zarar na taba wani wuri a jikinsa idan ina so wutar ta jani.

Wannan 'yar na'ura dai wadda sunanta Pavlok, wasu sun ce ta taimaka musu barin wasu dabi'u da suke son watsi da su, kamar gaigayar farce ko kwakwalar hanci ko cin wani abu.

Wanda ya kirkiro ta Maneesh Sethi ya ce tana iya raba mutum da dabi'ar da yake so ya bari cikin kwana biyar.

Saboda haka ina jarraba ta domin na daina amfani da wayata a lokacin dsa naje na kwanta, wanda daman masana sun ce amfani da wayar lokacin da za a kwanta yana damun barcin mutum kuma yakan iya haddasa masa matsalar rashin gani ta dan lokaci.

Wadanda suka kirkiro 'yar na'urar sun tsara ta ne ta yadda, idan mutum ya sa wutar lantarkin ta ja shi a lokacin da yake yin wannan dabi'ar da yake son bari - kamar ni a nan amfani da waya a gado - zai rika danganta halayyar da abu maras dadi, wanda hakan zai iya fitar masa da sha'awar yin halayyar, har ya kai ya rage yinta, wata rana ma a wayi gari ya daina gaba daya.

A karshe dai haka na daure na jajirce har nake sa na'urar ta ja ni a duk lokacin da na shiga dabi'ar tawa, kuma ya kasance jan da wutar take min yana da tsanani, ba zan iya jurewa ba.

To wannan yana nuna kenan wani dan karamin horo, misali na jan wutar lantarki ko wani hukuncin kamar cin tarar kudi hanyoyi ne na sauya halayyar mutum?

Lada ko Hukunci?

Wanne ne daga cikin biyun nan ya fi tasiri wajen raba mutum da wani hali da ba a so ko ba ya so ya yi?

Masu bincike sun yi kokarin gano yadda mutane suke daukar hukunci da kuma lada a gwaje-gwaje da suka yi da dama.

Misali an yi wani gwaji da aka wallafa sakamakonsa a mujallar kimiyyar kwakwalwa ta Cognition, inda mutane suke samun dan ladan kudi ko a ci tararsu dan kudin idan sun kasa wani aiki da ake jarraba su da shi.

Jan Kubanek na Jami'ar Stanford, wanda ya jagoranci binciken ya ce daga abin da suka gano; ''kwakwalwa tana bambanta lada da kuma asara a martaninta kan wani abu da ya faru da mutum.

Ya ce a kan asara ko cin tara, babu wani bambanci na sosai ko tarar kudin da aka yi wa mutum tana da yawa ko ba ta da yawa, a matsayin horo don ya bar wata dabi'a.

To amma kuma ba haka lamarin yake ba idan an zo maganar ladan da mutum zai samu idan ya yi abu.

Kubanek ya ce, idan ladan kudin da aka ba ka kadan ne idan ka guji yin wani abu, akwai yuwuwar za ka iya sake aikata abin a gaba.

Amma idan ladan kudin da aka ba ka yana da yawa za a ga ka guji sake aikata abin a gaba.

Shi kuwa rashi za ka ga duk yadda za ka rasa abu, da yawa ko kadan, hakan ka iya sa ka bar dabi'ar da kake yi da gudu.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Kila ma iya jarraba biyan abokan aurenmu 'yar tarar kudi don yaki da dabi'ar da ba ma so kuma ta zame mana jiki?

Bincike ya nuna cewa horo ko hukunci ma, a wani lokacin yana sa mutum ya sauya dabi'a. Misali wani gwaji da ka yi ya nuna ko da alamar ido aka yi a wani wuri da ba a son zubar da shara, ya isa ya hana mutane zubar da shara.

Saboda za su ga kamar ana ganinsu, kuma ba za su so a kama su a hukunta su ba.

A littafinsa mai suna God is Watching You, Dominic Johnson, ya ce, tsoron cewa akwai wani abu, Ubangiji ko wuta ko dai wani abu ya danganta da yadda mutum ya dauki Allah, yana sa hadin kan da ya fi wanda yadda hukumomin gwamnati suke a cikin al'umma.

Ya ce gwamnati da 'yan sanda suna da iko ne takaitacce, domin sanya idon da suke yi ba shi da yawa kuma hukuncinsu takaitacce ne.

Amma shi kuwa Ubangiji, yana sanya ido a ko'ina sannan hukuncinsa ba shi da iyaka. Kamar yadda mabiya addinai suka yi imani Ubangiji ya fi dan sanda karfi matuka gaya.

Akwai shedar da ke tabbatar da sakamakon wannan binciken, ciki har da wadda masanin halayyar dan'adam Azim Shariff ya gano cewa karancin aikata laifi a cikin al'umma yana da dangantaka da yadda suka yi imani da azabar wutar lahira.

Amma kuma wannan ya ta'allaka ne da yadda mutanen suka yi imani da aljanna in ji Johnson, amma dai abin shi ne mutane suna kokarin kaurace wa laifi ba lalle domin aljanna ba sai dai domin wuta.

Mu koma kan maganar awarwarona mai wutar lantarki, wanda na sa a hannuna, wanda yake da alama karara da ke gargadina cewa sai na sa wutar lantarki ta ja ni, idan na yi amfani da wayata lokacin da na kwanta barci.

Duk da cewa wannan alama ba ta kai ta hana ni wannan dabi'a ba gaba daya, amma dai ta kasance tana tuna min burin da na sa a gaba, na watsi da dabi'ar amfani da waya a gado. Kuma hakan ya taimaka min na rage yin amfani da wayar kullum dare.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Ba karamin aiki ba ne yaki da dabi'ar amfani da waya a gado

Abin da ya yi nasara wajen hana ni wannan dabi'a shi ne tarar kudi mai yawa, kamar yadda na gani a mako na gaba da na jarraba.

Mun yi yarjejeniya da mijina ne, a duk lokacin da na kwanta kuma nake amfani da wayar (shiga intanet), to zan biya shi tarar wasu kudade masu yawa, wadanda shi kuma zai kashe su a kan wasu abubuwa marassa muhimmanci, wato zai kashe kudin a banza.

Bayan dare daya kawai da na biya wannan tara, lalitata ta girgiza ta yadda ba zan sake marmarin amfani da wayar ba a gado.

Bayan kammala wannan gwaji, sai kuma na koma gidan-jiya na wannan dabi'a tawa ta amfani da wayar a lokacin barci, wanda hakan ke nufin sai na rinka biyan wannan tara ta kudi har abada - Wanda kuma hakan kila ba abu ne da zan iya jure wa ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. My attempt to stop my bad habits through electric shocks