Ka san hadari da kuma amfanin kayan jin dadin rayuwa?

kayan kwalan-da-makulashe Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Mutane ba su san illar da ke tattare da wasu abubuwan da suke jin dadinsu ba

Za ka ga kamar abu ne da ba zai iya yuwuwa ba ka fassara bayani a kan abin da ya shafi lafiya - amma wannan bayanin ko kididdigar mai sauki za ta iya taimaka maka a kan abubuwan da kake son yi a rayuwarka ta yau da kullum.

David Robson ya yi mana nazari.

A tsakanin giya ko wani abin sha da kuma tsawon rayuwa ko da da sau daya marubuci Kingsley Amis bai taba shakku ko tunanin wanda zai zaba ba a kan dayan. Kamar yadda aka taba ruwaito shi yana cewa; Ba dadin da za ka iya hakuri da shi don kawai ka samu karin shekara biyu ta rayuwarka a gidan kula da tsofaffi a garin Weston-Super-Mare da ke Ingila.

Ba lalle ba ne ka yarda; saboda matsalar ita ce kididdiga ko bayanan da aka bayar kusan ba a ba da su yadda ya kamata ba, ta yadda ba za mu iya fahimtar yadda ainahin abubuwan da muke yi a rayuwarmu ke illa ga lafiyarmu ba.

Misali: Ta yaya za ka iya kwatanta hadarin cin kayan kwalan-da-makulashe (burger) da zaman kallon talabijin?

Domin wayar wa da jama'a kai masanin kididdiga David Spiegelhalter a Jami'ar Cambridge ya saukaka alkaluman ta yadda za mu iya sanin ainahin irin yadda suke shafar tsawon rayuwarmu.

Ya nuna cewa kada mu sake mu dauka cewa akwai wata dabara ko al'ada da za ta iya yi mana maganin wata ta'ada: Misali, komai yawan 'ya'yan itacen da za mu sha ko mu ci ba zai hana mu mutuwa da wuri ba, idan muna da mummunar dabi'ar yawan shan taba ( ta akalla kara 20 a duk rana).

Amma dai akalla tana taimaka mana wajen fito da ainahin yadda abubuwan da muka zaba a rayuwarmu ta yau da kullum suke, ba tare da wani abu ya shige mana duhu ba.

Duk da irin fargabar da ke tattare da rayuwar wannan zamani na yau, idan ka kwatanta tsawon rayuwarka da ta kakanninka za ka ga yadda ka yi sa'a a ce ka zo wannan duniya a zamanin nan na karni na 21.

Daga Mujallar Likitanci ta Birtaniya

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Shan karan taba 20 a duk rana, na rage kusan shekara bakwai na rayuwarka
Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Shan kofi 2-3 na gahawa a kowace rana na kara tsawon rayuwarka da shekara daya
Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Kallon talabijin na tsawon sa'a biyu a duk rana na rage rayuwarka da shekara daya
Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Tafiyar minti 20 a duk rana na kara tsawon rayuwarka da shekara biyu
Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Shan kofin giya uku a duk rana na rage rayuwar namiji da wata hudu, mace kuwa da wata 16
Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Yawanci muna rayuwa da karin shekara 13 da rabi a kan kakanninmu da suka girma a 1910
Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Maza ba sa kai tsawon rayuwar mata da shekara hudu

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The real risks - and benefits - of everyday pleasures