Alawar Cakuleti da Kayan Lambu : Wanne ne ya fi illa ga muhalli?

Alawar kofi ko cakuleti Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cakuleti na yi wa hakori illa saboda zakinta

Idan ana maganar fitar da hayaki mai guba da ke gurbata muhalli da dumamar yanayi, abin mamaki za a iya ganin cewa wasu kayan kwalan-da-makulashen sun fi alheri a kan wasu da ake ganin sun fi sa lafiya.

Ga nazarin David Robson

Yayin da dan'adam ke ci gaba da fuskantar barazanar dumamar yanayi, muna kara gano irin yadda kusan dukkanin ayyukanmu ke yin tasiri ko illa ga muhalli. Abincin da muke ci kusan shi ne ma ya fi wannan illa.

Noma da ayyukan samar da kayayyakin amfaninmu na yau da kullum da muke yi a masana'antu da kuma safarar kayayyaki a motoci kusan dukkaninsu ana samun yinsu ne ta hanyar kona makamashin da ke fitar da hayaki mai guba da ke dumama yanayi.

Masana kimiyya suna auna tasirin wannan a matsayin alamar hayaki mai guba, wanda aka fi bayyana shi a matsayin yawan hayakin da ke fita idan za a samar

Bisa wannan abu ne da ba zai yuwu ba a iya yin dalar kayan abinci, wato daya kan daya, bisa irin illar da kowane kayan kwalan-da-makulashe da abinci ke yi a kan muhalli.

Nama da abubuwan da ake yi da nono ko madara suna kasan dalar, a matsayin wadanda suka fi illa, yayin da kayan marmari ('ya'yan itace) da kayan lambu, a matsayin wadanda ba su kai kowanne illa ga muhalli ba suke a sama.

Kayan da ake samarwa daga hatsi ko masara ko alkama da makamantansu, kamar burodi da taliya, da kuma alewa suna tsakiyar dalar.

Sai dai wannan tsarin ma'aunin ba ya la'akari da yawan makamashi ko karfin da jikinmu ke samu daga wadannan kayan abinci.

Kana bukatar cin ganyen salat mai matukar yawa kafin ka samu yawan sinadari ko makamashin (calory) da za ka samu misali idan kai mai cin nama ne misali kilishi.

Kamar yadda wani nazari ya gano idan har za a samar da yawan wannan ganyen salat da zai iya ba ka yawan wannan makamashi a jikinka daidai da na naman to sai an fitar da hayaki mai dumama yanayi linki uku a kan yawan da ake fitarwa idan naman za a samar.

Kayan lambun da aka sarrafa su kuwa misali wadanda aka sanya a gwangwani ko wasu abubuwan adanawa wadanda kamfanoni ke yi ko kuma wadanda ake kawo su daga wasu kasashe ko gonakin da ke nesa ka iya sa a samu hayakin da ya fi wannan yawa ma.

A wata kasida da aka wallafa a mujallar abubuwan da suka shafi lafiyar kayan abinci, Adam Drewnowski na Jami'ar Washington a Seattle tare da abokan aikinsa, sun yi kokarin nazari a kan wannan ta hanyar kiyasta yawan hayaki mai dumama yanayin da ke fita idan za a samar da yawan kwayar makamashi 100 (calory) wanda abinci ke ba wa jiki, a kayan abinci daban-daban.

Idan aka biyo ta wannan hanya da wadannan masana suka tsara domin tantance yawan hayakin mai dumama yanayin da kowane irin kayan abinci ke dalilin samarwa, sai waccan dalar ta muka fara yi, ta juye na sama su dawo kasa. Wato wadanda a da ake ganin sun fi illa ga muhalli, ta wannan kiyasin su ne ba sa illar sosai.

To yanzu kenan za a ga cewa kek ko alawar cakuleti kafin a samar da su sai an fitar da hayaki mai sa dumamar yanayi da ya kai kashi goma na illar da kayan lambu da aka sarrafa ko aka sanya a gwangwani (na kamfanoni) ke yi ga muhalli ta yawan hayaki mai gurbata yanayi. A kan samar da nama ana fitar da hayakin da ya kai rabin wanda ake fitarwa a wurin samar da kwai.

To amma fa wannan ba yana nufin wata dama ce gareka ka ci gaba da shan alewar cakuletinka ba da sauran kayan zaki, domin akwai tarin shedu da ke nuna shan sukari ko kayan zaki da yawa kan kai mutum ga kamuwa da cutuka iri daban-daban, da suka hada da cutar sukari da ta zuciya.

Kuma har yanzu kayan lambun da aka debo daga gona ba a sarrafa su ko zuba musu wani sinadari don kada su lalace ko a samu damar safararsu zuwa wani wuri ba, sun fi zama alheri ga muhalli da kuma lafiyarka.

Bayanan wadannan hotunan da suke kasa za su iya taimaka maka wurin zaben kayan abincin da za su fi maka amfani a jiki.

Burodi

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Burodin da zai ba ka (awon) makamashi 100 a jikinka na samar da gram 50 na hayaki mai dumama yanayi

Kek

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Kek din da zai ba ka (awon) makamashi 100 a jikinka na samar da gram 81 na hayaki mai dumama yanayi

AlawarChakuleti

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Chakulet din da za ta ba ka (awon) makamashi 100 a jikinka na samar da gram 59 na hayaki mai dumama yanayi

Kwai

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Kwan da zai ba ka (awon) makamashi 100 a jikinka na samar da gram 440 na hayaki mai dumama yanayi

Madara

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Madarar da za ta ba ka (awon) makamashi 100 a jikinka na samar da gram 351 na hayaki mai dumama yanayi

Nama

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Naman da zai ba ka (awon) makamashi 100 a jikinka na samar da gram 248 na hayaki mai dumama yanayi

Kayan lambu na gwangwani

Hakkin mallakar hoto OLivia Howitt
Image caption Kayan lambu na gwangwani da za su ba ka (awon) makamashi 100 a jikinka na samar da gram 787 na hayaki mai dumama yanayi

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Chocolate vs vegetables: The true environmental costs