Ka san yadda za ka kauce wa karerayi da labaran karya?

Jaridu da mujallu Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption A wannan zamani na intanet labarai na karya kullum karuwa suke yi

A wannan zamani da karerayi da labaran karya suka cika shafukan sada zumunta da muhawara na intanet BBC ta duba hanyoyin da ya kamata mutum ya rika bi domin tantance labari.

Ga nazarin David Robson:

Kama daga ikirarin cewa Simpsons ya yi hasashen nasarar Trump a shekara ta 2000 zuwa labarin kanzon-kuregen nan da aka ce Sarauniyar Ingila ta yi barkwanci kan kisan Trump, shafukan sada zumunta da muhawara da kafafen watsa labarai na intanet na cike da karerayi da labaran karya.

Ka duba labarin harin da aka a masallacin Quebec ranar 29 ga watan Janairu, na Alexandre Bissonnette. A cikin 'yan sa'o'i kadan kawai sai ga labarai na karya sun fara bazuwa wadanda ke cewa 'yan sanda na kokarin boye wani Musulmi da ke da hannu a harin.

Kamar yadda David Mikkelson, wanda suka kirkiro shafin nan na Snopes, wanda ke warwarewa da gano labarai masu sarkakiya da karya, ya ce:

'' Abin sai tashin gwauron zabo yake, (yana bazuwa kamar wutar daji).'' To hatta shi kansa shafin na Snopes ya samu karin masu ziyartarsa a wata suka linka zuwa kusan miliyan 13.6 a watan Oktoba na shekarar da ta wuce, a lokacin da masu karanta labaran shafin ke kokarin sanin abubuwan da ke wakana kafin zaben Amurka.

Yanzu dai an dace masana tunanin dan adam sun fara fahimtar abin da ya sa muke yarda da labaran karya da suka dace da ra'ayinmu, kuma muke kin yarda da maganganu na gaskiya da suka saba da fahimtarmu.

To a nan mun duba hanyoyi shida da za ka iya bi domin ganin ba a yaudare ka ba da labaran karya.

1, Kada ka bari a yaudare ka ta hanyar sanayya ko saukin labari:

Bincike da nazari da dama da aka yi sun nuna cewa abu ne mai matukar sauki a boye karya idan aka raba ta da wani mutum ko kafa mai gaskiya, saboda za a ce tun da aka bayyana labarin karara haka da wani dungu, to ai kawai gaskiya ne.

Idan ka wallafa labari karara ta yadda kusan kowa zai iya karanta rubutun, wannan ma zai iya sa ka yaudari mutane da labarin karya, domin da sun gani za su yarda, saboda ba ka yi wani boye-boye ko dabaru ba.

Kusan haka lamarin yake, ta yadda za ka ga kusan za mu fi saurin yadda da mutum idan mun san shi ko sananne ne (misali idan ana ganinsa a talabijin sosai), ko da kuwa mutumin ba shi da kwarewa sosai a kan abin da yake magana a kai.

Ka yi kokarin matsa wanda ya ba ka labarin da tambayoyi, kuma kada ka tsaya ga bayani ko maganar da ya yi kawai.

2, Kada ka bari a yaudare ka da hotunan bogi:

An ce ''gani ya kori ji''. Hotuna na kara wa labari armashi da tabbatar da gaskiyarsa, to amma a wannan zamani na kwamfuta za a iya sarrafa hoto a jirkita shi kuma ba lalle ka gane yadda hakan zai yaudare ka ba, ka yarda da labari.

Masu shafin intanet na Slate sun taba yin wani gwaji, inda suka sanya hotunan wasu abubuwa da suka faru na siyasa, wasu hotunan na gaskiya ne wasu kuma ba na gaskiya ba ne.

Da suka tambayi masu ziyarar shafin bayan sun sanya hotunan, kusan rabin masu karanta labaransu, sun yi ikirarin cewa lalle sun tuna lokacin da abubuwan da aka yi hotunan nasu na karya, suka faru (ba su san cewa hotunan karya ba ne).

Saboda haka wannan hanya ta amfani da hoto, daya ce daga cikin hanyoyin da ake saurin yaudarar mutane da labaran karya.

A don haka ka rika kokarin tabbatar da labari daga kafofi daban-daban, kuma kada ka dogara ga sheda ko abin da ke gabanka kawai.

3, Ka yarda da jahilci ko rashin saninka (kada ka dauka ka san komai):

Mutane da dama suna yaudarar kansu da cewa suna da sani, suna ci-da-zuci, suna ganin cewa sun fi yawancin mutane ilimi ko sani.

Kuma manyan wayoyin da muke da su masu intanet wadanda kusan duk ilimin da muke neman sani, a yau da mun bude za mu gani cikin sauki, suna kara mana wannan ji da kai.

Saboda haka ba za mu kalubalanci duk wani labari da ya zo daidai da ra'ayinmu ba, yayin da muke kin yarda da wanda ya saba da ra'ayinmu.

4, Kada ka tsaya iya kafar da ka sani ko wadda ke kusa da kai (ka fadada bincikenka):

Kamar yadda Zaria Gorvett (mai yi wa BBC nazari) ta bayyana a wani labarinta kan yadda mutane ke rarrabuwa, bisa al'ada mutane na yarda da ra'ayin wadanda suke kusa da su walau ta makwabtaka ko kuma ta 'yan uwantaka.

Saboda haka ka rika kokarin magana da mutane daban-daban masu ra'ayin da ya saba da naka, kuma ka nemi labari ta kafofi da yawa wadanda ba ka damu ka duba ba.

Idan ka yi haka za ka iya mamaki ka ga bayanan da ke tuhuma ko shakkun abin da kai ka raina a wannan labari. Ma'ana wata kafar labaran za ta dago ko taso da wasu abubuwan da za su nuna maka shakkun gaskiyar wannan labari ko ma karyar da ke cikinsa.

5, Ka zama mai kwakwar bincike:

Masanin tunanin dan adam Tom Stafford ya shawarce mu da mu kasance masu kwakwar neman sani domin za mu iya amfana da hakan.

Ilimi kadai ba kasafai zai kare mu daga karkata ga wata fahimta ko ra'ayi na bangare daya ba, amma mutanen da suka kasance masu kwakwa da tambaya sukan binciki hatta sheda ta kimiyya ba tare da nuna son kai ko karkata ga wani bangare ba. Wato dai ra'ayinsu ba zai hana su yarda tare da bin gaskiya ba idan sun ji ko sun gan ta.

6, Ka saurari ra'ayin da ya saba ko kishiya:

Har kullum ka yi nazari tare da sauraro ko duba ra'ayin da yake sabanin fahimtarka. Ka sa kanka a matsayin masu wancan daya ra'ayin.

Misali idan aka gabatar da bayanan da ke nuna cewa hukuncin kisa ya rage yawan kashe mutane, sannan aka bukace ku da ku duba tsarin da aka bi wajen wannan nazarin sanna ku dauka cewa akasin wancan sakamakon aka samu, wato hukuncin kisa ya sa an samu karuwar kashe mutane.

To wannan tsarin zai sa mutum ya rage son rai, wato zai rage kin yarda da shedar da ta saba wa ra'ayinsa, sannan kuma ya zama mai shakku ko bincikar shedar da a da ya dogara da ita, ta sa yake da ra'ayin da ya kafe a kai.

Ta dalilin wannan mutum zai kasance mai adalci, wato za ka ga bai karkata wajen wani ra'ayi na son kai ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How to avoid falling for lies and fake news