Me zai faru idan aka daina cin nama a duniya?

Tarin gurji Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Idan aka daina cin nama aka koma cin kayan lambu da 'ya'yan itace kawai, yawan mutanen da ke mutuwa duk shekara a duniya zai ragu da miliyan 8

Shin me zai faru idan aka wayi gari rana daya aka daina cin nama a duniya har abada? Ba shakka akwai alfanu da illolin da ake gani za su iya biyo bayan hakan, a kan yanayi da muhalli da lafiyarmu da tattalin arziki da sauransu.

Sophia Smith Galer ta yi mana nazari:

Idan kowa ya dauki tsarin cin kayan itace kawai a madadin nama daga nan zuwa shekara ta 2050, yawan mutanen da suke mutuwa a duniya zai ragu zuwa miliyan bakwai kawai a duk shekara - idan kuma tsarin daina cin duk wani abu na dabba ne ba nama kadai ba to hakan zai rage masu mutuwar a duniya zuwa miliyan takwas.

Hayakin da ake fitarwa a sanadiyyar samar da abinci zai ragu da kusan kashi 60 cikin dari kamar yadda Marco Springmann mai bincike a Jami'ar Oxford ya bayyana. Wannan kuwa zai kasance ne idan mutane suka yi watsi da amfani da jan nama.

Sai dai kuma manoma a kasashe masu tasowa ka iya shiga mawuyacin hali. Wasu wuraren a wasu sassan na duniya kamar yankin Sahel na Afirka da kuma Sahara ana iya kiwon dabbobi ne kawai.

Saboda haka idan aka yi watsi da nama, hakan zai tilasta wa jama'ar wadannan wurare zama wuri daya su daina yawan kiwo, kuma za su rasa al'adarsu wanda hakan zai kai ga a manta da su gaba daya.

Haka kuma a sanadiyyar hakan, dazukan da wadanna mutane suke kiwo suna cinyewa, za su dawo, a samu raguwar matsalar sauyin yanayi ta rashin bishiyoyi da sauran tsirrai, daji zai bunkasa manyan namun daji irin su bauna da kura su dawo bayan da a da aka kore su ko aka kashe su domin a kiwata shanu da sauran kananan dabobin gida na nama.

Harwayau idan aka daina cin nama, dukkanin mutanen da suke kiwo ko wata harka da ta shafi kiwon da sana'ar nama za su rasa aikin yi, sai an horar da su a wata hanyar da samun abin tafiyar da rayuwarsu - sabuwar sana'ar za ta iya kasancewa a fannin gona ko samar da daji ko samar da mai na makamashi daga tsirrai (bioenergy).

Idan kuwa ba a sama musu da wasu sana'o'in ba to hakan zai haifar da dimbin rashin aikin yi da rashin kwanciyar hankali tsakanin jama'a, musamman a yankuna na karkara.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Idan mutane suka koma cin 'ya'yan itace kawai fa, me zai faru?

Kawar da dabbobi irin su tumakai zai iya yin illa ga rayuwar sauran dabbobi da tsirrai a doron kasa, domin kiwon da suke yi ya taimaka wajen kasancewar yadda filayenmu suke tsawon karni da dama. Saboda haka za a biyan wasu manoman su bar dabbobinsu saboda amfanin muhalli.

Babu sauran kajin salla - rasa nama na nufin cewa za mu kai ga rasa wasu al'adunmu:

Al'ummomi da dama a fadin duniya suna bayar da kyautar dabbobi a lokacin bikin aure da sauran taruka. A fahimtar Ben Phalan na Jami'ar Cambridge, wannan ne dalilin da ya sa kokarin rage cin nama ya samu matsala.

Daina cin nama zai rage hadarin kamuwa da cutukan zuciya da cutar sukari da ta shanyewar jiki da kuma wasu nau'ukan cutar daji, wanda hakan zai taimaka a rage asarar kashi biyu zuwa uku cikin dari na kudin da ake kashewa a duniya wurin neman lafiya.

To amma kuma fa muna bukatar maye gurbin nama da wasu kayan abincin musamman ma ga mutane sama da biliyan biyu da ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki.

Nama da sauran abubuwan da ake ci wadanda ake samu daga jikin dabbobi sun fi yawan abubuwa masu gina jiki a kan sauran kayan abinci da muka saba ci, kamar shinkafa da dangin hatsi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The consequences if the world decided to go meat-free