Ka san yadda abokanka suke ɗaukarka kuwa?

Kawaye Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba za ka taba sanin fassarar da abokananka suke yi maka ba

A kullum muna ɗaukar cewa mun san yadda abokai da dangi da sauran jama'a suke ɗaukarmu, to amma muna yaudarar kanmu ne da hakan, domin ilimin sanin tunanin ɗan adam ya ƙaryata mu da cewa ba za mu iya sani ba.

Christian Jarrett ta yi mana nazari

Idan kai ma kamar sauran mutane kake, kila zai iya kasancewa ka san yadda yanayinka yake- walau kai me kunyar magana ne ko me yawan magana ne ko faran-faran da jama'a da sauransu.

To amma kana ganin fassarar da mutane suke yi maka ta yi daidai ko kusa da yadda kake daukar kanka?

Masana tunanin dan adam da suke nazari a kan wannan tambaya sun gano cewa yawancinmu muna da wani dan sani na abin da suke kira ilimin sanin yadda mutane suke daukarmu.

Amma kuma duk da haka akwai abubuwan da mutane da yawa suka sani a kanmu ko suke tunani a kanmu sosai kuma mu ba mu da masaniya a kan abubuwan.

A zahirin gaskiya idan rayuwarka tana tafiya yadda ya kamata; kana cikin kwanciyar hankail da farin-ciki, to zai kasance ba ka da masaniya sosai a kan yadda mutane suke kallonka.

Daya daga cikin cikakkun bincike-binciken da aka yi a kan ko mutane sun san yadda sauran jama'a suke kallonsu, an wallafa shi ne a 2011 wanda masu bincike a jami'ar Washington a St. Louis da jami'ar Forest suka yi.

A nazarce-nazarce da dama da aka yi, Erika Carlson da abokan aikinta sun nemi daruruwan dalibai da su ayyana yadda suke ganin kansu, misali a kan yawan magana ko zurfin ciki wato rashin magana sosai da sauran dabi'u kamar gaskiya da barkwanci da kyau, sannan kuma su daliban su kawo abokai da danginsu, wadanda su ma za su fadi yadda suke kallonsu.

A karshe daliban suka fadi matsayin da suke ganin wadannan abokai da dangin nasu za su bayyana a kansu.

Hanya daya da za ka auna yadda sauran mutane suke kallonka, ita ce ka duba kai yadda kake kallon kanka, kuma ka yi amfani da hakan a matsayin ma'aunin yadda sauran mutane suke kallonka.

Idan kai mutum ne wanda ba shi da zurfin ciki, wato mai yawan magana da sauransu, haka su ma sauran jama'a suke daukarka.

Carlson da abokan nazarinta sun duba wannan, inda suka gano cewa hatta bayan gano yadda daliban suke daukar kansu, akwai alaka tsakanin yadda daliban suke ganin sauran mutane ke fassara su da kuma yadda ainahin su wadannan mutanen suke fassara sun a zahiri wato kimarsu.

A gaskiya ma yadda su daliban suke daukar yadda sauran mutane suke kallonsu ya ma fi nuna ainahin matsayi ko kimarsu, fiye da matsayin da su daliban ke ba wa kansu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutanen da ke tare da kai za su iya fassara ka yadda kai ba ka taɓa ɗaukar kanka ba

Masu binciken sun ce sakamakon ya bayar da shedar da suke ganin ta nuna cewa mun iya lura fiye da yadda muke daukar kanmu har mu gano yadda wasu ke kallonmu.

Kuma wannan sakamako haka yake kasancewa ko da kuwa an sake yin wannan gwaji ne da bakin da su wadannan dalibai ba su taba mu'amulla ko tattaunawa da su ba tsawon abin da ya wuce minti biyar ba.

Wannan ya nuna kamar kana da 'yar masaniya a kan yadda mutane suke daukarka, amma kuma wani bincike da ka yi bayan wannan na farko ya nuna fahimtar taka ba haka take ba, kamar yadda wasu masana ilimin tunanin dan adam 'yan Jamus suka nuna a wani bincike da suka yi daga shekarar 2013.

Dalibai 65 sun ayyana yadda suke ganin haka yanayinsu yake ta hanyar kalamai guda 37 na ''e'' ko '' a'a'', (kamar ''ba na nuna bambanci ga kowa'' da ''ni malalaci ne''), bayan sun rubuta irin wadannan kalamai a takarda, sai suka mika takardun ga abokai da 'yan uwa da yawa domin su bayar da amsar tambayoyin. A karshe kuma sai daliban suka bayyana yadda suke ganin wadannan abokai da 'yan uwa za su bayar da amsar halayen nasu.

Masu binciken sun gano cewa akwai kusan daidato a kan yadda abokai da dangin suka bayyana halayyar daliban, (kamar a ce kusan duk kowa ya yarda wannan mutumin malalaci ne)wanda ya bambanta da yadda su daliban suka dauki kansu, kuma wannan ba ya cikin tsarin yadda daliban suke dauka sauran mutane na daukarsu.

Masu binciken sun ce nazarin nasu ya nuna yawanci mutum ba shi da masaniyar wasu daga cikin hanyoyi na musamman da wasu mutane ke fassara shi.

Nazarin kanka da kanka

A wani nazari da aka wallafa a shekaran nan, wasu masana ilimin tunanin dan adam su biyu a jami'ar Martin-Luther a Jamus, sun nemi dalibai su harhadu mutum hudu-hudu, su yi wa kansu fassarar yadda suke daukar kansu, su bayyana yadda suke daukar 'yan cikinsu, a karshe kuma su yi kiyasin yadda 'yan cikin nasu za su fassara su.

Haka kuma daliban sun cike wani ma'auni na yanayin tunaninsu, abin da ya hada da yadda suke daukar mutuncinsu da kuma abubuwan da suke nuna alamun rashin natsuwar mutum.

Nazarin ya nuna daliban da suke cikin farin ciki fiye da saura sun nuna alamun rashin sani na yadda wasu ke daukarsu, sun fi dogaro a kan yadda suke daukar kansu, kuma daliban sun fi yin haka da wadanda suka fi sabawa da su.

A takaice abin da binciken ke nunawa shi ne, idan kana cikin yanayi na kwanciyar hankali, za ka fi daukar cewa abokanka suna kallonka kamar yadda kake kallon kanka (wanda idan kamar yawancin mutane kake, kallon mutumin kirki za ka yi wa kanka).

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Za ka ɗauka kafi kyau a hoton da ka ɗauki kanka da kanka, amma wani bincike ya ce ba haka abin yake ba

Za a fi ganin muhimmancin wannan bambanci sosai a shafukan sada zumunta da muhawara na intanet. A zamanin yau mun fi gabatar da kanmu ga duniya ta hanyar intanet, maimakon a zahiri, kuma masana tunanin dan adam sun fara gudanar mana da bincike a kan wadannan sabbin hanyoyi domin mu san yadda sauran jama'a ke kallonmu.

Wani bincike da aka wallafa a shekaran nan ya yi nazarin lamarin musamman ta fannin hoton da mutum yake daukar kansa da kansa da wayar salula, wanda muke sanyawa aintanet.

Kusan daliban jami'a 200 ne suka shiga wani dakin bincike na kimiyyar tunanin dan adam, inda suka dauki hotunan kansu, sannan kuma mai bincike ya dauki hotonsu da wayar da suka dauki hoton kan nasu.

Daga nan kuma sai daliban suka bayyana kyawun hotunan da yadda za a kaunaci hoton idan an gani. Masu binciken daga jami'ar Toronto, sun gano cewa daliban da suka saba daukar kansu hoto da kansu (selfie) suna ganin sun fi kyau da jan hankali a hoton da suka dauki kansu da kansu maimakon hoton da mai binciken ya dauke su.

Amma kuma da aka nemi wasu mutanen ta intanet wadanda za su fayyace hoton da ya fi kyau da daukar hankali sai suka zabi hpotunan da masu binciken suka dauki daliban maimakon wadanda daliban suka dauki kansu da kansu.

Kila wannan wani abu ne da ya kamat ka yi la'akari da shi nan gaba idan za ka sanya hoton da ka dauki kanka da kanka a intanet.

Wannan bincike ya nuna cewa, idan har kana son sanin ainahin yadda mutane suke daukarka, zai fi kyau ka tambaye su. In dai har abokanka da danginka za su gaya maka gaskiya, za ka ga cewa ko alama yadda kake daukar kanka ba haka kake ba.

To amma fa a daya bangaren in dai har kai kana jin dadin yadda kake, da kuma yadda kake ganin sauran jama'a ke kallonka, zai fi dacewa gareka, ka guji yawan tambayoyi. Wannan jahilci zai iya kasancewa alheri a wurinka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why you can never tell what your friends really think of you