Me ya sa mata suke yi wa al'aurarsu kwaskwarima?

Likita
Image caption 'Yan mata sun ce sun tsani farjin su'

Mata masu karancin shekaru, kamar shekara tara, suna neman a yi musu tiyata a farji saboda ba sa jin dadin ganin siffar al'aurar tasu.

Wata fitacciyar likitar mata, Dr Naomi Crouch, ce ta shaida wa BBC wannan labari.

A tiyatar da ake kira Labiaplasty ana rage bakin kofar farjin ne ko kuma a sauya siffarsa.

Hukumar kula da lafiya ta Birtaniya (NHS) ta hana yi wa macen da ba ta kai shekara 18 tiyatar ba.

A shekarun 2015 zuwa 2016, fiye 'yan mata 200 da ke kasa da shekara 18 aka yi wa tiyatar labiaplasty kan tsarin ba da kulawa kyauta na NHS.

Wasu masana suna tsoron cewar kallon hotunan batsa ta a shafukan sada zumunta na sa 'yan mata na neman siffar farjinsu ya fi yadda ya kamata.

Baya ga Birtaniya ko a kasashe irin Najeriya ma a kan samu matan da suke kai kansu a yi musu irin wannan tiyata, musamman matan da suka manyanta saboda yawan haihuwa.

'Abin takaici'

Dr Crouch, wadda ke jagorantar kungiyar likitocin yara da 'yan mata a Birtaniya, ta ce a dukkan aikin ta ga hukumar NHS har yanzu ba ta ga yarinyar da take bukatar tiyatar da gaske ba.

Ta ce: "A wasu lokutan 'yan mata za su zo da kalamai kamar: 'Na tsane shi ne kawai, ina son a cire shi,' kuma a ce yarinya tana jin haka kan wani sashin jikinta, musamman bangaren da ya fi kusa, abin takaici ne."


'Labarin Anna'

Anna' ta bayyana dalilin da ya sa ta so ta yi tiyatar farji a lokacin tana yarinya.

Anna - wannan ba asalin sunanta ba ne - ta yi tunanin yin tiyatar labiaplasty a lokacin da take 'yar shekara 14.

"Kawai na kama daga wani wuri da nake ganin tsaftarsa bai cika ba, kuma na ji ina son a rage shi.

"Mutanen da ke kusa da ni na kallon hotunan batsa kuma na ji ya kamata wurin ya yi daidai, ba wai ya yi ta fitowa ba ne.

"Na yi tunanin haka na kowa yake, saboda ban taba ganin yadda na kowa yake ba

"Na tuna a lokacin ina tunanin cewar: 'In ana masa tiyata, ba ni kadai ne nake son ayi mini ba. Ta yiwu ba wani abun a zo a gani ba ne'."

Daga baya sai ta yanke shawarar cewar ba za ta yi tiyatar ba.

"Na yi matukar murnar cewar ban yi tiyatar ba. Bana bukatarta.Ina ganin sifar jiki na yadda ya kamata.."


Paquita de Zulueta, wata likiltar komai da ruwanka wadda ta shafe shekara 30 tana aiki, ta ce a 'yan shekarunnan ne 'yan mata suka fara zuwa mata da damuwa game da siffar bakin farjinsu.

"Ina ganin 'yan mata 'yan shekara 11 zuwa 12 zuwa 13 suna tunanin wajen farjinsu na da matsala - cewar siffar wajen farjinsu ba ta da kyau, kuma girman wajen farjin ba ya yadda ya kamata, kuma sun nuna kusan nuna kyama .

"A tunaninsu bai kamata a iya ganin bakin farjinsu ba, kamar na 'yar tsanar Barbie, amma a zahiri, akwai bambance-bambance da yawa. Babu matsala idan bakin al'aurar ya fito."

Image caption Paquita de Zulueta ta ce wasu 'yan matan sukan zuzuta yadda sifarsu ta ke domin su samu damar yin tiyata

Ta ce hotunan batsar da yara suke kallo ne silar matsalar.

"Babu isasshen wayar da kai, kuma ya kamata wayar da kan ya fara a lokacin da yara suke kanana. Wayar da kan zai bayyana cewar akwai kamar yadda mutene suka sha bamban a ta fuska, haka muke da bambanci a can kasa, kuma babu matsala kan hakan.

Hukumar NHS ta Ingila ta ce ba ta gudanar da tiyatar domin kwaskwarima ba, tana mai cewa ta yi ta ne domin dalilai na lafiya.

A shekarun baya-bayan nan kungiyoyin da ke kula da lafiya a anguwanni sun tura mara lafiya da ke jin radadi ne da kuma damuwa zuwa asibitin tiyata.

Amman Dr De Zulueta ta ce wasu 'yan matan sun san sai sun zuzuta matsalarsu kafin su samu a yi musu tiyata.

"Suna sane da cewar idan suka ce farjin na cikas ga jima'i ko kuma wasannin motsa jiki, za su fi samun damar tiyata."

'Ta sha bamban da kaciya'

Dr Crouch ta yi imanin cewar 'yan matan da ke da tawaya ne kawai ya kamata a yi wa tiyatar labiaplasty .

Ta ce: "Ina matukar mamakin cewar akwai 'yan mata 150 da ke da tawaya wadda ke nufin suna bukatar tiyata kan bakin farjinsu."

Ta kara da cewar akwai kamanni masu ta da hankali tsakanin wannan tiyatar da kuma kaciyar mata, wadda aka hana a Birtaniya.


Neman shawara

Dr Gail Busby, wata babbar likitar 'yan mata a asibitin St Mary, ta ce yana da muhimmanci 'yan mata da iyayensu su tuna cewar:

  • A lokacin balaga, lebban al'aura suna kan girma - ina lebban na ciki ke fara girma -saboda haka ba abun damuwa ba ne su fito sosai. Kada 'yan mata su gwada kansu da manyan mata
  • A lokacin da mace ta kai shekara 18, wajen bakin farjin zai rigaya ya girma. Idan 'yan mata za su iya kamewa daga neman tiyata har zuwa lokacin da suka gama balaga, a wannan lokacin farjinsu zai riga ya sauya- lamarin da zai cire dalilin neman yin tiyata tun daga farko
  • Tiyata ka iya janyo tabo. Tun da leben farjin na kan girma ne, tiyatar na iya sa kai bakin farjin ya yi daidai bayan mace ta gama balaga
  • Kar ki ji ke kadai ce. Rabin 'yan mata a ajinku za su kasance cikin irin wannan matsayin, wani banagre ne na girma da kowa ke bi. Kawai ba a magana a kansa a bayyane ne.
  • Idan iyaye na son su kawar da tsoro, ku kai 'yar ku ga likitan komai da ruwanka
  • A wasu lokutan, idan akwai damuwa da yawa kan sifar jiki, zai iya taimaka wajen ba da karin dabarun jurewa

Likitocin kwaskwarima masu zama da kansu ne suke yin yawancin tiyatar labiaplasties kan mata masu sama da shekara 18.

An soki ma'aikata a fannin tiyata da mayar da tiyatar farjin wani abun yau da kullum.

Image caption Likitan tiyata na kwaskwarima, Miles Berry, ya ce tiyatar labiaplasty za ta iya kara wa mata kiman da suke ganin kansu da shi

Likitan tiyatar kwakwarima, Miles Berry, ya kare tiyatar, yana mai cewar za ta iya inganta rayuwar mata.

"Za ta iya sauya mutane matuka, irin yadda suke ji game da kansu, karfin gwiwarsu da kuma yadda suke ji da kansu.

"Na ga marasa lafiya masu shekaru tsakanin 16 da 21 wadanda ba su taba yin saurayi ba saboda sun damu da wannan lamarin."

Kungiyar likitocin ciki da haihuwa da kuma mata ta ce kar a yi tiyatar har sai yarinya ta gama girma, bayan ta kai shekara 18 da haihuwa.

Kalli shirin Victoria Derbyshire programme a ranakun mako tsakanin karfe 09:00 zuwa 11:00 kan BBC Two da kuma BBC News Channel.